Chapter 16
Jikinta na rawa ta ƙaraso gabansa. Duk da yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, hakan bai hanata satar kallonsa ba.
Cikin ɗan rawar harshe ta gaishesa.
Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata. Tun da ya yi mata kallo ɗaya, ya ɗauke kansa.
Cikin in'ina ta ce,
"Na... Na'am, Yaya..."
Ba tare da ya tanka ba, ya miƙa mata Ajmal da ke sharar barci a hannunsa, sannan ya nuna mata jakar Mammy da ke kan kujerar.
Murya a ƙasan maƙoshi, kamar yadda ya saba, ya ce,
"Ɗauki wannan."
Bai tsaya jiranta ba. Ya yi gaba da Afaf a hannunsa.
Da sauri ita ma ta bi bayansa. Duk da cewar tafiyarsa da nata ba daya ba, amma saboda tana son su jera da shi, hakan ya sa ta shiga haɗawa da gudu, duk da Ajmal da ke hannunta. Sai dai ina, hakan ya gagareta, saboda da sauri sosai yake tafiya.
Duk yadda ta so ta hana wannan ɗan tazarar da ke tsakaninsu, hakan bai yiwu ba.
Hakan ya sa ta haƙura tana binsa a baya, yayin da idanunta ke kansa ƙyam. Wani irin kallo take masa mai wahalar fassarawa.
Tun lokacin da ta fara ganinsa a unguwarsu, zuciyarta ta zaɓe shi. Sai dai ba ta taɓa samun ƙarfin halin bayyana masa abin da take ji ba. Ba don komai ba, kuma ba don ba ta fatan hakan ba.
Sai don shi ɗin ne bai taɓa ba ta damar da za ta sa ta yi hakan ba. Saboda ko da sun haɗu a unguwa, baya ma ko daga ido ya kalli inda take. Duk maitanta kuwa, haka take haƙura. Don ko ta gaishesa ma, wani lokaci amsawa kawai yake yi cikin taƙaitacciyar murya, wani lokacin kuma sai ya wuce kamar bai ji ba.
Hakan kuma bai sa ta karaya da sonsa ba. Ta dai danne ne tana jiran lokaci.
Amma yau...
Yau shi ne da kansa ya kira ta.
Wannan ya sa take jin kamar za ta mutu saboda daɗi. Duk da ta san kiran na wani dalili ne, hakan bai sa ta ji komai ba, sai ma wani daɗi da gwarin gwiwar da ta samu. Don kiranta da ya yi kaɗai ya wadatar, ya kuma saka ta cikin farin ciki sosai. Saboda zaɓarta da ya yi, a ganinta, hakan ma wani alfarma ne.
Oho, shi dai bai san abin da take tattaunawa a zuciyarta ba. Tafiyarsa kawai yake yi cike da nutsuwa da ƙwarjini.
Har suka iso, ba ta ankara ba sai da ta ga ya tsaya, sannan ita ma ta tsaya.
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya buɗe, kai tsaye ya kutsa kai ciki ba tare da ya yi knocking an ba shi izinin shigan ba.
Tsit ofishin yake. Ba ka jin ƙarar komai a cikinsa, sai ƙamshin turarurruka kala-kala da ke tashi tare da sanyin na'urar AC da suka tarbe su.
Mammy ce kaɗai zaune a saman kujerar CEO. Wayarta manne a kunne. Daga ganin yadda take magana cikin shagwaɓa tana tura baki, zai tabbatar maka da Daddy take waya. Fuskarta ɗauke da murmushin da ba ta yi wa kowa irinsa sai Daddy.
Jin motsin buɗewar ƙofar ya sa ta ɗaga idanunta a hankali, ba tare da ta cire wayar daga kunnenta ba.
A kansa idanunta suka fara sauka.
Kafin su sauka kan Suhairat da ke bayansa, ta yi kamar za ta ɗauke idanunta daga kansu, sai kuma ta fasa. Ta ci gaba da kallon Suhairat, wacce gaba ɗaya hankalinta ke kansa.
A hankali ta isa wajen da yake tsaye, ta durƙusa ta kwantar da Ajmal a kusa da wajen da ya kwantar da Afaf a kan sofa cikin kulawa, sannan ta gyara masa rigarsa da ta ɗan naɗe.
Cikin nitsuwa ta miƙe tsaye tana satar kallonsa da fatan shi ma ya ganta ko da sau ɗaya ne. Sai dai, a maimakon shi da ta yi fatan ya kalleta, hakan bai yiwu ba.
Sai ma idanunta suka shiga cikin na Mammy, wacce har yanzu ba ta daina kallonta ba.
Wani irin kallo ne...
Kallon da ya sa Suhairat ta ji kamar ƙafafunta sun kasa ɗaukar jikinta. Zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi, dalilin tsoron Mammy da ya darsu a zuciyar gaba ɗaya ma'aikatan da ke cikin company tun daga jiya zuwa yau.
