3
by @zaynaberhhh
Yarinya taci suna Amina Ana kiranta binta Banda Khalil da ke kiranta aminatu yayi murnan samun kanwa dan haryanzu hauwau bata sake haihuwa ba Yan fofure sunzo suna.
Dama zaso kuma da Khalil ne dan yayi Hutu yace shi zai zauna da kanwarsa suka tafi suka barshi dake ita Maman namiji ta so sai rainon binta ya koma hanun Khalil.
Har Hutu ya kare ya kuma makaranta bata fara kiran sunan kuwa ba sai nashi sai tace jaliiiii Yakanyi dariya hakan nasa shi nishadi Ana haka ya kuma makaranta ci gaba da karatun shi.
Rayuwa naja suna Kara girma binta na Kara wayo shekaranta biyu a duniya mama ta sake haihuwa Allah ya Karbi addo anta ta samu da namiji da ga nan kuma ta fita harkan binta gaba daya ta kuma rainon Magaji inji ta da fada.
lokaci ya ja Yau binta na da shekaru 3 Khalil nada 16 Autan Su Ahmad nada shekaru 1 lokacin Khalil yake gama secondary da yake Jami’a sai ya Kai 18 yayi zaman gida na shekaru biyu shakuwa ta Kara shiga tsakaninshi da binta dake uwarta tace ita ta Magaji take ya Kara girma da hankali dama ba mai sun magana bane.
Ansa binta a makaranta intaje ta dawo ta kan zo ya Yi mata assignment yanzu ta shekara bakwai shi kuma 20 da ke yana da kukari a makaranta sai abokinshi daya da yake da shi mai suna Faisal ya bashi shawaran cika scholarship ko zai samu cikin ikon Allah ya samu gurbin karanta business administration a Canada shirin tafiya yafara Yi.
Abba na ganin haka ya tashi ya tafi fofure ya Sami baba sudais Akan ya na son kafin khalil ya tafi yason ahada shi da binta baba sudais yace ba laifi amma yayi magana da mama Tukunna shima zaiyi magana da umma (hauwau kenan ).
Ya dawo yola ya Sami mama ya gaya mata niyyan shi tace ita bata San zance ba yarta Baza ta auri talaka ba shi Khalil din mai ya Tara, ba abunda abba baice mata ba don ta fahimta amma taki sai ya fita harkan ta, Wannan dalilin yasa take hantaran Khalil a Gidan yanzu.