AHALIN HARIJAI

9&10

by @autaralheri

💫💫💫💫💫💫💫💫
   *😘AHALIN HARIJAI😘*
🫣🫣🫣🫣🫣🫣🫣🫣

   Special Book👌
 
      Writer by 
 
         Autar alheri ✍️
💫💫💫
💫💫💫💫
💫💫💫
👄👄👄👄👄👄👄👄
😘😘😘
👄👄
👄
Romantic love with  hot sexy story 🥳🥳🔥🔥🔥

Wannan book ɗin babu gawraye acikinsa 🧏 idan dai har kinsan/kasan, bakuda aure to ina baku haƙuri acikin wannan tafiyar.🙏


Book 1
Page 9&10

End free. 


"Cikin ikon Allah kuwa yaɗaga tana gab da tsinkewa. Dasauri Dr yaƙub yace "Assalamu'alaikum Yaa Sheikh barka da dare...ɗan shiru yayi kafin ya amsa cikin kamilallaiyar muryarshi, yace "wa'alaikassalam.  "Affuwan yaa Sheikh nakiraka yanzu, wlh wata emergency patient ce mukeda ita, sedai duk iya abinda ya dace munyi amma wlh kamarma batada rai, sedai computer na nuna mana tana raye amma sam bata nomfashi, kusan awa huɗu muna akanta amma wlh ba abinda yasauya, shine muke neman alfarma dan Allah kozaka temaka mana muceci rayuwarta dan Allah. Yafaɗa yana ɗan murmushi domin yasan doline se sheikh yazo tunda har yahaɗashi da Allah, dama abinda bayaso kenan ahaɗashi da Allah ga abinda akasan bazeyiba domin  komi wahalar abu indai ka haɗashi da Allah to zeyi muddin abin besaɓawa Allah da manzonsaba. Ajiyar zuciya ya sauke cikin kanewarsa yace "zanzo in sha Allah. Daga hakan ya yanke wayarshi. "Alhmdllh gashinan zuwa, cewar Dr yaƙub cikin farin ciki. "To baradai yazo ɗin mugani ni wlh nasan abune me wahala koyazo yadubata tunda mace ce, dama yafaɗa atsarin aikinshi babu mata, dudda kuwa yasan matsalarsu tamkar yunwar cikinshi, amma sam baya taɓa duba mace. "To mujira dai zuwanshi bara musanarda iyayenta domin hankalinsu ya kwanta, cewar Dr Musa, yafice faga room ɗin. Aiko suna ganinshi duk suka taso suna tambayarshi  yaya jikin nata. "Kuyi haƙuri in sha Allah zata samu lafiya. "To amma minene ke damunta doctor? "Nima abinda nakeson sani kenan shiyasa muka kira babban doctor zezo yanzu yadubata yadda zamusan matsalarta in sha Allah. "To Allah yabata lafiya, cewar baba. Sauran kam jugum kawai suke suna jiran tsammani, sukuwa ƴammatan da iyayensu mata kuka kawai suke domin duk gani suke Ayat tarasu kawai suna ɓoye musune. 

Bayan minti 40 dayin waya da Sheikh Faisal segashi yashigo cikin asibitin cikin kamewarshi, excort ɗinshi duk sun zagaye shi, sanye yake da alkabba yaɗora hularta akanshi domin  ƙaramar hulace yasaka irin wadda ake kira, taɓanni kasha hadisi. Shiyasa yafora hular alkabbar, daga cikin  kuwa riga da wando ne ya saka irinna buzaye masu kamada Pakistan, kana yasaka ɗan siririn glass yarufe ƙwayar idonshi dashi. Tunda yadoso cikin doguwar barandar idon ahalin Ayat na kanshi, domin kamalarshi kaɗai ta isa akalleshi, balle ga hassken Alqurani atare dashi, dudda basuganin fuskarshi amma baƙaramin burkesu yayiba. Dayazo ta kusansu kuwa kafin yawuce seda yayi musu sallah dudda excort ɗinshi basuso hakan ba amma seda yabawa su abba hannu suka gaisa cikin mutuntawa, harsu yaa khamal duk seda yabasu hannu, domin yana gama gaisawa dasu abba, Suma duk suka bashi hannu, hakan yasa ya tsaya suma ya gaisa dasu, kafin yaƙarasa cikin doctor's room ɗin. 

