18
by @sadisakhna
____👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (18)*👑
Sai bayan la'asar liss nasamu damar gano ɗakin dayake,a hankali na buɗe asabarin dayake baƙin ɗakin na shiga.
Yana kwance akan katifar auduga,kansa yana kallon sama,akan ƙirjinsa kuma wani mayafine a jike da ruwa. Abokinnasa yake manna masa idan yayi ɗumi yacire yasake manna masa wani.
Harna ƙarisa wajen dukkansu babu wanda yaɗaga ido ya kalleni. Saboda shi marar lafiya yana kwance yana fama da kansa,yayinda abokinsa kuma shima hankalin sa yana kansa,ɗan gyaran murya nayi kafin ya ɗago ya kalleni,babu yabo ba fallasa muka gaisa. Nabashi uzurina na rashin zuwa akan kari.
Maganin dana haɗa jiya da ciro a gefen rigata na miƙawa abokinnasa, har ya miƙo zai karba yayi saurin dakatar dashi tareda cewa yatafi ni zanyi masa. Abun yabani mamaki wannan wanne irin bawa ne mai cikeda kwarjini,kyau da kuma jiji dakai,karon farko kenan danaga wani bawan yanayim kaman wani sarki a gaban sauran bayi. Ko daƙika ɗaya kuwa bai ƙara ba yafice daga ɗakin. Inda ya tashi naje na zauna a hankali tareda zura masa ido.
"Karon farko naga bawa mai abin mamaki,ka karya shedar ba'a kawo bayi nan wajen koda kuwa suna kan gabar mutuwane,sannan sai kayita ɗaga kai koda a gaban ƴaƴan sarauta ne,gashi hakan yakai ga har sun jawo maka ciwo"
Kallona yayi kana yayi ɗan taƙaitaccen murmushi,lokaci guda naji notin kaina ya kusa kuncewa,nace bazan taba auren bawa ba,harsai nayi gwagwarmaya nazama mai ƴan ci sannan na auri ɗa. Ta hakanne zan ceci zuri'armu daga ƙarewa a matsayin bayi. To amma wannan yana wulgawa ta gabana hakan zayyi wu kuwa?
"Waye ya sanar dake cewar sune suka jimin ciwon,kodayake ina bata yawun bakina ne,inaga bayanni da nakejin ciwon babu na biyu dayafi sanin tasirin da ciwon yayi min saboda ke,tunda batareda izinina ba kikayi katsalandan na dubani. Ko haka duk masu aikin jinya suke?"
"Waye yace maka ni mai aikin jinya ce bayan ban sanar dakai ba?"
"Uhmm Joda kenan"
"Ohh wato har sunana ma saida kabi ka sani alhalin kana halin jinya,to kayi ƙoƙari. Yanzu dai kasha magani tukunna,dui da naga kaman ka warke tunda kake zuba wannan surutun"
Na faɗa ina miƙamasa ƙoƙon hannuna dauke da maganin dana haɗa jiya,saina tafasashi da ruwan ya huce zuwa dan ɗumi ɗumi. Karba yayi babu musu ya shanye kana yamiƙomin ƙoƙon.
"To kasha na yammaci kenan yanzu saina safe kuma,ga yanda za'a dunga haɗashi da farko za'a..........."
"Waye zayyi wakikewa wannan bayanin,nida nake kwance banida lafiya kokuma bangon ɗakin"
"To zanyiwa mai jinyar naka bayani kuma ka koreshi, kaga kuwa tunda bayanan ai sai nayi maka bayani ko"
"Kinada abin dariya Joda,to akwai mai yin jinyar tawa dayawuce ke,tunda kika bincika kika gano matsalata to kuwa kece zakiyi maganinta. Dan haka karki wani bata yawun bakinki wajen yimin bayani domin ba fahimta zanyi ba"
"Tunda bazaka fahimci magani ba to barina yimaka bayanin abinda zaka kikaye.
Da farko Jininka yana cikin halin jinya,yayi rauni amma ba mai tsanani ba da sai anyi ƙaho. Iya magani ma dacin abincin daya dace sannan kuma da ɗaukar matakan kariya ya wadatar.
Wannan haɗin maganin kullum zaka dunga sha safe da yamma,Dolene ka kore duk wani abu dazai haifar maka da tunani,domin Ruhin da baya samun hutu yana tareda jinya a kodayaushe. Sannan kujewa cin Abinci mai nauyi sosai da maiƙo,wannan dukka zan bincika abincin daya kamata ka dunga ci a kullum.
