PAGE-1
_Hi Mutanena,mutanen amana,gani na dawo fa ku shirya ku gyara Zama._ 😻🤍
PLATEAU STATE, JOS NORTH. RingRoad.
Dauke take da tulin daurin kaya akanta hannunta kuma tana rike da rake tana gatsa tamkar mayunwacin zaki. Tsohuwar dake gefenta suna tafiya ne ta ce, "Salame ai yau dai zan yi maganin Ilu duk iskancin da yake ji dashi da matar tashi sai na sauke masu shi kasa basu san cewa a zamanin ina daya daga cikin tantiran yan iskan kauye bane shiyasa suke mun wannan iskanci." Sai da Salma ta gatsi rakenta kafin ta ce, "Aradun Allah kuwa Inna kar ki raga masu sam sam kar ki raga masu gwanda ayi maganinsu ai." Ta karasa maganar suna tsaya daidai wani gida madaidaici baza ace da shi karami ba kuma ba za asa shi sahun manyan gidaje ba sai dai kam ba laifi ya tsaru wanda kallo guda za asama a tabbatar da cewa lallai mai gidan na da rufin asiri daidai gwargwado.
Buga gate din suke dukansu su biyu tamkar wa inda suke dakan sakwara. Jiki na bari mai gadin ya bude yana, "Subhanallahi wasu gidahuman ne haka?"
Inna ta kalleshi ita da Salma kafin ta ce, "gidahumai? Ni kake cewa gidahuma? Na ce ka ci gidanku ka ci gidan ku to nan gidan Ɗana ne nice nan uwar illu mai gidan nan ka kiyaye tun kafin inyi tamola da kai da shegen kai kamar kwallon mangoro."
Mai gadi ya ce, "ehto ayi hakuri ranki yadade amman ni ba kan mangoro gareni ba."
Inna ta bude baki kafin ta ce, "Au da ance ma raina ba zai dade bane? To ahir dinka dadewa kan munyi kuma muna kan yi sannan kuma kace kanka bana mangoro bane?" Ta fada tana maka masa rankwashi aka. Ita ko Salma me zata yi ban da dariya, "yawwa Inna wallahi ki kara masa har sai kan nasa ma ya koma irin na mangoron."
Hayaniya ce ta kaure tsakanin mai gadi da Inna har sai dai Alhaji Ismail da Matarsa Hajiya Maryam suka fito. Kaka na ganinsu ta fashe da kuka tana faduwa kasa. Hawaye da majina shaɓe-shaɓe a fuska ta ce, "Ilu wai har kaine zaka dauko wanda zai dunga tozartani a gidan nan? Har kaine zaka dauko wanda zai ci mini mutunci." Durkusawa Salma ta yi tana share mata hawayen tare da fadin, "kiyi hakuri Inna mu koma kauye kawai tunda tun a kofa aka fara yi mana kora da hali kiyi hakuri ni ina sonki bana so ki mutu." Ta karasa maganar ita ma tana kakulo nata kukan.
Da sauri Hajiya Maryam ta karasa tana rike Inna. Inna ta bangajeta tana , "Dalla cen guzumar munafuka ai gwamda kowa dake ni barni bana son munafurci."
Alhaji Ismail ya kalli mai gadi ya ce, "kai ko me yasa zaka yi haka? Baka san cewa wannan din mahaifiyata ba ce?"
Mai gadi zaiyi magana kenan Inna ta tunkure shi da kafarta sai da ya fadi a kasa ta ce, "munafiki ne ai kuma indai ina gidan nan sai na gyara masa zama."
Karasawa Alhaji Ismail ya yi da kanshi ya daga Inna yana, "kiyi hakuri Inna In sha Allah ba zai kara ba." Tashi tayi tana tafiya dakyar kamar wacce aka ma duka. Suna tafiya Salma ta juya tayiwa mai gadi Gwalo, can ma sai ga Inna ta juyo da tsukeken bakinta ta masa gwalon. Sake baki ya yi yana mamaki A zahiri ya ce, "Ikon Allah gaskiya akwai matsala babba a gidannan." Suna shiga cikin gidan salma ta aje tulin kayanta ta fice.
★★ Ya fito daga wanka kenan daga shi sai towel dinsa a daure karasa ya yi daidai gun windown dakinsa yana budewa. Budewan da zaiyi fitsari ne ya fara sauka masa a fuska. A gigice ya daga kai suka yi ido biyu da Salma ce tsaye ta haye kan setin windown tana tsura fitsarinta hankali kwance a tsaye. Kallonshi ta yi tana murguda baki, "ji wani kasurgumin dan iska ina fitsari yana leƙena."
Kasa hadiye yawu Abdul-Saheer ya yi kasancewar sa mutum mai zafin rai cikin sauri ya dauki belt ya fita ita kuwa Salma har lokacin tana zaune abunta tana, "gwanda ma da ka tafi don ni wallahi bana wasa da yara." Saukar Belt taji a gadon bayanta ta tsalla wani irin ihu. , "Ance miki nan gun fitsari ne da zaki zo kina yiwa mutane?" Ya daga zai kara mata tayi wani irin tsalle ta shige ciki da gudu tana, "kwarto jama'a kwarto yana dukana dan iska ne."
Tsaki Saheer ya yi ya koma dakinsa kai tsaye toilet ya nufa zai kara yin wankan domin koda yace zai wanke iya gun ne yata tsarguwa.
Salma na shiga ta birkitasu duka suka fito basu ga kowa ba. Inna ta ce, "daga zuwa birni har za a fyeɗe mun jika? Na ce har za a fyeɗe? To wallahi sai na dau mataki zan baku mamaki ga dukkan alamu dukanku yan gidannan sai na gyara zaman duwawunku domin a karkace suke duk."
Haka Inna ta zauna Salma na jikinta ance su je suyi wanka fur sunƙi.
Saheer ne ya fito cikin shirinsa zai fita dake weekend ne. Ko sallamar da ya fara bata bari ya karasa ba ta katse shi. ta fara nuna shi tana, "Inna wallahi wallahi shine kuma har lekani ya yi kuma ya dakeni." Tashi tsaye Inna tayi tana rike kwankwaso, "Iya ah lallai wato gadon uwarka ka yi Sahaaru? Gadon iskanci da fitsara Kodayake ai kasha a wancen tamulallen nonon uwar taka wacce ko nawa ya fita fasali to baka isa ba yadda ka fara gane mun ita sai ka aureta domin ka riga ka gama da ita ba zan bar gidan nan ba sai ka aureta e na ce sai ka auri salame." Daga Saheer har Iyayen nasa suman tsaye sukai sun gagara cewa komai. Salma ta.....
*** Urs Xayyeesherthou [6/25, 11:07 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*