RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 1:P1

by @meefatinkwriters99

Meefat ink writers 
RAUNIN DA BA A GANI 
Meefat ink ✍️ writers 

Ananne aka mikamasa takardar sammaci daga koto, yayinda ya lula duniyar tunanin ina tashiga?. 
A lokacinda saurayin ya fahimci cewa baffa baya tare da shi sai ya dafasa, dago kai baffa yayi sai saurayin ya gaishesa, amsawa yayi sai saurayin ya mikamasa wannan takardar, kallon sa baffa yakeyi cikin rashin fahimta sai saurayin yace”baba takardar sammaci ce daga koto” “sammaci kuma akan me” baffa ya tambaya cike da mamaki, ananne saurayin ya labartamasa abunda ke gudana,sai baffa girgiza kai yace”indai akan wannan ne ai bama sai anje su koto ba, na hakura na sawwakemata “da haka ya rubuta yabawa saurayin. 
 Sallama suka jiyo awaje kan su kaiga amsawa baffa yashigo jiki a sanyaye. Mairo dake ta faman yiwa y’arta fada akan tundazu ta aiketa amma sai yanzu taga daman zuwane ta dago ta kalli baffan dake kokarin shiga parlour “baffa lfy kowa me yafaru na ganka haka jiki duk asabule? “bai kula taba yayi shigewarsa.

SHAGARI LOWCOS. 
Zaune take gaban mahaifiyar ta tana tambayar meke faruwa, saboda ganin hankalin ammiennata atashe “ammie dan Allah kifadamin ko hankalina zai kwanta, mikewa ammie tayi tana faman safa da marwa sai kuma tafara cewa ”shikenan ruhaina, shikenan ansake nemanta an rasa, gashi ita kadai taragemin ohh ni a'isha yazanyi da rayuwata “sai tafashe da kuka mai tsuma zuciya, fahimtar da ruhy tai dawa takene yasa ta rungume mahaifiyarta itama tana kuka tace ”ammie kiyi hakuri ina da tabbacin zata dawo wannan karan ma, kuka da damuwa ba shine mafitaba, mutsananta addu'a insha Allahu allah zai dawo da ita garemu.