Cikin sanyin jiki ta sauke kanta ƙasa, ta juya sum-sum kamar mara gaskiya ta nufi ƙofar fita.
Sai dai kafin ta fita, ta kasa hana kanta juyowa ta saci kallonsa.
Ta juya a hankali, amma cikin rashin sa'a, idanunta suka sake shiga cikin na Mammy, wacce dama ita ba ta ɗauke idanunta daga kanta ba. Kunnenta makale da waya har yanzu.
Da sauri Suhairat ta fice kamar wacce aka hankaɗa.
Shi kuwa bai ma san abin da ke faruwa ba. Yana gama gyara wa yaran kwanciya, ya juya zai fita ba tare da ya kalli wajen da take zaune ba.
Cikin tsananin jin takaici da jin zafin yadda ya ba wa
banza ajiyarta yasa a zafafe ta ce,
"Wait."
Yi ya ya yi
kamar bai ji ta ba ya ci gaba da tafiyarsa.
A fusace ta miƙe tsaye, tare da kashe wayar da ke kunnenta. Kana ta buga teburin gabanta da ƙarfi cikin isa da gadarar da ta saba yi masa magana da ita. Ta ɗaga murya ta ce,
"You womanizer."
Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta ganin yanayinta yasa a hankali. Ya rumtse idanunsa, sai kuma ya buɗe su a kanta.
Harararsa ta yi tana ƙoƙarin tinkararsa ta sauke masa kondon masifar da ke cin ta tun ɗazu.
Wayarta da ke ajiye ta shiga ringing. Ganin Daddy ne mai kiran, ya sa ta fasa abin da ta yi niyya, ta kuma zauna.
Ta ɗaga wayar tare da kaiwa kunne. Murmushi ne ya fara bayyana a fuskarta, a ta koma kan kujerar ta zauna. Cikin shagwaɓe, kamar tana gabansa, ta ce,
"Sorry Daddy."
Daga nan ta ci gaba da maganar da ba ta gama ba a ɗazu ta ƙashe.
Shi dai yana tsaye a wurin da yake, hannayensa cikin aljihun wandonsa. Fuskarsa babu alamar damuwa ko gajiya, sai idanunsa da kallo ɗaya za ka musu ka fahimci bai samu isasshen barci a daren jiya ba.
Yana tsaye a wajen kusan mintuna biyar, ba ta kula shi ba. Cike da gajiya, ya zaro hannunsa da ke cikin aljihun wanda ke ɗaure da ɗan madaidaicin agogon da kana gani, ka san ba a saye shi da kuɗi masu yawa ba.
Ganin ƙarfe 1:22 ya sa ya sauke ajiyar zuciya. Takaici ya sa ya ja guntun tsaki tare da satar kallonta kaɗan.
Ganin yadda take ta zuba shagwaɓa tana turo baki ya sa ya kauda kansa daga kallon da yake mata. Ya rumtse idanunsa ya buɗe su a lokaci guda. Duk da yana da inda zai je mai muhimmanci haka ya haƙura ya tsaya, gashi ta yi kamar ba ta san yana wajen ba.
A hankali ya haɗiye yawu, jin maƙogwaronsa a bushe. Ya shiga bin ofishin da kallo. A can gefe, kusa da wajen da take zaune, ya hango wata ƙatuwar firiji.
A hankali, cikin nitsuwa ya juya kai tsaye ya nufi wajen da firijin ke tsaye.
Kaɗan ya rage tsawonsa yana kallon cikin firijin. Gorar ruwan Faro mai tsananin sanyi ya ɗauko tare da ɓalle murfinta.
Kai tsaye ya ɗaga gorar zuwa bakinsa. Yadda yake shan ruwan kai a sama ya ba Adam's Apple ɗinsa damar motsawa cikin kaikawo, yana haɗiyar ruwan da sauri-sauri.
Ya sa Mammy daka tawa tana kallonsa, dama tun ɗazu hankalinta na kansa.
Sai da ya shanye ruwan tas ya sauke bottle ɗin, yana furzar da nannauyar numfashi kamar wanda ya daɗe bai sha ruwa ba.
Da mamaki a fuskarta, ta kawar da wayar gefe. Muryarta cike da masifa ta ce,
"Kai... har ka isa ka taɓa min firiji da wadannan hannayen naka?"
Banza ya yi mata kamar ba da shi take magana ba.
Da empty bottle a hannunsa ya ɗaga yana kallonta. Ganin kallon da take masa tasa ya ɗan ja
Tsaki ya a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska. Dan har ga Allah ya gani kwanciya yake da bukata a yanzu amma ya zai yi boss nashi ta haka.
Cikin kasalar da yake ji tun da safe ya juya a hankali ya ƙarasa ya zauna a kujerar baƙi da ke fuskantar kujerar da take zaune a kai. Ya haɗe hannayensa a ƙirji.
