Chapter 1:RDBG
Anan ne aka mikamasa takardar sammaci daga koto, a yayinda ya lula duniyar tunanin ina ta shiga?.
A lokacinda saurayin ya fahimci cewa hankalin baffa baya tare da shi sai ya dafasa, dagowa baffa yayi sai saurayin ya gaishesa bayan ya amsa sai saurayin ya mika masa wannan takardar sai baffa ya kallesa cikin rashin fahimta, sai saurayin yace baba takardar sammacice "sammaci kuma akan me?" baffa ya tambaya cike da mamaki.
Anan ne saurayin ya labartamasa abunda ke gudana, sai baffa ya girgiza kai yace "indai akan wannan ne ai bama sai anje su koto ba na hakura na saw wake mata" yafadi hakan duk da bai soba sai ya rubuta ya bashi.