PAGE-4
Ya zabga mata a gadon baya, kara Salma take son yi amman babu hali saboda ya riga ya kulle bakin. Tana ta wutsil wutsil da jiki tana kokarin kunce daurin da ya mata. Cikin fushi Saheer ya kara sake mata Belt dinnan a jiki wanda don azaba sai da ta saki fitsari a gun ga wata irin zufar wahala da ta keto mata. Jin karar abu na zuba ya kalli kasa, aiko idanunsa suka ci karo da fitsari na tsiyaya kan tais dinsa kamar famfo. Wani takaicine ya kara sarƙafansa a zuciya. Ya ce, "Wai ke wacce irin bagidajiyar kazamiyar yarinya ce? Fitsari? Fitsari zaki mun anan? Aiko sai kin goge shi tas da kayan jikin ki, kafin nan ma zaki kara zuwa ki hau mun mota inyi magana ki mun rashin kunya har ki kai mun duka mara?" Ya fada yana murɗa mata kunne. A galabaice ta girgiza masa kai alamar e. Ya kara sake mata belt din kafin ya ce, "zan kunce ki kuma ki cire wannan zanin naki mai dauda ki kwashe fitsarin nan tas." Ya fada yana kunceta. Salma ido ya yi fiki-fiki anji azaba. Haka ya tasata a gaba ta cire zaninta tana kwashe fitsarin daga ita sai wani gajeran wando da dauda tasa ya canja launi domin yanayin fari garesa amman ya koma brown brown don azabar kazanta ga wani munafukin wari da ke tashi.
Kasa jure tsayuwarta agun Saheer ya yi,tun yana toshe hanci har ya gagara ya ce, "Just Go." Yana kara rufe hancinsa. Ina Salma kam bata san me yake fada ba kara gogewa take. A fusace ya ce, "Ya isa ki fita na ce."
Rungume Zaninta mai fitsarin ta yi ta fice da gudu sai da ta zaga daidai windown da yake tsaye ya yi tsuman tsaye ya tura kanta tana fadin, "Mugu azzalumi Dan Masara mai bakin Daddawa kan tafarnuwa aradun Allah sai na rama mai idon damusa kawai." Tana fada ta tattara yawo ta watsa masa daidai fuskarsa kafin ta arce a dari ta shige ciki.
Rikicewa Saheer ya yi take kansa ya fara wani gigitaccen ciwo,idanunsa suka kada suka yi ja. Cikin sauri ya shiga toilet ya fara wanke fuskarsa yana wanken bakinsa. Karshe sai da ya kara brush ya kara yin wanka yasa kaya. Da sauri ya bar dakin domin gabadaya a tsarge yake da dakinma.
Ciki ya shiga domin gaida iyayen nasa, ya shiga dakin Momy ya gaidata har zai fita ta ce, "Saheer." Ya juyo ya kalleta yana amsawa. Ta ce, "sai dai ka yi hakuri kuma ka sa aranka cewa babu Ɗan da zaiyiwa iyayensa biyayya ya taɓe biyayya bata taba zama a banza ka da kasa komai aranka ka ji cewa kawai duk abun da Ubangiji ya tabbatar shine daidai a garemu duka."
Da mamaki ya kalli Momy domin sam bai gane inda ta nufa ba,don shi ya ma mance da wani batun auren shi da Salma. Ya ce, "Momy ban gane ba,me ya ke faru wa?"
Momy ta ce, "magana nake akan aurenka da za a hada dana yar uwarka Salma."
Momy na fada Saheer ya kara ji kanshi ya yi wani irin sarawa. Da sauri ya dafe kan.
"ka karbi hakan a matsayin kaddara da biyayya kuma In sha Allah nan gaba zaka alfanun hakan." Momy ta fada.
Kau da kanshi ya yi kawai bai ce komai ba ya fice. Momy ta kara fadin, "Dadynka na falo kaje ku gaisa kafin ka fita."
Falon ya shiga kuwa ya tarar da shi zaune da Inna da Salma. Salma na ganin shi ta fara murguda mishi baki tana harara. "Inna kin ga wallahi duka na ya dunga yi da wani abu kamar wayar injin mugun ne."
Gaishe da ita Saheer ya fara, "Inna an tashi lafiya?".
Da harara ta bishi kafin ta ce, "Gidanku na ce ka ci gidanku da ban tashi lafiya ba zaka ganni hakane? Kodayake ai daman kai da Uwartaka fatan mutuwa kuke mun to ahir dinku na fiku tijjara da tashanci ni fa na gama fahimtar take taken yaron nan wato saboda kazo fyeɗeta baka samu galaba ba shine ka daura mata karan tsana da duka? Na ce to karbi nan gidanku gobe goben nan za a daura maku aure sai kaje can ya karata da maitarka." Ta kalli Dady kafin ta ce, "Illu ka ga abun da nake gudu ko? Wannan Ɗan naku tuzurun tuzure indai ba a gaggauta anyi abun nan ba akwai lukutar matsala kana ganin idanun sa ma ai ka ga mai bidar aure , gabadaya ya ga yarinya yar dumurmur ya birkice to ahir ayi abun da ya dace amman ban da duka."
Dady ya ce, "In sha Allahu Inna."
Saheer ya gaida Dady ya fice cikin sauri a dakin domin ya fara kasa gane kan shi. Bai nufi School ba,a kan hanya ya yi parking motarshi gefe ya kunna sigari yana sha. Aranshi yake fadin, "wai da gaske wannan bagidajiyar kazamiyar yarinyar za a aura mun? Aure ni kuma da wannan yarinyar? Mu zauna gida daya? Inuwa daya? Kai Never." Ya fada da karfi.
Inna ta kalli Dady ta ce, "Yawwa Illu maza ka tashi ka je a tanadi goro da mintinan kan lokaci kuma kar a manta a kawo mun nawa yawwa, ke kuma Salame tashi mu shiga daki in baki wasu sirruka domin nan da gobe kin zama matar aure, kar waccer figaggiyar matar mai kirjin faranti ta ji ta karu maza mu shige ciki." [6/28, 12:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*