EELHAM🌹

EELHAM

by @rabearhwakili

{🌹EELHAM🌹}




Story and written........✍️
              By
   (Rabe'arh wakili)



Episode 1 📲 


بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai 



Yah allah yadda na fara wannan littafin cikin Koshin lafiya allah ka bani iKon kammalawa cikin Koshin lafiya
  
Ubangijin mu Allahu ka bani daman da ikon  rubuta alkhairi🤲


Ina yiwa ɗaukakin Musulmai na duniya Barka da sallah fatan munsha ruwa lfy Allah ka karɓi ibadun mu yah ubangiji Allah  kasanya mu cikin yantattun bayin ka Allah kasa munyi ibada karbabbiya Allah ka ƙara maimaita mana Amin ya arrahman rahimin 🤲 





A hankali nake tafiya Ina zagaye gari Dan in dauko maku labari,haka nayi ta lulawa ina kalle kalle, ban ankara bah naji ana ta faman fadin minna²wai Ashe har na iso tashan mota ban sani bah, Aiko banyi Wani Tinani bah na afka ciki dan naje na dauko maku story Dan kun san Ina sonku 

 a haka harmuka iso tashan garin kowa ya kama gaban shi, Nima haka nata tafiya har nazo wajen Wani kantamemen gida innalillahi wainna ilaihi raji'un, wai aljannar duniya kenan subhanallah na Baku dama ku kiyasta gidan a xuciyar ku Dan in nace zan lissafa abinda nagani daga wajen kawai zamuja lokaci, a haka nata kallan gidan Ina rakube daga gefe naga ana wangale gate din,yah Allah kyau iya kyau wata musulmar mota ce wacce ta ansa sunan ta mota kirar range Rover, ban tsaya karewa motar Kallo bah nayi wuff na afka cikin gidan gudun Kar Mai gadi ya kulle gidan kuma.
Da shigata  naga Ashe wajen ba komi bane bisa ga cikin, haraban gidan babba ne Masha Allah gefen chan parking space ne wanda akalla zai iya daukan motoci gudu 20 ko ma fiye da haka  kuma bazasu takura juna bah ,family house ne Wanda ya Tara mutane da yawa a cikin shi ko wanne da part dinsu ga part din da nagani daga ta chan gefe nasan na samarin gidan ne, da mamaki na banga kowa a waje bah duk fadin gidan kuwa, Amman duba da cewa hudu tayi kilan suna islamiya, haka har nashiga Wani part din Shima ya hadu sosai da sosai dan falon babban gaske ne mai dauke da set din kujeru biyu, still akwai sauran space sosai dan ko da za'a kara wasu set na kujerun zai dauke tsaf kuma har waje ya rage, ƙasan kuwa center capet ne wanda ya amsa sunan capet dan laushi idan kana tafiya kaman a kan katifa kake sabida laushi, tsakiyan kuma center table ne da flower mai kyau cikin wani glass cup mai girma, bakowa a falon haka ne yabani daman karewa falon kallo,gefe chan daga falon dining room ne dake dauke da d/table da kujerun su masu kyau kyau ga capet mai laushi malale a kasa gefen shi kitchen ne babba mai aiki na hango sai hidima take a cikin shi,ta gefen da kamshi yafi buso min na maida hankali,Masha Allah wata mata ce fara sol da ita gata da matsakaici jiki tana da tsayi Amman ba wai chan bah,aiki take cikin nutsuwa da kwarewa, juyowa tayi tana magana da mai aikin ta ai bansan sanda na sake baki da hanci ina kallon matan bah kyakkyawa ce Masha Allah duk da ta manyanta amman hakan bai boye komi daga kyawun ta bah haka dai ta juya ta cigaba dayin aikin tah Nima dai haka na fito na shishiga sauran sashen wanda komi iri ɗaya ne hadda fadi da komi saide ace kowa da irin nasa kwalliyr daki, part din dake a ƙarshe na shiga shima dai kaman sauran haka yake Saide nan dinma da nasa kalan. Wasu yara yan shekaru biyu a duniya na hango a falo da gani kasan twince ne dan kamannin su har ya ɓaci gasu suma ba tayan baya bah wajen kyau gasu Masha Allah,wasa suke Abunsu irin nasu na yara haka dai na fito bawai dan na gaji da kallon yaran ba! dan irin yaran nan ne masu shiga rai farat ɗaya 
         
Karfe shida 6 matasan gidan suka fara dawowa daga aiki ko wanne da tasa Motar wasu suyi cikin gida wasu kuwa part ɗin su na samari suke tafiya sai wasu da suke shiga wani sashen chan daban suma haka dai nake ta jinjina kai ina mamaki,maida duba na nayi bakin gate jin horn na moto gate man ya bude nan motar tasamu daman shigowa a parking space bus din yayi parking, haka ko su ka rinƙa fitowa daya Bayan daya haka dai duk suka kammala fitowa wasu suyi sashen uwayen su sai wasu yan mata ne wanda a shekaru zasuyi sha uku suka nufi sashe inna inda yayyin su suke cewa wai basuda zuciya kullum suna nan inda za'a walakantasu,oho ina ruwan su dankan ko a  jikin su, suma dai haka ko waccen su tayi hanyan part ɗinsu..........................✍️