BA SO BANE?

Chapter 11

by @hafsatwaziri1122

***


BA SO BANE.

Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page 11


I Dedicate this book to
 Nanakhadii 💅📕_



A fusace ta miƙe tsaye. Wayar hannunta ta jefa kan tebur da ƙarfi, sannan ta yi taku biyu zuwa gabansa, tana hura hanci.

Sosai ganinsa ya sa ta ji haushi, duk yadda ta so ta ci masa mutunci idan ya zo, a yanzu sai ta ji duk ta rasa wannan gwarin gwiwar. Saboda wani irin kwarjini da shakkarsa da suka daki ƙirjinta.

Cikin ƙarfin hali ta watsa masa harara da faɗin,

“Wanene ne kai? Me kake taƙama da shi a ƙasar nan da har zan saka maka lokacin da za ka zo ka tsallake? Tsabar kai cikakken marar mutunci ne. Ba cewa na yi tun ƙarfe huɗu za ka zo ba? Ka sani, idan har ka sake tsallake magana na, hukuncin ba'a kanka kadai ba, har ma'aikatan da ke cikin Companyn nan sai na hada na Kore ku..."


A hankali ya rumtse idanunsa, sai kuma ya buɗe su a kanta. Nan take ta yi shiru saboda yadda ta ji zuciyarta ta buga da sauri, sakamakon wani irin kwarjini mai cika idanu da ya yi mata. Amma saboda tsabar ƙarfin hali da taurin zuciyarta, sai ta ci gaba da masifar, wacce take fita cikin muryar shagwaɓa data saba.


“Idan har ka kuskura ka ƙara saɓa ko da minti ɗaya ne, to ka tabbata a bakin aikin gaba ɗaya ma'aikatan.”

Cikin deep voice ɗinsa mai fita da nutsuwar murya ya furta,

“Sorry, Boss.”

A hankali saboda yadda sam baya son hayaniya ga kuma kansa ke sarawa.

Da sauri ta ɗago kai tana kallonsa cike da mamaki. Idan kunnuwanta ba su yi mata ƙarya ba, kamar haƙuri ta ji ya ba ta.

Sai dai ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ya sa ta yarda kunnuwanta ne suka yi mata ƙarya.

Oga Fahad, da ke jinsu bai ce komai ba. Ya ɗago kai yana kallonsa cike da mamaki. Shi ma dai zargin kunnensa da samun matsala ya fara yi. Tuna girman kan Aziz ɗin ya sa ya haɗe fuska. Haka kawai yake jin tsanar Aziz din har cikin ransa. Shi ya sa tun farko ya ƙi saukasa aikin. Yanzu ma Saboda mommy ta yi abinda ke ranta a kansa ne yasa ya bar shi.

Ya juya zai fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Taku biyu ya yi...

Ta tsaida shi ta hanyar faɗin,

“Ba ka iya gaisuwa ba?”

Karon farko al'amarinta ya so fara ba shi dariya, amma bai nuna ko a fuskarsa ba. A ransa ya maimaita kalmar,

“Ba ka iya gaisuwa ba?”



Taku biyu ya yi ya dawo baya, ya tsaya gabanta.

Ba zato ba tsammani, ya ciro hannunsa daga aljihun wandonsa, ya miƙa mata alamar su yi musabaha.



Cike da jin haushi, ta jefa masa key ɗin motar a hannu. Tana jan tsaki tare da harararsa.

 reƙe key ɗin ya yi, sannan ya juya zai fita a zafafe.

Ta ce,

"Yaran fa?"

Juyawa ya yi ya kalli yaran da ke wasansu. Macen ita ce babba, za ta kai shekara shida, sai ɗayan kuma zai kai uku. Kafin ya ce wani abu, yaran suka nufe shi a guje, kamar dama sun san shi tun da daɗe.

Ajmal yana isowa ya riƙe ƙafarsa.

"Uncle, supermarket za mu je ka siya min katon teddy irin na Afaf, ko? Daddy ya siya mata, bai siya min ba."

Ya ƙarasa maganar yana kifkifta ido, kamar zai yi kuka.

Yaran sun burge shi matuƙa. Murmushi ya yi musu, irin murmushin da idan ba ka san shi sosai ba, ba za ka taɓa gane ya yi ba. Ya tsugunna ya ɗauki yaron, domin duk wannan haɗe-haɗen fuskar da yake yi, yana matuƙar son yara. Sannan ya riƙe hannun yarinyar.

Shagala ta yi wajen kallonsu. Ita kanta ba ta san me ya sa take kallonsa ba. Ta kasa dauke kanta har sai da ya juyo suka hada ido. tsaki taja mai ƙara tare da murguda masa, sannan ta buɗe ƙofa ta fita.

Duk inda suka haɗu da ma'aikata, sai sun gaishe su. Idan sun gaishe ta a tsoro ce, sai kuma su juya su gaishe shi cike da girmamawa, kamar shi ne ogan kamfanin. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ta wuce fuuu kamar zata fire.

suna fitowa harabar kamfanin, gaba ɗaya bodyguards ɗinta suka miƙe suna tinkarar ta.

Ganin Abdul-Aziz kusa da ita ya sa suka zagaye shi, kamar wanda ya yi sata. Shi kuwa Aziz yana tsaye cak, babu ko alamar tsoron su tattare da shi.

A yatsine ta kalle su, domin ita kaɗai ta san irin haushin su da take ji. Sam ba ta yi tunanin Daddy zai yi mata haka ba.

"Leave him."

Ta faɗa cikin sigar bada umurni.

Nan take suka ja baya, ba tare da sun yi nisa ba.

Ɗaya daga cikinsu ya ce,

"We are sorry, Madam, but we can't let you go anywhere."

Shekeke ta kallesa, irin kallon nan na idan ka isa ka hana ni.

Ta ɓalla masa harara tare da nufar motar ta.

Ganin haka ya sa hankalin Japhat ya yi matuƙar tashi. Cikin tashin hankali ya zaro wayarsa daga aljihu.