Yayana2
by @zaynaberhhh
waye yayana
mallam iro dan karamar hukumar fofure dake garin adamawa shi fulani ne shi kadai ne a gun iyayen shi wanda sun rasu yana da mata da da yara biyu hauwau da kuma ibrahim sungirma tare acikin garin inda ibrahim ke shiga cikin garin yola makaranta ita kuma hauwau tun daga primary ta tsaya tana shekara 15 aka yi mata aure ta auri wani saurayinta mai suna sudais lokacin ibrahim na shekara 20 yayi kandi Allah ya taimaka ya samu shiga F.C.E yola ya samu gurbin karanta islamic studies.
Allah ya bata haihuwa da na miji lokacin ibrahim ya fara karatun shi cikin ikon allah yana aji na daya aka yi mishi takwara yaro yaci suna ibrahim Khalil
yaro ya fara girma chiwo ya kama mallam iro Lokacin baba Ibrahim na Aji na boy u Allah bayyi zai rayu ba ashe chiwon ajali ne Allah ya mishi rasuwa wata ranan asabar wanan rashi ya taba duniyar iyalanshi dan shi ne ya rage gatan su se mahaifiyarsu da suke kira inna da yake baba ibrahim baya zama se inna ta dawo gidan hauwau da zama wannan har yama dalilin da yasa ta fara samun matsala da uwar sudais bata fada wa kuwa ba har shi sudais din.
Haka ta ringa hakuri har Allah ya taimaka ibrahim ya gama makaranta yayi bautan kasa ya dawo lokacin yana shekaru Ashirin da hudu Allah yayi wa inna rasuwa bayan zaman makoki limamin garin ya raba musu gado se ya sayarda wasu daga cikin shanayen shi ya bar Sauran a hanun sudais ya kuma cikin Yola Neman aiki.
Dake kasar namu se ahankali da kyar ya samu aiki bayan watanni kusan 3 yana wahala lokacin shekaru sun fara ja ya dawo gida ya gayawa hauwau ta mishi murna tace Saura aure.
Ya samu aikin koyarwa ne a ramat anan ya hadu da mama sunanta Hajara suka fara soyyaya bayan shekara daya sukayi aure.
Lokacin Khalil na shekara 10 a duniya ya gama primary abba (Ibrahim) ya nema mishi gurbin karatu a nan ramat ya fara zuwa .
Hajara batason zuwan nashi Wai ace wanta dan kauye ne shi kuma ita batasan wani sa idon uwar shi ta turo shi Yi ba sau biyu Tana bari dan Shan magunguna marasa kan gado nan fa ita da danginta suka ringa cewa shi da uwar shi ne.
Na ukun ne ya zauna lokacin yana shekaru 13 yana shirin jnr waec duk Wannan cin fiskan nata baitaba gayawa abba ba dab zasu fara waec Allah ya sauke ta lafiya ta samu ya mace ba haka ta so ba amma ai yanzu ta fara inji ta.