BABI NA ƊAYA
Iskar asuba mai sanyi ta ratsa ta cikin ƙaramar tagar ɗakin, tana ɗan motsa labulen ɗakin cikin nutsuwa, kamar tana ƙoƙarin shigowa da wani sabon yanayi na kwanciyar hankali. Wani irin sanyin safiya ya mamaye ɗakin, yayin da daga nesa ake jin ƙarar zakaru suna sanar da bullowar wata sabuwar rana. Amma gareni kuwa, babu wani sabon abu a cikin wannan ranar. A wajena kowace safiya tana zuwa ne da irin nauyin da wacce ta gabaceta ta zo da shi. Sabuwar rana ce kawai da ta sake zo min ɗauke da tsohuwar wahala.
Kamar yadda aka saba, sai na ji an shure ni da ƙafa da ƙarfi.
"Ki tashi."
Muryar Alhaji Bashir ce. Ba da tsawa ba, amma muryarsa tana ɗauke da irin umarnin da ba ya buƙatar maimaitawa. Umarnin da na saba ji tsawon shekaru, umarnin da na san babu damar ƙin aiwatar da shi. Ko da jikina yana neman hutu, ko da idanuna suna neman ƙarin bacci, dole ne na tashi. A wannan gida, ba ni da damar cewa na gaji ko kuma ina buƙatar hutu.
Na buɗe idanuna a hankali. Kafin ma na miƙa hannu zuwa agogon da yake ta ƙara, zuciyata ta riga ta san lokaci ya yi. Wannan ba shi ne karo na farko ba, kuma na san ba zai zama na ƙarshe ba.
Na kashe ƙarar agogon.
Karfe huɗu da minti biyu na safe.
Na ɗan zauna a bakin gado ina jin yadda gajiyar jiya ta yi wa jikina katutu. Kamar wani nauyi ne aka ɗora mini tun daga kafaɗa ta har ƙafafuna. Idanuna suna ƙuna saboda baccin da bai wuce na sa'o'i biyu ba. Duk da haka, babu wanda zai tambaye ni ko na samu isasshen bacci. Tun shekaru uku da suka wuce, kowace safiya tana zuwa mini da irin wannan nauyin. Kullum kafin ma na gama jin daɗin ɗan gajeren baccin da na samu, sai na ji ƙafar mutum ta shure ni da ƙarfi, tamkar ba mutum ba ce ni, tamkar wata na'ura ce da ake kunnawa idan lokacin aikinta ya yi.
Na juya na kalli Alhaji Bashir.
Ya riga ya juya baya ya ci gaba da baccinsa, kamar ba shi ne ya tashe ni ba. Kamar ba shi ne ya san cewa tun daga lokacin da na rufe idanuna har zuwa wannan lokacin ban samu isasshen bacci ba. Numfashinsa yana fita a hankali cikin kwanciyar hankali, alhali ni kuma hatta zama ma ya fara yi mini nauyi saboda gajiyar da ta mamaye jikina.
Na kasa miƙewa daga bakin gadon. Ina zaune ina sauraren ƙarar fankar da ke juyawa a hankali, da kuma shiru mai nauyi wanda ya mamaye ɗakin. Wannan shirun ya fi kowace magana ciwo, domin yana tuna mini irin rayuwar da nake ciki. Rayuwar da babu mai tambayar halin da nake ciki, babu mai lura da abin da zuciyata take ɗauke da shi.
Na sauke numfashi.
A hankali na furta,
"Ya Allah... Ka ba ni ƙarfi."
Wannan addu'ar ita ce addu'ar da ta zama tamkar abokiyar rayuwata. Kusan babu ranar da take wucewa ba tare da na furta ta ba. Ta zama kalmar farko da bakina ke furtawa idan na buɗe idanuwana da safe, kuma sau da yawa ita ce kalma ta ƙarshe kafin na rufe idanuwana da dare.
Ba na addu'ar neman dukiya, bare ta neman ɗaukaka, ba kuma na neman rayuwar alfarma.
Abin da nake nema kawai shi ne ƙarfin da zai kai ni ga ƙarshen wannan rana. Ƙarfin da zan samu damar cika amanar da ke gabana. Ƙarfin da zan iya ci gaba da tafiya ko da zuciyata ta gaji, ko da jikina ya gaji, ko da rayuwa ta yi mini nauyi fiye da yadda zan iya ɗauka.
Na ɗauki mayafina na nufi banɗaki domin na ɗauro alwala. Bayan na idar da sallar nafila, na
ɗaga hannayena sama. Hawayen da ba wanda yake gani suka cika idanuna.
"Ya Allah... Ka san abin da nake ɓoyewa a zuciyata., Ka sauƙaƙa mini."
Ba na son kowa ya ganni ina kuka, domin a wannan gida, babu wanda yake tambayar dalilin
kukana.
Na share hawayen kafin na miƙe, na ninke sallaya da hijabin.
Kai tsaye kicin na nufa, na ɗan yi jim ina tunani. Nan take tunanin na ya bani cewa lokaci
yana tafiya. Cikin ƙanƙanin lokaci na ɗora tukunya kan abin girki na soma gudanar da abin
da yake gabana.
Jim kaɗan ƙamshin shayi ya fara gauraya da ƙamshin albasar da nake yankawa, domin
dafa abinda yara zasu tafi dashi makaranta
A yau ma, kamar kowace rana, akwai ayyuka masu yawa a gabana.
Yara biyar za su tashi su ci abinci su shirya domin tafiya makaranta, ina bukatar yi musu karin kumallo. Zan haɗa wa Alhaji Bashir abin da zai tafi da shi gurin aiki.
Duk wannan kafin ƙarfe bakwai na safe nake bukatar na gama su.
Na kalli hannayena.
Sun yi kauri har sun fara kaushi saboda yawan aiki, ba zan ya tuna lokacin ƙarshe da na
zauna na huta ba.
Bazan tuna lokacin da wani ya ce min,
"Amina, kin gaji. Zauna ki huta, ko aikin nan yana miki yawa yarannan su rinka taimaka miki
ba."
Na yi murmushi, amma ba murmushin farin ciki ba ne. Murmushin mutum ne da ya daɗe
yana ɓoye damuwar da ta zama kamar wani ɓangare na rayuwarsa.
Yayin da nake motsa shayin, wata murya daga cikin zuciyata ta sake tambayata.
"Shin wannan ita ce rayuwar da kika yi mafarki da ita ranar da aka ɗaura miki aure?"
Hannuna ya tsaya cak. Cokalin da nake juyawa a cikin tukunyar ya tsaya ba tare da na sani ba. Idanuna suka yi nisa cikin tunani, zuciyata kuwa ta fara tafiya zuwa shekaru uku da suka wuce. Wani lokacin da har yanzu idan na tuna shi, zuciyata kan yi wani irin bugawa. Lokacin da ban san komai game da rayuwar aure ba. Lokacin da zuciyata take cike da mafarkai, ba tare da ta san cewa rayuwa tana iya sauya komai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba.
Tunani na ya fara komawa shekarun baya...
Ranar da aka saka ni a lalle.
Har yanzu ina iya tuna yadda hannuwana da ƙafafuwana suka yi jajawur saboda kyawun lallen. 'Yan uwana da ƙawayena sun kewaye ni suna ta dariya da zolaya, suna gaya mini cewa kwanaki kaɗan suka rage in bar gidanmu. Kowacce kalma da suke faɗa tana ƙara sanya zuciyata cika da farin ciki. A lokacin bana jin tsoro, bana jin damuwa. Sai dai fatan alheri da burin ganin rayuwata ta zama kamar irin wadda nake ji ana ba da labari.
Ranar da aka yi min kitso, da kwalliya irin ta amarya.
Na tuna yadda aka zaunar da ni a gaban madubi. Aka yi mini kwalliya cikin natsuwa har na kasa gane kaina. Kowa da ya shigo ɗakin sai ya tsaya yana kallona, yana yaba kyawuna. Ana ta yi mini addu'a, ana ta faɗin kalaman da suke ƙara cika zuciyata da fata. A wannan ranar na yi ta murmushi ba tare da na gaji ba. Murmushin da yake fitowa daga zuciya, ba irin wanda nake yi yanzu domin ɓoye damuwa ba.
Ranar da mahaifiyata ta rungume ni tana kuka saboda farin ciki.
Har yanzu ina jin ɗumin rungumar da ta yi mini. Hawayenta suna zuba a kafaɗata, amma ba hawayen baƙin ciki ba ne. Hawayen uwa ne da take ganin diyarta za ta shiga sabon babin rayuwa. Ta riƙe hannuna tana ta yi mini nasiha. Ta ce in riƙe mutuncina, in yi haƙuri, in girmama mijina, in kula da gidana. Na ɗaga kai ina amsa mata da murmushi, saboda a lokacin ina ganin duk abin da ta faɗa abu ne mai sauƙin yi.
A wannan lokacin, na yi imanin cewa ƙofar farin ciki ce zan shiga.
Na yi imanin cewa zan shiga sabon gida ne da zan fara sabuwar rayuwa. Rayuwar da za ta kasance cike da ƙauna, kulawa, tausayawa da kuma fahimtar juna. Na yi imanin cewa zan samu mutum guda ɗaya da zai zama mafakata. Mutumin da zan faɗa masa damuwata ya saurare ni. Mutumin da zai riƙe hannuna idan na gaji, ya share mini hawaye idan na yi kuka, ya tsaya a bayana idan duniya ta juya mini baya.
Na yi imanin cewa idan na tashi da safe, murmushi zan fara gani.
Na yi imanin cewa idan na yi kuskure, za a gyara ni cikin tausayi.
Na yi imanin cewa idan na gaji, za a ce mini,
"Amina, ki huta."
Amma...
Na ɗan runtse idanuna.
Numfashi mai nauyi ya fito daga bakina ba tare da na shirya ba.
Ta yaya zan san cewa a wannan ranar da nake dariya, rayuwa tana ɓoye mini wani sirri?
Ta yaya zan san cewa ranar da ake yi mini addu'ar samun farin ciki a gidan aurena, ita ce ranar da ƙaddara ta fara rubuta mini wani labari daban?
Ta yaya zan san cewa murmushin da nake yi a gaban mutane, wata rana zai koma murmushin da zan riƙa yi domin kawai in ɓoye hawayena?
Ta yaya zan san cewa kalmar haƙuri za ta zama tamkar inuwar da ba zata taɓa rabuwa da ni ba?
Ta yaya zan san cewa ranar da aka raka ni gidan aure cike da addu'o'i da fatan alheri, za ta kai ga ranar da zan riƙa ɗaga hannuwana bayan kowace sallah...
Ba domin neman arziki ba...
Ba domin neman ɗaukaka ba...
Sai dai domin neman ƙarfin zuciyar da zan iya rayuwa da shi.
Ban taɓa zaton cewa wata rana zan wayi gari ina roƙon Allah ƙarfi maimakon farin ciki ba.
Na sauke numfashi a hankali, sannan na ci gaba da motsa shayin da ya kusa tafasa. Na share hawayen da suka cika idanuna kafin su zubo, domin na san lokaci bai tsaya jiran tunanina ba. Ayyukan gidan suna jirana, kuma ko da zuciyata tana ciwo, dole hannuwana su ci gaba da aiki.