BABI NA BIYU
Ranar da aka ɗaura aurena ta kasance ɗaya daga cikin ranakun farinciki da bazan taɓa mantawa da su ba a cikin rayuwata ba, ranar da burina ya cika. Ranar da na zama mallakin mutumin da na yi imanin cewa shi ne zai zama abokin rayuwata har ƙarshen numfashina. Mutumin da a lokacin nake ganin cewa Allah Ya aiko min da shi ne domin ya zama farin cikin rayuwata, sanyin idaniyata.
Tun da sassafe gidan marigayi Alhaji Musa ya cika da 'yan uwa, maƙwabta da abokan arziki. Ana ta kai komo, ana dariya, ana taya juna murna. Ƙamshin turare da na lalle yana gauraye da farin cikin da ya mamaye cikin gidan kowa ka kalla fuskarsa cike da annuri.Yan uwan hajiya Bilkisu suna ta kai komo ana ta kwashe abincin daurin aure ana tsokanar juna ana ta dariya, dangin mahaifina marigayi Alhaji Musa ma sunzo daga garin Katsina domin halartar daurin auren.
Ni kuwa ina zaune a ɗakina cikin kayan amare. Fuskar nan tawa cike take da annuri, yayin da ƙawayena ke zagaye da ni suna yi min barkwanci.
"Amarya, yau fa zaki bar gidanmu, zaki fara sabuwar rayuwa mai cike da yanci."
Kawata Khadija tace, " kawata Allah ya baki zaman lafiya. Allah yasamu a danshin ki ke kam kin gama dace, mijinki nada rufin asirinsa."
"Ke dai bari Khadija Amina tayi aure inda zata miƙe kafa ta huta," wata daga cikin ƙawayena ta faɗa tana dariya.
Ni dai ina sauraron su ina murmushi, amma zuciyata cike take da wani irin yanayi. Farin ciki ne da ɗan tsoro suka haɗu a lokaci guda.
Jim kaɗan muka ji yara sun shigo da gudu "an ɗaura an ɗaura."
Muryoyin mutane suka haɗu da kalmar,
"Allahu Akbar! Allah ya bada zaman lafiya," gida ya kara cika da shewa da farinciki.
A wannan lokacin, zuciyata tai wani irin tsalle. An ɗaura.! Na zama matar Alhaji Bashir, auren da na yi mafarki ya zama gaskiya.
Mahaifiyata ta rungume ni. "Allah ya baki zaman lafiya Amina."
Hawaye suka zubo daga idanuna.
'Yata," in ji mahaifiyata cikin sanyin murya, "ki riƙe haƙuri. Aure ibada ne. Ki mutunta mijinki, ki riƙe Ibada, ki yawaita addu'a. Komai ya zo miki, kada ki manta Allah, ki nemi mafita daga Gareshi, Allah yayi miki jagora cikin lamuranki."
Wannan addu'ar da mahaifiyata tayimin ta zauna a cikin zuciyata.
"Ban san cewa wata rana zan koma ga waɗannan kalmomin ba, na rinƙa tunawa dasu da koda yaushe a cikin zuciyata ba. Bansan cewa waɗannan kalaman ba kawai nasiha bane. Kalamaine da zasu taimakamin tsira daga abubuwan da rayuwa zata jefomin."
Na share hawayena.
"Zan yi iya ƙoƙarina Umma, Insha Allah zan kasance yar da zakiyi alfahari da ita."
Da yamma motocin kai amarya suka zo daukar amarya zuwa gidan ta dake Federal low-cost. Na rungume mahaifiyata ina kuka. Cikin muryar lallashi Umma tace "kiyi hakuri Amina kowacce mace da haka ta fara. Kema zakije ki zaman aure ki kafa iyali, ki kiyaye duk nasihar danai miki sannan ki zama mai yawan tawakkali, mai yawan ibada Allah ya baki zaman lafiya."
Haka na rabu da mahaifiyata ina kuka har mukazo gidana dake Federal low-cost. Gidan ba babban gida bane, ƙarami ne madaidaici mai kyakkyawan tsari.
A tsakar gidan akwai ƙananan furanni da aka shuka a gefen hanya. Bangon gidan an yi masa fenti mai launin madara, yayin da tagogi masu shuɗin gilashi ke ƙara masa kyau, daga ciki kuwa akwai falo mai dan girma, sai dakunan bacci guda biyu da kitchen. Na kalli kayan dake cikin gidan a zuciyata nace " lallai umma tayi kokari."
Da na zauna a bakin gadona na ce a raina:"Alhamdulillah. Allah Ka sanya wannan gidan ya kasance gida ne da zan gina rayuwata cikin farin ciki da kwanciyar hankalin Ka kareni daga dukkan sharri."
A lokacin, babu abin da ya nuna min cewa wannan kyakkyawan gida da nake kallon sa zai taɓa zama wurin da zan zubar da hawaye fiye da murmushi.
Bansan cewa a bayan wannan kyakkyawan fasalin akwai ƙalubalen da ban taɓa tsammani ba.
Alhaji Bashir ya yi min kyakkyawar tarba, washe gari da safe Alhaji Bashir ne ya hada mana abin karin kumallo tun kafin na tashi, da rana ma shi yayi mana jalof din shinkafa, nayi mamakin yadda ya iya girki.
Na kalle shi ina murmushi.
"Alhaji, ashe ka iya girki haka?"
Alhaji Bashir ya yi dariya.
"Kin ga dai. Ba ke kaɗai kika iya girki ba ko, wata rana idan sarautar ta tashi sai na ringa mana."
Nayi dariya. "Sarauta kuma Alhajina." "Ke din ai sarauniyata ce." Gabaɗayanmu muka kwashe da dariya.
A cikin waɗannan kwanakin Alhaji Bashir ya nunamin soyayya da kulawar da bazan taɓa mantawa ba. Na fara rayuwa cikin farinciki.
Hakan ya ƙara kwantar min da hankali na ƙara samun nutsuwa. Cikin kwanakin nan na ƙara haske, duk wanda ya ganni ya san cewa lallai ina samun kulawa daga mijina.
A kwanakin farko, na fara jin cewa lallai mutane sun yi gaskiya da suka ce na yi dacen miji.
A cikin kwanaki bakwai da Alhaji Bashir yayi a gidana na fahimci ma'anar farinciki, kullum da yamma zai daukeni a mota muje siyan gasasshen kifi, mu zagaya gari mu dawo. Ranar daya cika kwana bakwai ya koma gidan sa ranar nai kwanan kadaici domin da kyar bacci ya ɗaukeni. A haka rayuwa ta soma tafiya har na fara sabawa da zama ni kaɗi idan bayanan, har zuwa ranar dana cika mako biyu da tarewa.
Sai dai...
A ranar dana cika sati biyu da tarewa a dakin mijina, na waye gari da wani mummunar labari...
labarin da ya sauya alkiblar rayuwata, ya ruguza dukkanin mafarkaina.