20
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (20)*👑
Bayan Shekara ɗaya da rabi.
*** *** ***
Aminatou ce take gudu tanason Kama Sultan ɗan ƙaramin yaro da bai wuce shekara uku da rabi ba. Ko yaushe idan zata shiryashi haka suke fama. Batason binsa da gudu saboda tsoron kar ya faɗi tayi laifi. Amma ta makaro domin waiwayowar da zayyi baiga me yake gabansa ba yayi tuntube ya faɗi. Daidai lokacin da Gimbiya Asmah ta shigo harabar sashennata ta kalli yaronta a kife yana kuka,bakinsa ya fashe har jini yana zuba.
Bakaramin firgici Aminatou tashiga ba domin tasan yau ɗin Allah ne kaɗai zai ce ceta daga hannun Gimbiya Asmah wacce batada mutunci ko kaɗan. Tana isowa inda take kuwa ta kifeta da mari,babu tantamar ta girmeta har ta kusa haifarta haka ta yanke ɗanyen hukunci mai cikeda tozarci.
"Ke Jahilar ina ce kuma marar imani dazaki dunga bin yaro ƙarami da gudu,yaron ma yariman masarautar nan,kinsan hukuncinki kuma idan har yasamu mummunan rauni. Maza ki ɗaukeshi kuje ciki ki rarrasheshi kiyi masa duk abinda yakeso. Idan na kuma sake cin karo da irin wannan gangancin saina saka a yanke miki hukunci. Sa'ar ki ɗaya duk cikin bayin danake tareda su dake kaɗai ya dogara,badan hakaba da sai kinga abinda yabiyo ba, mtsewww Jaka kawai."
Tashi tayi daga tsugunnon da take ta matsa inda Ameer ke kwance ta ɗaukeshi,sai mimmiƙewa yakeyi irinna yara sakalai.
Bayan sun bar wajen itama tura ƙaton cikinta tayi wanda yashiga wata na bakwai amma kaman yau zata haihu don girma,har yafi na Ameer girma da kuma bata wahala. Saboda na farkon hadda raki da shagwaba,wannan kuwa wahalar ce take jinta muraran.
Sashen mijinta ta nufa tana huci da numfarfashi dan ita kadai ma cika take tana batsewa saboda fushi irinna masu ciki. Daga wajen zagayawa take inda acan ma saida sukayi ƴar tsama da gimbiya meerah,hakanne yasa bata wani daɗe ba kaman yanda saba ta dawo.
Bata nemi iso ba haka ta tura kanta cikin sashennasa,tun kafin ta isa takejin gurnani da nishi. Gabanta ne yafara faɗuwa,saboda dama tasan abinda zata gani,amma bata taba tsammanin har yanxu yana aikatawa ba,tayi zaton ya daina kaman yanda yayi alƙawari, Ƙafafunta nason juyawa su koma,amma kuma zuciyarta nada muradin ganin abinda yake wakana,duk da cewar tasan idan ta karisa komai zai iya faruwa da ita,to amma zuciyarta tafi rinjaye akan kwakwalwarta,dan haka cikin sanyin jiki taja kafafunnata zuwa cikin turakar tasa.
Turmi da tabarya ta sameshi da wata baiwa mai manyan Baya da kuma albarkar ƙirji shima. Mace ce har mace amma babu kyan fuska da kalar fata. Kana ganinta kasan baiwace da batasan komai ba sai bautar,dan shi kansa saida yasakata banɗaki ya dirjeta kafin ya iya zuwa inda take. Kana gani kasan albarkatun jikinta ne kawai yajashi gareta.
Runtse ido Gimbiya Asmah tayi tana jikin wasu taurari suna yawo a cikin kanta. Wani ƙululun baƙin cikine ya taso ya tokare mata maƙoshi,wai ace mijinta ne yake tarayya akan gadon sa hakam kuma baiwa. Yarasa waxai dunga hada shimfiɗa dasu sai bayi kuma itama yazo yayi tarayya da ita,tasha sakawa a kashe baiwa,ko a lahantata saboda ta hada shimfiɗa da mijinta,to amma hakan sam bashine mafitar ba,saboda shi ummul aba'isin na faruwar hakan ba dainawa zayyi,badan cewar shine zai zama sarkin gobe ba,kuma ɗan ta daga baya yayi sarauta da tuni ta kasheshi tun yanzu,to amma bazatayi hakan yanzu ba akwai sauran lokaci tukunn.