Sannan wannan zafin ƙirjin da kake fama dashi Rashin gudun jini yanda yakamata ne yake sakawa jiki ya tare zafi a ƙirjinka,shima idan ana magani kuma ana kula komai zaixo da sauƙi. Shin babu damuwa idan naji Bugun zuciyarka?"
Tunda na fara bayanin yake kallona na rasa mai yagani a tattare dani haka.
Ƙirjinsa ya buɗemin daidai inda hatimin zakin yake,batareda yacemin komai ba.
Saurin sunkuyar dakaina nayi,domin haka kawai naji tsikar jikina ta tashi da kallon kwantacciyar sumar dake kan ƙirjinnasa.
"Ahah kota hannunka zan iya ji shima zai wadatar"
Na faɗa ina mika hannu zan riƙe hannunsa, wani laushi naji da santsi dana kama hannunsa,wannan ai ko hannun mace albarka ballantana kuma na namiji,ikon Allah.
A haka nagama duk wani bincike dazanyi masa kafin na nufi hanyar ƙofa zan fita.
"Na sallameki ne kika kama hanya zaki fita"
Juyowa nayi na kalleshi,wai wannan mai ya ɗauki kansa ne? Nace a raina,a fili kuwa ɗan murmushi nayi tareda cewa.
"Naga nayi maka dukkan abinda jikinka ke buƙata a yanxun,inada wani uzuri da zanyi sannan idan na fita zan turo maka abokinnaka ya zauna tareda kai"
"Bashi nake buƙata ya zauna dani ba,ke nake buƙata ki zauna dani,ba yanzu kikace na dunga yin abinda zai farantamin rai ba,sannan na guji kaɗaici da abinda ke sakani tunani dakuma bacin rai. To tafiyarki shine abinda zaisakani tunani dakuma bacin rai,dan haka kizo ki zauna dani. Ko bakyaso kici jarrabawar da aka baki akaina?"
Zaro ido nayi ina kallonsa,wai wannan waye shi haƙika yana wuce gona da iri wajen sanin dukkan bayanai daya shafeni,miye alaƙarsa da Gurinnan alhali yana matsayin bawa.
"Karki zurfafa tunani da nisa,kina hana wani kekuma kinayi. Ancemin mai kulada jinyata zataxo kuma nine Jarrabawarta,idan ta faɗi zata cigaba da zama a wannan wajen,idan kuma tayi nasarar yimin magani na samu lafiya to za'a saka mata da ƴan ci a matsayin kyautarta sannan............"
Tun kafin ya ƙarisa maganar bansan lokacin danayi tsalle na koma gefensa ba,bakina a washe kaman am cemin ga yancin yanzu haka.
"Dagaske dan Allah haka baba Almahdi yace,yan cine kyautar dazai bani?"
"Uhm tantama ma kike kenan,to shikenan bari idan yaxo zance ya sauyamin mai kulada ni akawomin wata daban"
"Ahah dan Allah kada kamin haka,nayi maka alƙawarin zanyi yadda kace,kuma zanyi iya ƙoƙarina wajen kulawa dakai harka warke"
"To shikenan na haƙura,yanzu dai ƙara min wannan dafa hannun kiji mai yake damuna"
Ɗan jimm nayi tareda kallonsa,hakan ya tabbatar min dagaske yakeyi kenan, babu yanda na iya haka nasaka hannuna tareda rufe idona,wajen shuru ne babu komai sai bugun zuciyoyinmu wanda a hankali suka fara bugawa a tare,duk da cewar tasa akwai rauni a ciki amma sai naji kaman tana kara sauri alamar tana so ta iso tawa zuciyar. Wani abu kaman zare naji ya haɗamu waje guda ta jikin hannuna. Ji nayi kaman ruhinmu ya haɗu waje guda ya lula cikin wata da'ira mai sanyi da saka nutsuwa. Kwatsam kuma sai naji wani baƙon yanayi yafara ziyartar zuciyata. Ƙoƙarin janye hannuna nafarayi,amma sai naji yasaka nasa hannu ya danne nawa akan ƙirjinsa wajen guda.
Kuma du wani abune naji kaman zare yana fitowa daga zuciyata tana kewaye tasa zuciyar,a lokacin da hakan yake faruwa sai bugun zuciyarsa yafara ƙaruwa ƙadan kadan da sauri sauri.......jin kaman wani abu yana zanyeni mai shagaltar da duk mai jinsa yasakani saurin ɗauke hannuna daga ƙirjinnasa. Buɗe idona nayi daidai lokacin da shima ya buɗe nasa idon. Kallo kallo muka farayi bana iya kan ƙwayar ido ba sai kaman kowa na kallon ruhin kowa.
