MATAR HEDIMASTA

PAGE-2

by @xayyeesherthulhumaerath

Ta ce, "Aa fa Inna ni bana son auren dan iska yaje ya iskanta ni a banza a wofi." Tsaki Inna ta yi kafin ta ce, "Ya iskanta ki ban da tambadar da ya fara miki tun yanzu? Aure ba fashi." Ta ja kunnenta ta fada mata magana suka dago suna tafi da dariya kafin Inna ta gyara zama ta ce, "Yawwa ilu na san ka ji me na ce ai ko? Ko sai na maimaita ne? Ina so Sahaaru Ɗanka ya auri yar uwarsa salamatu."

Kallon kallo suka fara yiwa juna. Momy,Daddy da Saheer. Dady ya ce, "To Inna In sha Allah za ayi hakan." Dauko garin goronta ta yi ta zuba a baki tana mamula domin tsabar tsufa gabadaya hakoran sun wawushe. Ta ce, "Ah to ka ma Musa mana bawai naga kuna kifi kifi da ido ba kai da matar ta ka mai baki kamar tsohuwar jaɓa ga hanci kamar agwagwa na magana, eheem so nake a daura masu aure gobe da safen nan."

Wani irin mumman faduwa gaban Saheer ya yi take ya fice daga dakin cikin sauri, Momynsa ma ta fice. Dady ya ce, "To Inna amman kinsan ba a gaggawa a aure ki bari a shirya komai a tsanake tukunna kamar zai fi."

Galla masa harara ta yi kafin ta ce, "ji mun wani salon rashin daraja da guntun iskanci, me za a shirya? Na ce me za a shirya? Ba abun da za a shirya kuma aure gobe nake so a daura, yoo Ɗan naka ma da rufa mai asiri za ayi ayi masa auren kafin ya gama tambaɗewa ,tunda ya fara leƙen duniya kuma ai gaba gaba sai yawo a ciki to ba dani ba na ce ma ba dani ba auren nan gobe gobe kafin ka dawo daga asuba ka tabbatar da cewa ka zo mun da albishir andaura auren sahaaru da Salamatu in ba haka ba kuwa kasani sarai zan iya zan iya daga maka nono ka bi duniya ka watangale ."

Jiki a sanyaye ya amsata ba don yaso ba kuma ba don yasan ta ina zai bullowa lamarinta ba. Babban tashin hankalin ma bai san Dalilin zuwansu ba zato ba tsammani ita da bata son zaman birni.

Kwatsam kuwa sai jin mai gadi ya yi yana sheda cewa ana sallama da shi. Bayan ya fita ya ga yaron fadar mai garin kauyesu ne.

Bayan sun gaisa yake sheda masa cewa Mai gari ne ya aiko shi domin sheda masa cewa Salma da Inna sun yi laifi babba da ake nemansu ruwa a jallo domin kuwa sun kama matar mai garin duka su biyu sun mata dukan tsiya wanda har sai da ya kai ga ta suma sanadin kawai Don Salma ta kwacewa yaronta mangoro ta yi magana suka hadu suka dunga jibgarta kamar sun samu kayan wanki har sai da suka ga ta daina motsawa suka kwashe kayansu suka bar garin.

Sallallami Alhaji Ismail ya fara ya bashi hakuri tare da sanar da shi cewa ya bawa mai gari ma hakuri kuma In sha Allah yana nan tafe zuwa kauyen shi ma.

Jiki a mace ya koma cikin gidan ya nufi dakin Momy. Tagumi ya yi ya zauna ya yi shiru. Ta zauna gefen shi tana fadin, "Alhaji ba zama kayi tagumi bane mafita fa tunani zaka yi yadda za a bullowa lamarin domin kasan halin Inna inta kafe akan abu."

Numfasawa Dady ya yi kafin ya ce, "Hmm abun ne na rasa da wanne zan ji, yanzu fa zuwa akai nemansu daga kauye na ce basa nan na bada hakuri ga wannan batun auren da ta taso da shi kuma sannan Saheer ma ko kadan ba zai iya rayuwa da Salma ba domin yarinyar an riga an gama sakaltata gyaruwarta da nutsuwarta zaiyi wahala sosai."

Momy ta ce, "to ya za ayi karshen zancen dai kawai ka yi mata biyayya shi ma Saheer din ya yi hakuri." Dafe kai Dady ya yi ya ce, "abune mai wahala hakan ba zan so in cutar da Ɗana da hanuna ba dole zansan yadda zan bullowa lamarin." Ya fada yana tashi. "Bara in dan fita in dawo."

Saheer kuwa yana fita a gidan kai tsaye School ya nufa duk da cewa weekend ne domin ya ji bai son zaman gidan sam kuma daman gashi ba mai son hayaniya ba hakan yasa yaje ya bude office dinsa kawai ya zauna.

Saheer Namiji ne wanda ya amsa sunan namiji karfaffa domin kuwa wanda bai san shi ba zai iya alakanta da shi da jami'in tsaro kasancewar yanayinsa daya da nasu miskilanci,rashin son magana da rashin fara'a. Baya cikin sahun farare kuma ba asa shi cikin sahun bakake ba,yana da kyawun gani daidai gwargwado wanda kowacce mace zatai burin mallaka,saboda miskilancinsa yasa ko mata bai kulawa abokinsa ma guda ɗaya ne kadai wanda ya aminta da shi. Yana da tsafta da son gayu sosai daga nesa turaren jikinsa kan iya bayyanar da zuwansa waje sai dai yana da dabi'ar shan taba sigari wanda ta zame masa jiki musamman a lokutan da aka bata masa rai bai samun sukuni in bai zuƙa ba.

Yana zaune Inya tuna da abun da Salma ta mai da maganar Inna sai yaji ranshi ya baci Sosai ban da tsaki babu abun da yake. Take ya kunna tabarsa yana sha.

Salma kuwa ko a jikinta dadi take ji har cikin ranta Inna ta ce mata inta aure shi zata zama hajiya babba tayi kudi su koma kauye su kori mai gari da matansa.

Salma irin yaran nan ne masu gaɓa-gaɓan jiki gata karamar yarinya da bata zarce sha uku ba amman girman jiki da kibarta ya kai na mai shekara Ashirin. Baƙace sosai amman irin bakin nan mai kyau da sheƙi.

★★★Salma da Inna zaune suke a filin gidan sun shinfida taburma sunyi kane-kane su ci wannan su ci wancen.

Inna na ganin Saheer ya shigo da mota ta kalleta ta ce, "yawwa ga mijinki nan ya dawo maza tashi kije ki karbe shi ki mishi sannu da dawowa gwanda ki fara koya tun yanzu." Aikuwa tashi Salma tayi tinki tinki ta je gefen motar ta tsaya. Yana fitowa ta washe baki tana kokarin karban file hannunshi ta washe baki, "Barka da Zuwa Mijina." Wani takaicine ya sarƙafi zuciyar Saheer ya bita da wani gigitaccen kallo yana bisge hannunshi sai da ta fadi. Kafin Inna ta bude baki har salma ta tashi tana daga hannunta sai setin marar Saheer ta sauke masa. Bai san lokacin da ya saki wata kara ba,ta zura a guje. Ita kuwa Inna me zata yi ban da dariya. "Maddallah yoo daman Salma in baki rama ba ai ke ba jinina bace tunda shi ya yi gadon figaggiyar rashin daraja ke lukuta na koya miki."

Mai gadi ne da sauri ya karaso ya rike Saheer.....

*** Comments, Share and like Fisabilillah. Urs Xayyeesherthou 🤍🌾 [6/26, 10:16 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*