Da kallo ta bisa har ya je ya zauna
cikin yatsina fuska ta hararesa tare da faɗin,
"Au, ashe ƴan ƙauye ma sun iya buɗe firiji, har su sha ruwan gora?"
Kasancewar maganarta ta zo masa a bazata ya sa wani murmushin da bai yi niyyar yi ba ya kuɓuce masa ba tare da ya shirya ba.
Ita kuwa shagala ta yi da kallonsa, yayin da zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ganin abin da ba ta taɓa gani a kan fuskarsa ba.
Kamar an yi ruwa an ɗauke, haka ya gimtse fuskarsa tare da taɓe baki kamar mai shirin yin zunde. Sai dai har sannan fuskarsa cike take da annuri saboda maganar tata.
Ganin ya gimtse fuskarsa ya sa ta ja tsaki mai tsayi.
A fili ta ce,
"Mutum ba kyau ba, ba kuɗi ba, talaka. Ya shi sai shegen girman kai da nuna isa."
Sarai ya ji ta, amma sai ya yi kunnen uwar shegu da ita.
A hankali idanunsa suka fara yawo a cikin katafaren ofishin, suna kallon kayan alatu da aka tsara cikin tsari irin na masu kuɗi.
Kana shigowa cikin ofishin za ka fahimci company sarrafa kifi ne, saboda katon zanen kifin gwangwani da ke maƙale a ɗaya bangaren da ya ci kusan rabin bangon.
Haka ya ci gaba da bin ofishin da kallo, a kai-kaice, da dogayen labulan da suka rufe tagogin gilashi. Komai na ofishin abin burgewa ne, ya yi kyau sosai.
Yayin da zuciyarsa ke mamakin ta yaya aka yi ta mallaki wannan ƙaton company haka. Sanin babu wanda zai ba shi amsa ya sa ya kawar da tambayar a zuciyarsa, ya ci gaba da yawo da idanunsa har suka tsaya cak.
A jikin bangon da ke bayan kujerar da take zaune, wani babban frame ne mai matuƙar ɗaukar hankali maƙale.
Hoton Daddy ne tare da Ammi...
Hoton da daga gani ka san an ɗauke shi ne tun zamanin ƙuruciya. Sai dai duk da haka bai hana hoton yin kyau ba.
Daddy na tsaye cikin wani farin yadi mai kyau. Babu ko da digon walwala, bare murmushi, a kan fuskarsa.
Yayin da Ammi ke tsaye a gefensa, ita ma ta sha kwalliya sosai. Hannunta ɗaya ɗora a kafaɗarsa, yayin da fuskarta ke ɗauke da murmushin da yaso ya yi kama da dariya.
A cikin hoton, kallo ɗaya za ka mata ka fahimci tana cikin tsananin farin ciki.
Sosai Abdul ya ƙurawa hoton ido. Ba idanunsa kaɗai ke kallon hoton ba, gaba ɗaya hankalinsa, tunaninsa, imaninsa da zuciyarsa ya tattara su a kan hoton.
Cikin daƙiƙun da basu fi biyar ba ƙwayoyin idanunsa suka fara sauya kala, jijiyoyi suka bayyana a cikinsu. Adam's Apple nasa ya shiga motsawa da sauri kamar wanda ke hadiyar wani abu me zafin gaske.
Cike da wani irin yanayi wanda duk sa ido kan baka isa gano wani iri ba ne. Ya lumshe idanunsa tare da buɗe su a kan hoton.
Da farko ba ta kula da abin da yake kallo ba, duk da yadda ta dinga satar kallonsa.
Tun ɗazu ta gama waya da Daddy. Ta juyo za ta masa rashin mutuncin shan ruwan da ya yi ba tare da neman izninta ba, da kuma zama a kan kujera ba tare da ta basa izinin ya zauna din ba.
Sai dai ta kasa furta komai. Ta yi shiru tana kallonsa.
Ganin hankalinsa ya yi nisa sosai a kan abin da yake kallo ya sa ta bi wajen da ido.
A kan hoton su Daddy idanunta suka tsaya.
Ta sake dawo da idanunta kansa. Ganin irin kallon da yake wa hoton ya sa mamaki sosai ya sake bayyana a fuskarta.
Saboda wani abu mai tsanani da wuyar fassara da take hangowa a cikin idanunsa da ke kan hoton.
Magana ta shiga yi masa, amma ko motsi bai yi ba, saboda hankalinsa da gaba ɗaya baya cikin jikinsa.
Wannan dalilin ya sake bayyana mamaki da rudani sosai a kan fuskarta.
Ta ɗan matsa gaba kaɗan a kan kujerarta, yayin da idanunta da zuciyarta ke ƙoƙarin lallai sai sun hango wani irin yanayi ne wannan.
Sai dai ko kusa ta kasa hakan.