Saurin ɗauke nawa idon nayi zuwa lokacin jikina banda rawa babu abinda yakeyi,wannan baƙon al'amarin daya shigeni ban taba jinsa ba sai yau. Haka kawai nakejin kaman wannan zaren zaren Ƙaddarane mai tafiya da babban ƙalubale.
Nasan wannan tunanin bazai tana barina ba har bacci ya ɗaukeni.
***
(Hammar)
Dukkan yanayin da taji a tattareda haɗuwar ruhinmu nima najishi a cikin raina. Lokaci ɗaya tun bayan dana buɗi idona dayin wayo naji zuciyata ta nutsu da wanzuwar wata ruhi a gefenta, Tun ranar dana fara kallonta naji wani abu a jikina gameda ita,banason bayi banason mu'amala dasu,amma kuma kallonta danayi yasa naji ina son Bayyana a gabanta a matsayin bawa,abinda ko a mafarki ban taba tunanin yi ba. Yanzu kuma da duk wata daƙiƙa da nake karayi da ita,sai take sake sauyamin daya yanda nasanta zuwa fiyeda haka. Baiwarta fikirarta dakuma yanayin da take tafiyar da al'amuranta abune mai ban sha'awa ga duk wanda yakeson zama da mace wacce yakeso ta zama bango a gareshi,wanda in aka turashi zata yi masa waigi. To amma duk waɗannan abubuwan sai suka ta'allaƙa ga baiwa wacce kowa keyiwa kallon ƙasƙantacciya,ciki kuwa harda ni.
Bayan ta zare hannunta daga ƙirjina sai naji wannan lullubin nishaɗin da kwanciyar hankalin dukka yabarni,tamkar ina tsakiyar sahara a lullube da bargo mai ni'ima an yayeni. Saidai kuma duk da haka naji zuciyata ta rage kaso mafi tsoka daga zogin datake yimin shekara da shekaru. Ko naƙi konaso zaren ƙaddarata da wannan baiwar ya ɗauru,abinda banawa kallon daraja shi aka miƙawa ragamar nutsuwata a gareshi. Ganin taja da baya zata fita jinayi kamar na tashi na hanata fita,to amma babu halin hakan. Dan nasan abinda nakeji a yanzu haka ya ninka wanda ita taji,kawai dai dayake na ƙware wajen iya boye abinda yake damuna,shiyasa ba kowane zai fuskanci halinda nake ciki ba.
Shuru nayi tareda rufe idona,ina jin yanda ɗakin yayimin kadaici dayawa,ji nake kaman ta tafi da dukkan walwalata. Banso na faɗamata cewar tukwicinta ƴan cine ba,naso sai komai yazo ƙarshe nasanar mata,to amma nayi hakanne saboda tayi duk abinda na umarce ta dayi. Domin ni banason ana cemin ahah idan nace ayi abu. Naga alamar itakuma bazamu shirya akan hakan ba. Batason zama a ƙarƙashin ikon wani da alama,shiyasa inaga take muradin son ƴan ci. Yanzu abu na gaba shine fitarda ita a waccar gasar,saboda ni nakeson kambun nasarar,nasan kuma yanda takeda fikira zata gwara da kowa akan samunsa,nima kuma saboda ɗaga darajata bazan bari kowa ya karba ba...... Kiyi haƙuri Joda da amfani dazanyi dake na ɗan wani lokaci,inason yin wannan gasar amma bazayyiwu ba ina a halin jinya,koba komai amma bazakiyi biyu babu ba tunda zaki samu tukwicin ƴan ci........
Nayi zurfi a cikin tunani na naji shigowar Fasih Hadimina. A hankali na buɗe ido na kalleshi tareda cewa.
"Ina magani na"
"Ranka ya daɗe wanne magani,bata bani magani ba ai data fita"
"Ita nake nufi da magani na ba wani ba,idan tana gefena sai naji tamkar babu wani abu dazai ɗagamin hankali a duniyar nan"
"Ranka ya daɗe baiwa ce fah,idan ita tana maka kallon bawa ai kai kasan ita baiwa ce ranka yadaɗe,inda zaka bani dama zan fahimtar da ita ta dunga baka girmanka. Sannan mai martaba Baice ka maida kanka bawa ba ranka yadaɗe,kawai yace kayi badda kama ta yanda baza'a ganeka ba. Amma zama a matsayin bawa girmanka ya wuce nan mai girma magajin babbar daula"
"Banaso ta dungayimin kallon da takeyiwa sauran yayan manya,inaso naga ainihin zahirinta bawai bangaren Tsoronta da kuma tsanarta ga masu mulki ba. Nutsuwa nakeson samu daga gareta ba tsoro ba. Sannan shi kansa gasar idan na cinyeta ina matsayin bawa mai kake tunanin matsayina zaikai?"
"Zaka zama gagara badau ranka ya daɗe,hakan zaisa matsayinka ya tashi sosai,sannan kuma ka zama sarkin da zai iya jure duk wani ƙalubale kuma yayi nasara"
"To idan hakane inason na jefi tsutsu biyu da dutse ɗaya ta hanyar zamana a matsayin bawa. Inason a duk lokacin data shigo bani magani ka fita itace zatayimin komai inaso kallon cikin idanuwanta idan ina bata mamaki da maganganu na, tayi daraja dayawa tazo a matsayin baiwa,saidai Allah ne kadai ya barwa kansa sani. Juyawa nayi na kwanta,Kaina da zuciyata cikeda tunanin sabuwar halittar danayi gamo da ita a kwanakin da basu wuce uku ba.
Wasa wasa an shafe sati Ina ɗakin jinya sannan kullum da safe kafin ta tafi Wajen ɗaukar darasi zata biyo ta tabbatar nasha magani,wani lokacin na zolayeta ta hanyar kafa mata sharaɗi da kuma bata umarni,wanda na kula ko kaɗan batason hakan. Idan ta tasoma zatazo ta ganni hakama idan dare yayi zatazo tabani magani. Takanyi wasu abubuwan datasan inaso domin sakani nishaɗi,wanda nasan duk yana cikin Hanyoyin saka ruhina cikin walwalam a hankali Fasih wanda ya sauya suna zuwa Fasih yafara janyewa daxuwa,saboda shima yana cikin gasar,rashin ganinmu mu biyu za'a zargi wani abun,amma idan ni kaɗaine ba lallai a kulaba,Fasihmma dayazama kowa yasan cewar wasu daga cikin ɗaliban sun jimin ciwo. Yanzu joda ce kaɗai take kuladani indai bata wajena to tafi gurin karatu,sanin hatsarin ƴaƴan manya dakuma tasirin abinda zasu iya aikatawa, Fasihmman ga ita da take da kaifin kwakwalwa yasa nace a cireta daga cikin gasar. Nasan zansha rigima amma kuma na tanadi amsar dazan bata.
*****
(Joda)
Tun ina Jin shakkarsa har yazamto nafara sakewa dashi,amma duk da haka abinda nakeji akan sa maimakon ya ragu saima ƙaruwa dayakeyi, nakula mutum ne shi mai magana kai tsaye idan yanason abu batareda boye boye ba,ga saka umarni kaman shine sarkin gari. Tun ina mita har nazo nafara sabawa,Fasihmman danaga cewar halinsa ne ba dainawa zayyi ba. Yana samun sauƙi sosai,wanda hakan yasaka na zage dantse wajen yin bincike akan dukkan abinda yashafi Zuciya,jini da kuma garkuwar jiki. Saboda na tabbatar nayi masa dukkan abinda yake buƙata, yana warkewa zan samu ƴanci shikenan nan na zama tsutsuwar data fito daga keji.
Ina tafe ina ayyana hakan a raina ina dariya,sai kawai ji nai nayi karo da mutum har ya zubar abinda yake hannun sa.
Jalilah ce ya subhanallah shikenan nikam kashina a bushe a duburata babu ranar fita.
Hannuna na haɗa zan bata haƙuri Fasihmman ganin Akwashin abincinta kwacab a ƙasa. La haula miyasa Ƙaddarar abinci take haɗamune da wannan jikar ifritin a duniyar rashin mutuncin da rashin imani.
"Karki kuskura karki kuskura ki tsugunna domin bani haƙuri,saboda hakan ko kaɗan bazai amfaneki da komai ba sai ƙarin hukunci,da farko tsugunna ki cinye abincin da kika zubar."
Kallon abincin nakeyi a ƙasa,sauran suna ji an ce na tsugunna na cinye suka fara tofa yawu akai,wata harda takawa da takalmi tana min kallon mugunta mai haɗe da ɗan guntun murmushi.
Nikuwa nace a raina wlh ko zasu kasheni baxan ci ba, wannan ai cin fuska ne,ko kare bazaici ba ballantana ni mutum mai cikakken hankali.
Magana suka farayi akan na tsugunna na cinye,amma ina tsaye ƙiƙam kaman an gina dutse. Mari Jalila ta kwasamin,bance komai ba na dafe wajen ina cije baki . duk da ni nayi mata laifin to amma su suwaye da idan aka basu haƙuri bazasuyi ba,sai kace sune mala'iku masu gadin wuta.
