THE ENCHANTED KINGDOM

CHAPTER 23

by @queenmahirah14

THE ENCHANTED KINGDOM🧚
Story and writing by Queen Mahirah
Marubuciyar...
THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA)
KITABUL HUB
LABARIN DR NEELAH
LABARIN BINT ABDULAZIZ
PAID BOOK
FREE CHAPTER
Karku manta wannan littafi na kuɗi ne...
Sai de akwai bononza ga wanda yayi FOLLOWING CHANNEL da GROUP...
Kana da damar samun complete kafin watan June ya kare...
Amma in baka shiga ba har ya kare to be honest asusun ka zai kara..ƙiriiiin!!😁
Cos zaka biya 500 Naira kafin ka mallaki complete inshallah 🥰
contact:*** for more information 



THE ENCHANTED KINGDOM

CHAPTER 23
'' Hawayen Mace Da Ta Rasa Amanar Da Aka Ba Ta''

''Makomar Sayyadah Ruqayya Da Sirrin Mahaifiyar Maryam Zahrah''

A can nesa da hasken Masarautar Nurayn, wato kauyen ZAN -ZABIR dake iyakan MADINATUL ALAM. Akwai wani tsohon gida da ya daɗe yana ɗauke da ƙamshin kaɗaici.

Ba kamar da ba.

Ba a jin muryar Maryam tana aiki daga safe har dare.

Ba a jin umarnin da aka saba bayar ya cika gidan.

Ba a jin kukanta da take ɓoyewa a bayan bangon ɗakinta...

Domin yanzu...

Gidan ya yi shiru.

Shiru mai ɗauke da nadama.


---

Sayyadah Ruqayya tana zaune a kusurwar ɗaki, jikinta ya rame, fuskarta ta sauya.

Matar da ta taɓa zama mai ƙarfi, mai tsananin magana, yanzu ta zama kamar wadda rayuwa ta karya.

A gabanta akwai tsohon kyalle da Maryam ta saba ɗaurawa kanta lokacin tana ƙaramar yarinya.

Ta riƙe shi da hannuwa masu rawa.

"Maryam..."

Furta sunan ta kawai ya isa ya sa hawayen ta ba ƙakkautawa..

A baya, idan ta kira wannan sunan, tana kira ne da fushi.

Amma yau...

Tana kiransa da ciwo.


---

Ta tuna ranar data hadu da Mahaifiyar Maryam.

Ranar da wata mace mai daraja ta tsaya a gabanta tana kuka.

Matar ba kowa ba ce face...

Sultana Amina Rahma..

Mahaifiyar Maryam.

Mace mai taushin zuciya wadda ta san cewa rayuwar 'yarta tana cikin haɗari.

---

A wannan lokacin, Ruqayya ta yi alkawari.

"Na rantse zan kare ta kamar tawa."

Amma rayuwa...

Da jarabawa...

Sun canza komai.

---

Bayan wasu shekaru, lokacin da Maryam ta girma...

Zafin rayuwa ya mamaye zuciyar Ruqayya.

Ta manta cewa yarinyar amana ne a gareta..

Ta manta cewa nauyi ne a wuyan ta.

Ta fara kallon Maryam a matsayin damuwa.

Ba a matsayin rayuwa sandar kiwon da Allah ya ba ta ba.

Ta yi mata tsauri.

Ta yi mata kalamai masu ciwo.

Ta manta da hawayen mahaifiyarta.


---

Amma yanzu...

Komai ya dawo.

Maryam ba yar talakawa ba ce.

Ita ce wadda aka haifa domin gadon Nurayn.

Kuma Ruqayya ta fara ganin abin da ta rasa.

Ba zinariya ba.

Ba daraja ba.

Sai albarkar da Allah ya ba ta ta kula da wata zuciya mai tsarki.


---

Wata rana, wani dattijo daga Nurayn ya kawo mata wani saƙo, ace warsa lokaci yayi da Magajiya zata koma gida.
Bayan dogon neman da yayi ne na tsawon shekara 2 a karshe ya samu SAYYADAH RUQAYYA.

A cikin saƙon akwai kalmomin Sultana Amina Rahma

"Ruqayya, idan Maryam ta taɓa jin zafi a hannunki, kada ki manta cewa na ba ki ita ne saboda na yarda da zuciyarki."

"Kada ki bari duniya ta sa ki manta da amanar Allah."

'' kamar yadda na faɗa miki cewar lokaci zai zo da sanadin yarinyar zaki samu girma da dauƙaka''

''Alhamdulillah, a yau zaki zama cikakkiyar uwa kuma mata ga Malik Azeem, badan komai ba sai dan Alƙawarin da kika riƙe na kula da Maryam Zahrah''

''hakan zai samu ne in har kin rike amana, kin mata tarbiyya, ba ha'inci.''
---

Ruqayya ta kasa riƙe kanta.

Ta faɗi ƙasa tana kuka.

"Na yi kuskure..."

"Na yi wasa da abin da aka ba ni amana."

Ta kalli sama.

"Ya Allah, idan akwai hanyar da zan gyara..."


---

Amma kafin ta samu damar neman gafara...

Wata gaskiya ta sake bayyana.

Sultana Amina Rahma ba ta mutu saboda cuta ba.

An kashe ta.

A daren da ta bar Maryam a hannun Ruqayya...

Ta yi ƙoƙarin gudu daga waɗanda suke farautar 'yar tata.

Amma an same ta.

An kashe ta ne domin ta ƙi bayyana inda Maryam take.

Kuma kalmar ƙarshe da ta furta ita ce:

"Ku iya ɗaukar komai daga gare ni... amma ba za ku taɓa kashe hasken ɗiyata ba."

---

Shekaru da yawa, Ruqayya tana ɗauke da wani ɓangare na wannan sirri ba tare da sani ba.

Domin a ranar da Amina Rahma ta zo ta ba ta Maryam...

Ta kuma ba ta wani ƙaramin akwati.

Amma Ruqayya ba ta taɓa buɗe shi ba.

Saboda ta ji tsoron abin da ke ciki.

Yanzu...

Ta fitar da shi.

A ciki akwai hoton Amina da jaririyar Maryam.

Da kuma wata wasiƙa.

An rubuta:

"Ga Maryam Zahra, idan ranar gaskiya ta zo."


---

Ruqayya ta rungume wasiƙar tana kuka.

Domin ta fahimci abu ɗaya:

Ba wai kawai ta rasa ƙaunar Maryam ba...

Ta rasa damar zama uwa ga wata sarauniya.


---

A wannan daren, Ruqayya ta yanke shawara.

Ba za ta gudu daga kuskurenta ba.

Za ta je Nurayn.

Ba domin neman gafara kawai ba.

Sai domin ta faɗi gaskiyar da ta ɓoye.

Domin akwai wani abu da ita kaɗai ta sani...

Wani abu da zai iya taimakawa Maryam gano wanda ya kashe mahaifiyarta.


---

Amma tambayar ita ce...

Shin Maryam za ta iya gafarta wa matar da ta ci amanar amanar mahaifiyarta?

Ko kuwa wasu raunukan suna barin tabo har abada?

— ƘARSHEN CHAPTER 23 —