Da sauri duk suka taso suna gaidashi, "where is patient? "She's here yaa sheikh, suka faɗa suna nunamai inda suka naidata, cikin wani room dake ɗauke da na'urori. Ƙarasawa yayi cikin room ɗin, sedai kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kanshi, ganinta mace, juyawa yayi zuwa office ɗinshi, yace sukawomai binciken da sukayi yagani. Ba musu kuwa suka kawomai, yaduba,  kanshi ya girgiza domin shima bega wata matsala atare da itaba, umurni yabasu suje susakata a computer yana gaya musu yadda zasuyi, sukaje suka fara aikinsu, cikin bin umurninshi, duk abinda yace suyi shi sukeyi, kusan awa ɗaya, ana cikin hakan ta fara, numfashi, sekawai Dr Musa yayi mata wata allura kuma yajona ingi shaƙar numfashi, batare da yajira umurnin Sheikh ba, haba ai atake tafara wata irin zazzaga, idonta nayi wani irin turowa, cikin mugun tashin hankali Dr yaƙub ya shiga salati yana dokawa doctor sheik kira, afirgice, ya fito dagudu zuwa gunshi. Shima dafe da kai yasameshi yanajin haushin abinda doctor Musa yayi, sedai be iya faɗa ba domin tabbas daya iya faɗa a wannan lokacin se doctor Musa yaji babu daɗi. "Dan girman Allah yaa Sheikh kaceci rayuwar waccan yarinyar zata iya mutuwa yanzu, zokaga yadda takeyi. "I can't yaƙub but you can call dr nadiya idan tana ƙasar, she's help her in sha Allah. Yafaɗa yana ƙoƙarin kwashe wayoyinshi...idon Dr yaƙub harsun cika da kwallah yace "Dr nadiya bata cairo yaa Sheikh yarinyar nan zata iya mutuwa wlh, ceton raine zakayi dan Allah. "Stop yaƙub karka soma haɗani da Allah, domin kasan bazeyuba, ba abinda zan iya akai domin bawai anrasa wata mafitar bane, kuma koma miye zanyi mata sena taɓata, to tayaya zanyi hakan tunda ba muharramata bace? Ko kanaso na saɓawa Allah ne kawai dan zanceci rayuwarta? Ai likitanci ba hauka bane domin duk abinda zamuyi arayuwa Allah ya tsara manashi acikin Alqurani megirma, shiyasa  komai na ƴan Adam Allah yayishi jinsi biyu. Kuma idan har anyi kuskurenyin wani abin to se idan da lalura, wannan kuma batakai lalurar dazan saɓawa mahaliccina akantaba, kuje kuyi mata DfR injection kafin nan da awa biyu zan turo mace tadubata., yaƙarasa zancen yana dafe kanshi. Domin baƙaramin jigata yayiba da wannan dogon surutun da yayi. 