"Kiyi haƙuri banyi akan sani ba kuma na baki haƙuri,amma wlh ko kasheni xakiyi bazan ci wannan ƙazamin abincin ba"
Juyawa nayi zan tafi,kawai naji wata a cikinsu ta fizgoni,ina juyawa naga ɗaya daga cikin bayin da suka shigo gasarne,wanda ko sunansu ma ban sani ba.
Babu zato babu tsammani suka rufeni da duka ta ko ina,dan ma Allah yasa nima na yunƙura ina kaimusu naushi da dukkan ƙarfina,ko kaɗan faɗa da kokuwa baya cikin tsarina,amma tunda shiyazo ya sameni yazama dole nima na maida martani.
Biyu yafi ɗaya Fasihmman da ba iya faɗan nayi ba,duk da ina tsaye kan ƙafafuna amma kuma sunyimin rauni sosai. Abinda yabani mamaki su kuma mai nasu dazasu dakeni,bayan nida su duk kanwar ja ce,sai a lokacin nagane sunyi hakanne domin su tare nasu na gaba,so suke su zama karnukan farautar su,ba wai zomayen daza'a farauta ba.
Gefe na kalla,mu muna tsaye muna hakin kokuwar da muka sha,su kuma suna gefe a kwance cikin kwanciyar hankali suna shewa. Sake kallon bayin nayi cikeda takaici,naka dai bazai taba sauyawa ba.
Jijjiga kai nayi cikeda takaici na ma bar sansanin gaba ɗaya. Ɗakin da Hammar yake na nufa, don saida nayi ta tambayar sa kafin yafaɗamin sunansa,kodan yasan cewa sunan nasa da ɗadine shiyasa yake yangarsa,ban taba ganin bawa mai aji ba kamarsa,ta ko ina komai nasa dabanne.
Lokacin dana shiga ɗakin shikaɗaine yana bacci,kokuma rufe idonsa kawai yayi,yanayin yanda ƙirjinsa yake ɗagawa in yana numfashi ya nuna yasamu lafiya sosai, man tafarnuwa na ɗauka wanda aka kwabashi da zuma na nufi inda yake,da alama yayi wanka kuma bai sake shafa wani ba. A hankali nafara lakuta ina shafa masa ƙirjinsa inayi ne hankalina yana kan abinda yafaru a wajen karatun namu. Ban kulaba ashe ina shafa hannuna akan ƙirjinsa wanda yake santsi saboda man dana shafa masa. Saida naji muryarsa kafin na farga da abinda nakeyi.
Shafa maganin bai isa bane haka,ko dai dan kinji fata mai laushi ba irin taki ba.
Matsawa gefe nayi ina rarraba ido na kunya,gabaɗaya ban kulada idonsa dayake kaina ba sam.
"Menene haka a fuskarki naga duk ta kumbura hannunki kuma duk ciwo?"
"Babu komai wata yar matsalace tsakanina da abokaina"
"Joda kenan har kin manta inda muka haɗu da har kikemin karya,nasan bazai wuce waɗannan ƙoɗaɗɗun ƴan matan nan ba"
Zaro ido nayi ina masa alamar yayi shuru.
"Kabar faɗin haka,dokane bawa baya zagin mai ƴanci,duk da kana ganinka bawa mai gata amma duk da haka matsayin doki ya wuce na alfadari,basu bane ƴan uwana bayine sukayimin haka don na taba mai ƴanci,saboda sunason zama karnukan farautarsu,amma ba wata matsala yanzu komai ya wuce"
"Uhmm to ai shikenan,yanzu dai kije ki haɗomin abinci naci,yunwa nakeji banci komai ba yau,kinsaba sai kin biyo tanan kike tafiya majalisi amma yau kikayi wucewarki,gashinan alhakin ɗan bawan Allah yakamaki"
Murmushi nayi taƙaitacce kafin na fita zuwa madafar dake bangaren Jinyar,iya abincin da marasa lafiya zasu bukata akeyi kaɗai a wajen. Koren ganyen shayi nasa aka haɗa masa mai zuma. Saikuma alkubus da miyar alayyahu wanda yaji Gyaɗa.
Yaci sosai kuwa,don kullum idan nakawo masa abinci sai ya yaba daɗinsa,wani lokacin idan inason yaci wani nau'in abinci amma basuda shi haka nake dagewa na dafa masa, babu abinda nake kallo a tattare dashi sai ƴanci na. Wanda nakejin zanyi komai indai ban sabawa shari'ah ba dominsa.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow