MATAR HEDIMASTA

PAGE-3

by @xayyeesherthulhumaerath

Ganin yadda Saheer ya fara muradadawa lokaci guda kuma yanayinsa ya canja,hakan Yasa Inna da Salma tashi a guje. Suna tashi kuwa aka dauke wuta dake dare ya yi. Karo suka ci da juna karaf goshin Salma ana Inna.

Wata irin kara ta yi jiki na rawa Inna ta ce, "Na shiga uku na lalace na shiga ukuna ni Shatou, Lawakiri ka yi mun rai aradun Allah bani na yi kisan ba Jikata ce, jikata Salame ce." Inna ta fada hannunta dauke a fuskarta ta rufe idanunta da daya,dayan kuma ta kankame goshinta da yaji bugu.

Har an kunna Gen bata sani ba tana kankame a tsugune tana ta sambatu lawakiri ya yi hakuri ya mata rai lokacin baiyi ba tukunna da saura. Sautin dariyar Salma ta jiyo akanta tana, "Kai Inna Sarkin tsoro karo muka yi fa da goshi ba wani lawakiri."

A hankali Inna ta bude ido tana kif-kif da ido kamar karamar munafuka ta ja dogon numfashi, "Allah na gode maka, yoo ko salame wai haka goshinki ke da azaba kamar an turo roka? Wannan ai sai ki kashe mutum amman dai goshin nan naki kwai rashin daraja ba don ni da kaina na mulmula miki maɗiga ba lokacin da aka haifeki da na ce anguwar zomanki bata iya karban haihuwa ba."

Ita dai Salma dariya take harda shidewa. Inna ta ce, "Muguwa yar masara ni rikeni in tashi don ina ji ma har fitsari na gama yi a jikina aradun Allah, jina nake fa rabi a duniya rabi a lahira." Salma ta mika mata hannu ta tallafa mata ta tashi tana fadin , "Inna anji goshin manya ysn kin bani dariya yadda kika zauna dinnan nishadi kyauta."

Da haka suka shige cikin gidan suka baje a falo domin sunki shiga daki.

★Saheer kuwa mai gadi ne ya tallafa masa ya shiga daki domin mararsa ciwo take yi masa sosai ta rike. Kwanciya ya yi na yan mintuna kafin ya tashi ya hada ruwan lipton ya sha. Aransa ya kudarci cewa duk yadda za ayi sai ya kama Salma ya hukuntata. A zahiri yake fadin, "wannan yarinyar sam bata da tarbiya babu shakka sai nayi maganinta na sa ta samu nutsuwa." Ko cikin gidan bai shiga ba ya kulle kanshi a daki hatta sallah ma a ciki ya yi.

Salma da Inna na falo suna kuskus da tsoron cewa kar fa azo ace sun kashe Saheer.

Salma ta ce, "ni gwanda ma ya mutun ai yana nan kamar wani dan kasar waje." Inna ta ce, "ke wawiyace matsalata dake salame gwanda ya rayun ai ki aure shi baza ki gane abun da nake nufi ba, ba don ba ba aure tsakaninki da uban shi ba ai da ubanshi zaki aura amman sai dai kash shi yasha Nono ya barwa Uwarki ta sha." Suna cikin magana sai ga Alhaji Ismail ya shigo falon.

Durkusawa ya yi gaban Inna ya gaisheta sai ya yi shiru. Fara wura hanci Inna tayi tana dagawa ganin ya shigo da leda ga kuma kamshi na tashi. Ta ce, "Illu miye ne a ledar cen? Ji nake kamar kamshin gashasshiyar kaza miko min nan Salame."

Jiki na rawa Salma ta tashi taje ta dauko ta baje a gaban Inna suka bude. Fara ci suka yi kamar sabin kamu musamman Inna da saidai ta mamula ba iya taunawan ma take ba.

Alhaji Ismail ya yi gyaran murya kafin ya ciro wani dumin kudi a aljihunsa ya ajewa Inna a gefetan tukunna ya ce, "Inna Daman ina neman alfarma ne ban sani ba ko zaki amince." Inna na mamular nama ta ce, "ina jinka Illu illu dan albarka ina jinka ka yi gadon mahaifinta wajen sanin abun da nake so Illu nawa."

Dady ya ce, "daman kan auren Saheer da Salma ne,na ce me zai hana ki bari ta kara girma tukunna sai nake ga kamar ai tayi karama a yanzu za a cutar da it.....

Kafin ya karasa maganar ta fecar da kasar bakinta ta rike bango ta tashi tsaye ta kalli Salma ma ta ce, "ke salame tashi tsaye." Salma ta tashi tana jan cinyar kaza. Inna ta ce, "Yawwa juya gaba da baya." Salma ta juya. Ta ce, "to yi tafiya daga nan zuwa can." Salma ta taka daga farkon falon har karshe. Inna ta ce, "yawwa ince dai idanunka sun gani? Ko ta kara juyawa ne?" Alhaji Ismail ya girgiza kai alamar aa. Inna ta ce, "Yawwa batun aure ba fashi ka kalleta ka kara kallo." Ta nuna salma da hannu kafin ta ci gaba da fadin, "Diri iya diri gashi nan sassakar budurci iya sassaka gata nan,inma ƙirjin ne gashi nan a wadace dake gado tayi ba irin da shamulaliyar matarka ba,shi ma duwawun dai gashi nan kamar a dasa turmi ya zauna, mace iya mace son kowa kin wanda ya rasa salame ta kai,don haka ahir dunka da cewa tayi karama a aure ka cuceni ka kasheni da raina bayan danku ya fara leƙe mun ita,kai tsaya ma,wai kai bakasan diri ya gani ya furgice ba har yake kokarin fyedemun ita ? To ko yau na fadi na mutu indai Sahaaru bai auri salame ba ban yafe ma ba." Tana fada ta barke da kuka tana jan majina ta tattaro gefen zaninta tana gogewa.

Salma ma zama tayi tana kukan tana kwanciya jikin Inna.

Jiki na rawa Dady ya ce, "kiyi hakuri Don Allah Inna, kiyi shiru In sha Allah za ayi abin da kike so."

Inna na sheƙan majina ta ce, "Illu Indai ba so kake in hadiye zuciya in mutu ba ka hada Sahaaru da Salame ." Murya na rawa ya ce, "e e In sha Allah Inna yanzu to kiyi shiru Don Allah."

Share hawayen ta yi ta dauki kudin da aje mata gefe tana, "wa innan kudin da su zan yiwa salame hadin amare, kai ma kuma kaje a hada danka ehee." Salma ma ta share hawayen tana washe baki.

Dady ya ce, "amman za a bari zuwa jibi ko Inna? Kinga yanzu ban tanadi su goron daurin auren ba."

Inna ta ce, "e ba matsala Allah ya kaimu ai kamar yaune amman ka sani daga ranar ba dadi ba kari."

★★★Washegari. Da sassafe Salma ta fice tana zaune gefen motar Saheer tana wasa da kasa dake wajen akwai kasa ita har ma ta manta da abun da ya hada su jiya. Shi ko ya fito kenan ya shirya zai tafi school dake monday ne. Aiko yana ganinta ya koma da sauri ya ciro belt. Har ya fito sai kuma ya koma ya aje belt din tasa ya kara fitowa. Ji tayi kawai an dauketa cak. Ta fara wuntsili da kafa tana ihu hannunsa yasa ya rufe mata baki ya kaita dakin nasa yana shiga ya dauki tsimma ya rufe mata bakin ya daureta a jikin Window sannan ya dauko belt din ya......

*** Urs Xayyeesherthou [6/27, 9:54 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*