"Abin Sultanr baiwa ce fah ka kalleta ka kalle fasalinta,ita kake haɗawa kishi dani,nace maka in mata goma ne kake so ma ka auro ka zarce yanda musulunci ma ya tanadar,amma baiwa.....Bayi fah da bayi fah kake wannan ƙazamar mu'amalar. Wannan wanne irin zubewar Darajane,wai kai bakada izza da girma ne irin na ƴayan sarauta,gabaɗaya halayyar Bunsurancin ka ta hanaka kaja girmanka a tsakanin bayinka. To wlh........."
"Kinga dakata dan Allah,bayinnan fah bayina ne bana wani ba,Allah yayini da buƙata inaso na more rayuwata sai ki dunga shiga hanci na, idan banyi dasu ba buƙata ta kike biyamin kome? Babu abinda kike bawa muhimmanci sai jin cewa ke gimbiya ce kuma sarauniyar gobe,sannan kiyi ta ƙunsar ciki kina haifewa saboda ki ƙwace gida. To duk na baki waɗannan dan haka ki bar wata ta taremin wannan layin tunda ke kin kasa bazaki iya ba."
Kallonsa takeyi baki sake,ganin a gaban baiwar yake gasa mata magana san ransa.
"Haka kace ko,to shikenan ku gama ki fito kekuma ina jira ki fito ki damƙamin rayuwarki,domin wannan abun dayake miki shine jin daɗin rayuwarki na ƙarshe,kaikuma in kana so ku kuma sai kabita barzahu kuyi. Sannan wannan shine na ƙarshe idan ka kuskura na kamaka da wata baiwar sai nakai ƙararka wajen Mai martaba,bunsuru kawai"
Masifa take ta inda take shiga batanan take fitaba,wani abu taji yana tahowa tun daga ƙafafunta yazo ya shiga cikin ƙirjinsa,numfashinta ne taji ya takure cikin ƙanƙanin lokaci tafaɗi a wajen sumammiya.
Cikin hanzari ya zura rigarsa ya matso inda take kwance yana jijjiga ta cikin tashin hankali. Ƙarya yakeyi idan yace baya sonta,wannan abinda yake ma saboda bata iya biya masa buƙatarsa ne,sannan shi bayason sake wani auren kafin a naɗashi sarki,shiyasa yakeyin wannan ɗabi'ar.
Ganin hankalinsu baya kusa yasa baiwar saka kayanta ta sulale ta gudu,zataje tayi ƙokarin barin masarautar,tunda tasan idan gimbiya Asmah ta tashi to lallai saita aikata abinda tace.
Wasa wasa said gimbiya Asmah ta kwana a sume kafin ta farka. Sunkia Madeena ce akanta tanayi mata fifita,suna haɗa ido ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,cikin sheshsheƙar kuka tace.
"Ranki ya daɗe Yerima Kabeer zai kasheni kafin kwana na ya ƙare"
"Ki kwantar da hankalin ki bazaki mutu ba,kuma dama ai ba'a mutuwar sai kwanan yaƙare, Kuma nayi miki alƙawari zan ɗau mummunan mataki akan sa indai zai dunga sakaki damuwa haka da tsohon ciki. Sannan.........."
"Wayyo Allah na ki taimakeni kaina zai fashe wayyo Allah na bana gani sosai ki taimakeni Umma kaina ciwo"
Ganin matagugun da takeyi tana juya kai yasa hankalin Sunkia Madina ya tashi sosai,domin tasan ciwon kai ga mace mai ciki abune da baza'ayi wasa dashi ba sam.
Tashi tayi ganin babu kowa sai ita a ɗakin ta ƙira jakadiya,wadda akayi sa'a tana kusa batayi nisa ba.
"Ke ke Jakadiya maza jeki ƙiramin Uwar Ganye yanxunnan,kice ina nemanta da gaggawa a turaka ta"
Jikinta yana rawa ta karbi saƙon ta tafi domin isar dashi. Bata wani jimaba sai gata ta dawo da sauri uwar ganyen tana biye da ita a bayanta,Baƙar matace mai ɗan tirinyar jiki.
Tare suka shiga ɗakin,Sunkia Madina ce riƙeda ita tana tofa mata duk addu'ar data zo bakinta,yayinda itakuma take ƙaƙafewa tana cije baki,kana kallonta kasan tana a cikin halin ciwo mai tsanani.
"Uwar ganye maza xoki dubata ki kalli mai yake damunta,kafin kizo dai ƙiran kan ciwo yakeyi take,amma yanxu ta daina maganar ma sai fizge fizge kawai"
Ƙarisawa tayi fuskarta cikeda ƙwarin gwiwa na yarda da maganinta da tayi. Kan gimbiya Asmah takama na wasu daƙiƙu kafin ta bude jakarta ta ɗauko wani garin magani,ƙaramin ƙoƙo aka kawo mata ta jiƙa a ciki,kana ta mikawa Sunkia Madina akan ta bata tasha.
A taƙaice dai har dare yayi aka waye ciwo bai lafa ba,dan har idanuwata sun kumbura saboda tsananin ciwo da take ji. Zuwa lokacin gabaɗaya kowa ya fita hayyacinsa, ciki harda Yerima Kabeer wanda ya susuce yana jin shine maƙasudin faruwar komai.
A zaune take a Harabar ta tayi tagumi,fitowar ta kenan daga ɗakinta inda Gimbiya Asmah take kwance,sallama jakadiya tayi tana nemawa matar Galadima iso zuwa wajenta,ɗaga mata kai kawai tayi akan tashigo.
Doguwar matace mai ɗan haske,tasha kaya na alfarma da kuma zinare amma marar nauyi. Zama tayi suka gaisa da Sunkia madina kafin tafara faɗin abinda yakawota.
"Nikuwa Allah yabaki nasara Naji labarin rashin lafiya Gimbiya Asmah kuma ga ciki ya girma,mai zai hana bazaku kaita Jami'ar Al'azhar ba,ciki akwai wata yarinya mai matuƙar baiwa na magani,Fasihmmam ma ga mata masu ciki tayi karatu mai zurfi akansu. Nake faɗamiki waccan satin muka kai sirikata haihuwa yazo amma tanata zubar jini,har muka je wajen mai kulada majinyatan kasa shawo kan matsalar tayi saida wannan yarinyar tazo,tana duba tafaɗi matsalar kuma akayi nasarar shawo kanta. Wani irin baiwane da ita idan ta taba jikin mutum to zata gano mai yake damunsa. Naji ance kafin muje ma wai ta taba juyawa wata mata ɗa a ciki dayazo ba daidai ba,kuma tayi nasarar har matar ta haihu lafiya abinta........"
"Ke dan Allah Fulani Halima?"
"Ƙwarai kuwa dagaske nakeyi miki,domin ni ganauce ba jiyau ba. Wannan tsofin masu maganin na cikin fada babu abinda suka Sani sai ƙarya da Kurari,su saka mutun ya zauna da marar lafiya yana kallonsa har ya mutu batareda neman mafita ba"
"Gaskiya to in hakane yanzu kuwa zamu kaita,barina ƙira Yerima Kabeer ɗin ya shirya mana keken doki maza muje can ɗin in Allah yasa aka dace ai mu barkanmu"
Daga wajen ko bata lokaci basuyi ba aka shirya keken dokin,mutum biyar aka ɗauka,da ita Sunkia madina sai Yerima kabeer,ita marar lafiyan da kuma baiwarta ta hannun damanta saikuma matuƙin keken dokin.
Batareda Gudu ba kokuma tafiyar jinkiri a haka har suka isa bakin Jami'ar ta al'azhar,basu sha wahala ba kasancewar suna ɗauke da hatimin gidan sarautar. Cikin ƙanƙanin lokaci Wajen ya karaɗe da jirgi jirga na bayi dakuma nasu Ummu hajar,aka gyara waje mai kyau inda za'a tarbeta,surukar sarki guda na garin Goa.
Ummu hajar tashiga cikin ɗakin da rawar jikinta,tana sanye da kayan aikinta na duba marasa lafiya,hannunta ɗauke da madaidaicin ƙoƙo da ruwan Ɗumi a ciki da farin tsumma.