Jiki asanyaye Dr yaƙub yafito, yana  fitowa sukayo kanshi suna tambayar ko andace, cikin sanyin murya yace "I'm sorry to sey Amma zata iya mutuwa aco wani lokaci. Ihu matan suka ɗauka mazan kuma suna salati. Shima ƙwallar idonshi ya share domin betaɓa haɗuwa da patient ɗinda tabashi tausayiba irinta, cikin dakiya yace "mafita ɗaya mukeda ita, itace wannan bayan Allah daya shigo yanzu Sheikh Faisal, dama mun kirashine sabida matsalarta se dubamana har mushawo kan matsalar sedai cikin rashin sa'a komai ya lalace, shine kawai ze iya temakawa yaceto rayuwarta, sedai shikuma baya duba mata, nayi yadda zan iya domin yatemaka yadubata amma yaƙi amincewa, tace baze dubataba tunda ba muharramarshi bace, kuma baze taɓa sabawa Allah ba dasaninshi, sedai muje muyi mata allura zeturo mace tadubata, to ba iyawace macen bazatayiba, inda matsalar take kafin tazone, komi ze iya faruwa da yarinyar, kuma nasan wlh ba yadda za'ayi yayihakan tunda ya ɗauki haka matsayin saɓon Allah, abu ɗaya zakuyi shine kuyi ƙoƙarin haɗashi da Allah idan yafito, domin ni yahanani wannan damar, idan kuka haɗashi da Allah kobaze dubataba to baze tafiba haryaga ansamu wanda yadubata domin duk abinda akace Allah tozeyishi koda kuwa zecutu. Ajiyar zuciya su Abba suka sauke ga ƙoshi ga kwanan yunwa, kuma tabbas wannan matashin malamin yafisu gaskiya kawai mutane sun kasa fahimtar addinine yadda yadace, se afake da ceton rai ana saɓawa Allah. Sun nan tsaye kowa da abinda yake saƙawa arashi, kawai sega doctor Faisal yafito cikin kamewarshi excort ɗinshi na biye dashi abaya. Ai cikin sauri yaa khamal yasha gaban Sheikh Faisal, tareda zubewa akan guywoyinshi, yaɗaga hannunshi sama tareda buɗe baki zeyi magana kenan, ɗaya daga cikin excort ɗinshi ya cakumo wuyan yaa khamal tareda ɗaga bindiga zedoka mishi. Cikin sauri Sheikh yace "aa Bashir miye haka, sakeshi nace. Yafaɗa akame. "Affuwan Yaa Sheikh, yafaɗa tareda sakin yaa khamal ɗin. "Miyafaru ne kataremin hanya bawan Allah? Yatambaya cikin kamala. "Cikin rawar murya yaa khamal yace "yaa Sheikh kadubi girman Allah dazatinsa, kayiwa soyayyar fiyayyen halitta kaceci rayuwar ƙanwata dan Allah doctor. Ai wani irin runtse ido Sheikh yayi da ƙarfi yanajin yadda zuciyarshi ke lugude, domin khamal yaɗaureshi da jijiyoyin jikinshi. Kafin yayi wani dogon motsi yaga nasir abdul, mudassir sameen, mufeeda, balkusa, abida, duk sun zube agabanshi suna ruƙonshi suna kuka. Ai cikin tashin hankali yace "innalillahi wani'inna ilaihirajiun. Pls kutashi dan Allah, yafaɗa kamar zeyi kuka, aiko cikin sauri duk suka miƙe sedai dukkansu hawaye sukeyi. Ajiyar zuciya ya ɗauke kafin yace "kun haɗani da Allah akan abinda idan nayishi saɓawane agunshi, kun haɗani da Allah akan abinda bazan iyaba, sedai banida zaɓi akan wannan lamari domin duk wanda yace Allah yagama zance, sedai inaso kusani bazan iya taɓa wannan yarinyar ba domin ita ɗin ba muharramata bace, banida muhurin taɓata har agurin Allah, sedai zan Nemo wadda zata dubata yanzu in sha Allah dan Allah ku kwantar da hankalinku... dukkansu shiru sukayi jin yana kan ra'ayinshi, shiko abba tunanin dayakeyi daban, cikin dattako ya kalli Sheikh Faisal yace "haƙiƙa kafimu gaskiya Sheikh domin duk wanda yasan dokokin Allah baze yadda yatakasuba se wanda shedan keyiwa huɗuba, sabida hakan nake roƙar wata alfarma awurinka,  kuma Allah zakayiwa baniba domin kaceto rayuwar Ayatullah, dan Allah ka auri Ayat ayanzu idan ka amince wlh zan ɗaura muku aure...ai wani irin waro ido Sheikh yayi gabanshi na tsananta faɗuwa cikin tashin hankali yake kallon abba da tsananin mamaki. Shiko Abba bedamuba yacigaba cewa " kaga tazama muharramarka seka dubata, idan Allah yabata lafiya seka sahale mata amma dan Allah kayimin wannan alfarmar kaceci rayuwarta dan Allah. Yaƙarasa zance yana haɗe hannayenshi wuri ɗaya. Aiko duk su yaa Abdul duka dasu baba, su Dr yaƙub duk sukayi na'am dakalaman abba, suna cewa "wannan gaskiya ne idan akayi haka ansamu mafita in sha Allah. Kafin  yayi wata maganar sega Dr salis yafito dagudu yana faɗar "pls Yaa Sheikh help, waccan yarinyar jini take zubarwar sosai sabida allurar da doctor Musa yayi mata dan Allah mizamuyi akai? Ƙarjininta ya ƙare. Ihu ƴanmatan suka ɗauka da kuka lokaci ɗaya, su kuma mazan suna kiran Allah. Ido Sheikh ya runtse da ƙarfi kafin ya kalli ɗaya daga cikin  excort ɗinshi yace "bani ɗaya cer key dake hannunka. Babu musu yamiƙamai, miƙawa abba yayi  cikin kamewarshi yace "ga sadakinta idan yayi muku banada kuɗi ne ajikina yanzu, idan kuma zaku jira na ɗauko kuɗin semuje a ɗauko, yafaɗa cikin kamewa. "Yayi yayi wlh kuma munbaka kawai a ɗaura, duk suka faɗa atare, anan cikin doguwar barandar duk suka tsugunna aka ɗaura auren Ayatullah da Sheikh Faisal, inda family ta da excort ɗinshi, harda su doctor yaƙub suka zama shedu, cikin ƙanƙanen lokaci aka ɗaura auren da babu shiri balle tsammani, ana shafa fatiha yamiƙe cikin kamalarshi yanufi room ɗin da aka ajiyeta, sukuwa ajiyar zuciya suka shiga saukewa suna fatar Allah yabata lafiya.....! 

END

Free page yaƙare 🙏
Duk wadda ke buƙatar wannan cigaban wannan book zata iya biyan kuɗinta. 

AHALIN HARIJAI Paid book ne kibiya kuɗinki abaki, 1k kacal 👌
9112799371 moneypiont sha'awanatu kasim,ƴan Niger na zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉*** My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 *** on WhatsApp 🙏






Autar alheri✍️