DU’A (The Unwanted Daughter )

1: where it all began

by @hauwajaywrites

FLASHBACK


Before we continue with Du’a’s story, let’s take a little trip into the past…


This is where it all began.


Alhaji Muhammad Usman shi ne mahaifin Du’a.


Bafulatani ne ɗan asalin Tafawa Balewa Local Government, Bauchi State. Su biyu ne kawai a wajen iyayensu; shi da ƙanwarsa, Hibbah, wadda take zaune tare da mijinta a London.


Tun yana ƙarami, Muhammad Usman ya kasance mutum mai son ilimi. Bayan ya kammala karatunsa na farko a Najeriya, ya wuce ƙasar Australia, inda ya yi karatu a TAFEs University, specializing in Marketing.


A lokacin graduation ceremony ɗinsa ne ƙaddara ta haɗa shi da budurwar da daga baya ta zama matar aurensa…


Zahra.


Zahra ta je bikin ne domin taya uncle ɗinta murnar kammala Master’s Degree.


A farkon haɗuwarsu, kallon juna kawai suka yi.


Sai dai daga wannan kallon ne soyayya ta fara shiga tsakaninsu.


What started as a simple conversation soon turned into something beautiful.


Within a short period of time, their friendship blossomed into love.


Hajiya Zahra ita kaɗai ce ’ya ga iyayenta.


’Yar asalin Rimi, Kaduna State ce, kuma ta taso cikin gata, kulawa da tarbiyyar masu hali.


Iyayenta na daga cikin fitattun attajiran jihar Kaduna.


Ta yi karatunta a Stanford University, USA, inda ta karanci English Literature.


Kasancewar ta daɗe a ƙasashen waje ya sa wasu daga cikin halayenta suka sha bamban da na yawancin ’yan matan da suka taso a Najeriya.


Ba ta cikin matan da za’a kira da masu matsananciyar kyakkyawa ba, amma tana da wani irin kyau da nutsuwa da kima da ke sa duk wanda ya gan ta ya sake kallonta.


Bayan aurensu, Alhaji Muhammad Usman ya tattara iyalinsa suka koma Abuja, inda kasuwancinsa yake.


Allah Ya sanya albarka a sana’arsa.


Business ɗinsa ya fara bunƙasa fiye da yadda yake zato.


Bayan shekara biyu da aurensu, Allah Ya azurta su da ɗansu na fari.


Suka raɗa masa suna…


Aryan.


Shigowar Aryan cikin rayuwarsu ya kawo farin ciki mara misaltuwa.


Ba iyayensa kaɗai ba, har ma da Anti Hibbah ta taho daga London domin halartar suna.


Aryan ya taso cikin tsananin so, kulawa da gata.


Lokacin da Aryan ya cika shekara biyu, kasuwancin Alhaji Muhammad Usman da babban abokinsa, Alhaji Abubakar Tukur, ya samu gagarumar nasara.


Su na gudanar da international trade, kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka zama daga cikin manyan ’yan kasuwa masu kuɗi.


Wata rana, Alhaji Abubakar ya ba abokinsa shawara.


“Muhammad, me zai hana mu riƙa ziyartar gidan marayu lokaci zuwa lokaci? Mu taimaka musu saboda Allah.”


Shawarar ta yi wa Alhaji Muhammad Usman daɗi.


Ba tare da ɓata lokaci ba suka fara zuwa.


Sai dai…


Ba su san cewa wannan ziyara ta farko za ta sauya rayuwar mutane da dama ba.


A ranar da suka fara zuwa gidan marayun, idanun Alhaji Muhammad Usman suka sauka kan wata yarinya.


Aneesa.


Ba za ta wuce shekara goma sha takwas ba.


Ba kyawunta ne kawai ya ja hankalinsa ba…


A’a.


Abin da ya fi ɗaukar hankalinsa shi ne nutsuwarta, ladabinta da kuma yadda kowa a gidan marayun ke yabonta.


“She’s intelligent, respectful and very responsible.”


Hakan ne caregivers ɗin gidan suka ci gaba da faɗa a kanta.


Tun daga wannan ranar…


Zuciyarsa ta kasa mantawa da ita.


Da ya koma gida, ya tabbatar da abu ɗaya.


If he wasn’t going to marry Aneesa, then he wouldn’t marry anyone else.


Ba tare da ɓata lokaci ba, ya je ya nemi aurenta.


Da farko Aneesa ta ƙi amincewa.


A ganinta, ba ta shirya aure ba.


Sai dai caregivers ɗin gidan suka ci gaba da ba ta shawara.


Sun nuna mata cewa wannan wata babbar dama ce da za ta ba ta sabuwar rayuwa da ’yanci.


Bayan dogon tunani…


A ƙarshe, Aneesa ta amince.


To be continued…


kar a manta ayi following acc dina, a danna min gifts sannan a danna like, kuma kar a manta da sharhi


Questions for my lovely readers…

    •    Ya Zahra za ta ji idan ta san mijinta yana son ƙara aure?

    •    Shin Du’a da Amrah mahaifiyarsu ɗaya suke da Aryan?

    •    Kuma… waye ainihin mahaifiyar Du’a?


Drop your predictions in the comments. 


🎁 Kyautar 2GB ga duk wadda ta yi hasashe mafi kusa da gaskiya