A gefen gadon da Gimbiya Asmah take kwance ta ajiye sannan ta juyo ta kalli Sunkia Madina cikin giramamawa.
Ranki ya dade Idan bazaki damu ba zanso naji dame dame yake damunta.
Bayanin abinda ta sani ta kwashe ta faɗamata,ciki harda cewar taga abinda ya razana ta ne shiyasa.
Juyawa ummu hajar tayi ta kalli gimbiya Asmah,gashi tana juyin ciwo to amma kuma data dubata bakin mahaifarta a rufe yake babu alamar haihuwa nan kusa a tattare da ita. Shuru tayi tana nazari sai taji muryar sunkia madina tana magana.
"Uhmm ancemana akwai wata yarinya wacce takeda baiwar duba marar lafiya,bakya ganin bazaki ƙirata ta duba ta ba,ko ba tanan kai?"
Jimm ummu hajar tayi kafin ta bata amsa,wato sunan Joda ba iya cikin Jami'ar nan ba har gidan sarauta ma ya zagaya kenan. Lallai yarinyar nan Allah ne kaɗai yasan mai ya ajiye a tattare da ita.
"Ahh Inaga Joda kike nufi,ai ba ma'aikaciyar jinya bace,baiwa ce kawai tana tayani da aikine,amma idan kunaga babu komai zata iya taba marar lafiyanku to bari zan ƙirata."
"Ohh saboda baiwa ce shiyasa bazata dubata ba koda ta iya aiki?"
"Ahah ba haka bane ranki ya daɗe, nima bawai bana so ta dubata bane,wasu idan nasaka ta dubasu saisuce an ci musu fuska an bar baiwa tana tabasu,to inaga wannan da take suruka ga babban sarki ina gudun kada nayi laifine"
"Ahah bakomai ki ƙirata ta gwada baiwarta muma akanmu,dama jin labarinta ne yasa muka taso muka zo har nan ɗin"
Cikin sauri ummu hajar ta nufi ƙofa domin neman joda,wanda saida taje har sansaninsu amma bata nan. Wani badakare ne yabata amsar tana sashen baƙin mutanen dasuka zo gasar ƙiraan. Bata gane wajen ba hakan yasa ya wuce gaba yana yimata rakiya har ya isa da ita masauƙin Hammar. A zaune take ta kifa kanta da ƙaramin bencin da take zaune a gabansa,gaban ɗauke da tulin litattafai wanda suke karatunsu da hammar ɗin,yanzu ma wani shafi ne dayaƙi zama mata take ta faman rubutashi a takarda Guda 50,ta kusa gamawa Bacci yayi awun gaba da ita.
Bayan ya nuna mata inda take juyawa yayi batareda yashiga ba,itace ta buɗe asabarin ɗakin tashiga,a hankali take karewa jodan kallo,sanann tana kallon litattafan gabanta wanda wasuma ita kanta batasansu ba.
"Yarinyar nan a wacce gaba zata tsayane da neman ilimi,a shekarunta har takai ta karanci waɗannan litattafan,kaddai wannan bawa mai abin mamaki nan ne suka jone yake koya mata"
Tsugunnawa tayi tareda dukan kafaɗarta a hankali. Zabura tayi ta tashi amma fuskantar bayyane da alamar bacci.
"Kai Hammar ka barni na huta mana kai kanka kasan nayi ƙokari duk wanda mukayi bai isaba sai an sake cigaba. Ni gaskiya nagaji ka dunga ragamin mana. Har yanzu fah ni ƙaramace da saurana"
Tana maganar cikin sigar Gajiya da kuma alamun bacci.......
Zaro ido ummu hajar tayi tareda cewa.
"Ni ƴasu ke Joda wai me kike cewa ne,yabar miki mene?"
Saurin zaro ido tayi ta kalli Ummu hajar a gabanta,da sauri duk wani bacci yabar kan idonta,tanemeshi ta rasa dukkuwa da yanda takeson yinsa. Matsawa tafarayi dabaya tana girgiza kai,so take tayi bayani amma kuma kaman maganar ta gagara fitowa daga bakinta.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow