A TSAKANIN HAƘURI DA ZUCIYA

BABI NA UKU

by @sadiyayusufishak133

Ranar kwana goma sha huɗu da daurin aurena da Alhaji Bashir, na wayi gari da wani labari da ya girgiza zuciya.

Da sassafe Alhaji Bashir ya zo gidana, ina zaune a falo ina sauraron karatun Al-Qur'ani a talabijin hannuna rike da kofin shayi, fuskarsa da na saba gani cike da annuri yau cike take da damuwa.Ya samu guri ya zauna shiru.

Na sauko daga kujera na gaisheshi " Alhaji ina kwana," ya amsa da "lafiya," a takaice.

Bayan mun gaisa ne, ya ce cikin sanyin murya,

"Amina, ki shirya. Mu tafi gidana."

Na ɗaga kai ina kallonsa cikin mamaki, "gidan ka kuma Alhaji,"

"Lafiya dai, Alhaji.?"

Ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana neman kalmomin da zai faɗa.

Daga ƙarshe ya ce,

"Uwargidana ta tattara kayanta ta tafi... ta bar yaran nan biyar a cikin gidan."

Nan take naji wata irin faduwar gaba na zaro ido cikin mamaki,

"Ta tafi?"

Ya ɗaga kai a hankali.

"Eh."

Shiru ya biyo baya, daga ni har shi kowa ya kasa magana.

Tambayoyi marasa adadi suka cika zuciyata, amma na fahimci ba wannan ne lokacin da ya kamata ayi su ba. Na shiga ɗaki, na fara tattara kayana cikin gaggawa. Na fito na shiga mota muka nufi gidan Alhaji Bashir.

A hanya babu wanda ya sake magana a cikinmu. Alhaji Bashir yana tuƙi, ni kuwa inata kallon hanya zuciyata cike take da tunani. "Me zaisa mace ta tafi tabar ƴaƴanta biyar , ko Alhaji Bashir ya saki matarsa ne, nan take wata zuciyar tace "a'ah ko dai yaji tayi."

Har muka iso gidan tambayoyi da yawa sun kasa fita daga zuciyata. Da muka isa gidan, na sauko daga motar a hankali, jikina duk a sanyaye ina ƙarewa gidan kallo. Gidan babbane mai kyan tsari yana da yalwar tsakar gida, sai dai gidan ya yi shiru kamar babu mai rai a cikinsa.

Da muka shiga falo, na tarar yara biyar zaune a kusurwar falon kowanne ka kalla daga cikinsu idonsa yayi jawur alamun sun sha kuka, nan take naji tausayinsu ya kama ni, kowannensu yana kallona da wani irin kallo. Kallon da ya sa na ji kamar suna tambayata wata tambaya da bazasu iya furtawa ba.

Ke wace ce?

Me za ki yi a nan?

Ina Mamanmu take?

Babbar yarinyar, Amira, mai shekara goma sha huɗu, ta yi ƙoƙarin ɓoye hawayenta.

Sai Khalid, mai shekara goma sha biyu.

Sai Jibrin, mai shekara goma.

Sai Sadiq, mai shekara takwas.

Sai ƙaramin yaron, Aryan, mai kusan shekara biyu da rabi, duk da ban taɓa ganinsu ba amma na sansu a hoto.

Aryan ya miƙe a hankali ya riƙe gefen zanina

Ya ɗaga kansa yana kallona. "Mama" na ji zuciyata ta buga.

Ya ƙara cewa:

"Ina Mama?"

Me zan ce masa.? Ina zan ce masa Maman sa take? Ta yaya zan bayyana masa abin da ni kaina ban sani ba?

Na durƙusa a gabansa, na daukesa tare da shafa kansa cike da tausayawa, na kasa maida hawayen da suka taru a idanuna. Na fara jijjiga shi " kayi hakuri kaji Aryan Mama zata dawo kaji."

Na samu guri na zauna a daya daga cikin kujerun falon ina kuma kare wa yaran kallo a cikin zuciyata nace,

"Ya Allah... waɗannan yara fa.?"

Na yi zaton iyaye zasu zo su zauna a tattauna abin da ya faru, ko domin maslahar yaran nan, na yi zaton ko za a nemo wata mata da za ta kula da su, amma shiru ba'ayi hakan ba.

Ban taba zaton wannan nauyin zai hau kaina gaba daya ba. Har yau, idan na tuna wannan ranar, sai na tambayi kaina:

Da na san irin rayuwar da zan shiga, da na shirya kaina?

Amma a lokacin...

Ban san komai ba, ban san cewa rayuwa tana shirin sauya min alkibla ba. Ban san cewa wannan ranar za ta kasance farkon wata doguwar tafiya da ba zan taɓa mantawa da ita ba.

Amma haka Allah Ya ƙaddara min, tun daga wannan rana, komai ya fara sauyawa.

Ba tare da Alhaji Bashir ya tambaye ni ko zan iya ba, ayyukan gidan suka fara komawa hannuna, aka fara kallona a matsayin wacce za ta kula da komai a cikin wannan gidan. Na zama uwa, na zama mai girki, na zama mai wanki, na zama mai gyaran gida, na zama mai kula da yara biyar tare da mahaifinsu. Alhali ni kaina, sabuwar amarya ce da ba ta wuce shekara goma sha tara ba a duniya.

Da dare, bayan kowa ya kwanta, na zauna ni kaɗai shiru a bakin gadona, ina tunanin yadda rayuwata ta sauya cikin yan makwanni. Yanzu ni kaina bana tuna cewar ni amaryace. Sannu a hankali na fara fahimtar gaskiyar da ba na son fahimta.

Na ɗaga hannayena sama.

"Ya Allah, Ka ba ni ikon ɗaukar amanar da Ka ɗora mini. Kai riƙo da hannayena. Kada Ka bar ni ni kaɗai."

Duk da haka a lokacin ina ganin wannan jarabawar za ta wuce cikin 'yan kwanaki. Ina ganin matar Alhaji Bashir za ta dawo, ta zauna da 'ya'yanta, komai ya koma yadda yake. Ni kuma in ci gaba da rayuwata a matsayin sabuwar amarya.

Ban san cewa abin da nake gani a matsayin 'yan kwanaki zai zama shekaru ba.

Ban san cewa zan fuskanci abubuwan da ban taɓa tunanin su ba.

Ban san cewa zan yi kuka a cikin dare ba tare da kowa ya ji ni ba.

Ban san cewa zan yi murmushi a gaban mutane alhali zuciyata tana zubar da hawaye ba.

Ban san cewa wannan shi ne farkon gwagwarmayar da zan ɗauki shekaru ina yi ba...

Ban san cewa wannan shi ne farkon wata doguwar tafiya...Tafiyar da za ta ɗauke ni daga rayuwar yarinyar da ta yi aure tana mafarkin farin ciki, ta mayar da ni matar da za ta koyi rayuwa da haƙuri.

Wannan shi ne farkon labarina.

Wannan shine farkon rayuwata

Farkon gwagwarmayata.

Farkon wata doguwar tafiyar da za ta kasance...A TSAKANIN HAƘURI DA ZUCIYA...