PAGE-5
Tashi Inna da Salma suka yi suka shiga cikin daki. Dukaninsu suka ɗare kan gado. Inna ta kalli Salma kafin ta ce, "Salame, ki jini da kyau ki saurareni yau zan baki sirrin da ya sa na mallake zuciyar Kakanki Malam Auduwana, kai Allah sarki Malam Auduwa na shatou mun diga soyayya fa kamar ba za a mutu ba mu fa tsabar soyayya har zuciyoyinmu magana suke da juna,haka inuwarmu in muna tafiya basa taba rabewa zaki gansu manne da juna, ina fada miki ka da ki kuskura ki bar mijinki shi kadai duk inda yake kina bibiyarsa sannan kina daukan wanka kina kashe kala wannan jagirar da kike ta kauye karki fasa."
Salma ta ce, "Tom Inna ai nan ban da kayan kwalliyan fa." Inna ta ce, "Shi mijin naki ne ai zai siyo yoo ai shi zakiyi yiwa kwalliyar nidai ina fada miki, kuma ki dunga yi masa fari da idon nan." Inna ta karasa maganar tana wani irin juya ido. Kwaikwayonta Salma ta fara suka kyalkyale da dariya Inna ta ce, "Yawwa hakan kina ganinsa ki fara kina tande baki kina tsukewa wannan lamari ba karamin kara ɗankon soyayya yake ba,ko ya fita ke kawai zaina gani cikin idanunsa kamar ni da malam amadu shi fa ko kasuwa yaje in ba na bi bayansa ba ko ya dawo gida ya ganni mun hada ido nayi masa farin nan hankalinsa sam bai kwanciya."
Salma ta gyara zama ta ce, "ai tare ma zamuna fita da shi duk inda zaije dinnan."
Inna ta ce, "Yawware yar albarka haka nake son ji, in kuma baya nan ya dawo,yana dawowa ki rungumeshi irin rungumar da kike gani a talabijin din mudi mai balangu na yan indian nan."
"Eee ee na gane inna har hada bakinsu suke fa suna wani abu wai shi kuss (kiss)" Salma ta fada tana tafi da hannunta tana dariya.
Inna ta ce, "Tabbas kuss tsuke bakin ake sosai asa a ciki,yanzu ma kin ga kije kiyi wanka kisa kaya zanje in karbo miki kayan kwalliya gun waccer matar kafin ya dawo da dare ya ganki kin dau wanka."
Hakan aka yi kuwa Inna taje ta titsiye Momy ta karbo kwalli da hoda salma na wanka ta mulka wata irin gira daga gishi har ido ta cika bakinta da baki tana juya ido. "Aradun Allah Inna na san inya kalleni suman dadi zaiyi domin na san na yi kyau na fitar hayyaci wooo ni Salame ."
Inna tayi wani guntun murmushi ta ce, "ai Indai ina raye sai sahaaaru ya zame miki mijin kan ta ce ma." Mai Salma zata yi ban da dariya har cikin ranta wani dadi da shauki take ji.
★★Salman kuwa da ya fitan ma bai samu nutsuwa ba har sai da ya sha sigarinsa kamar yadda ya saba kafin ya shiga school. MARIA MEMORIAL PRIVATE SCHOOL. School ce mai kyan gani da kuma sanya son kasancewa a ciki ga dukkanin wasu yara masu tasowa domin cike take fal abubuwan wasaani da karatu. Saheer shine Headmaster a school din kuma yana koyarda Mathematics ga yan primary 4 da 5.
Yana samun girmama matuka agun teacher din da students domin duk miskilancinsa yana da saukin kai da tausayi.
★★★Koda dare ya yi Saheer ya dawo bai shiga cikin gidan ba,domin aransa ji yake baya son ganin salma sam in ko ya ganta zai iya kasheta a yadda zuciyarsa take. Inna da ita nata faman jiran shigarsa sunji shiru. Inna ta ce, "maza ke tashi muje ki dauki mayafin ki muje kuyi zance ba zan iya da wannan lamarin naku ba dake shi din munafukine yana so yana kaiwa kasuwa Kodayake ai da kunya yaga asirinsa ya tonu na gano shi."
Suka fita sunata bambami. Daidai kofar part dinsa suka je suka tsaya suna bugawa kamar zasu buga kofar. Inna na fadin, "kai sahaaru ka bude mune nan ."
Tsaki ya yi ya bude kofar ba don ya so ba. Suna hada ido da Salma ta fara kada masa ido tana fari tana cuno masa baki kamar zatai mai kiss.
Inna ta ce, "hira na kawota kuyi, ee hira zance zakuyi na masoya kafin gobe a daura maku aure." Saheer ya ce, "Inna kaina ciwo yake Don Allah ku barni in huta." Yana fada Inna tasa hannu aka ta kurma ihu tana, "na shiga uku na lalace Sahaaru har ni zan ce ma kayi abu ka ce baza ka yi ba? Har ni." Su Dady na fitowa ta kara daga murya tana kuka tana share hawayen da mayafinta. Shi kam Saheer ma ya rasa abun cewa binta da kallo kawai yake cike da mamaki ita kuma Salma na rarrashinta. Dady ya ce, "lafiya Inna?" Inna ta nuna saheer ta ce, "Yoo ina lafiya ilu ,na ce ina lafiya? Ummmm wai har nice zan sa sahaaru abu yaki? Wai daga na ce suyi zance da Salma tunda gobe za a daura masu aure wai shi aa kar mu dame shi,dole inyi kuka dole inyi kuka." Ta karasa maganar tana kara kakulo kukan .
Dady ya ce, "ki yi haquri ki daina kukan Inna Don Allah." Ya kalli Saheer kafin ya ce, "kai kuma ka fito ku zauna kuyi zancen ai ko ba komai yar uwarka ce."
Inna ta ce, "sosai ma kuma matarsa ba."
Haka Inna ta tasa su a gaba suka zauna a falo . Salma ce kadai ke sambatunta Saheer kam takaici ya hanashi fadin komai. Karshe sai wayo ya musu yace zaije ya dawo ya yi ficewarsa.
Washegari Dady na dawowa daga sallar asuba ya shedawa Inna an daura auren Saheer da Salma kamar yadda ta bukata. Inna ta ce, "Ma sha Allah Illu Allah yyi ma albarka ince dai wani gidan zasu tare ba nan ba ko? Suje can su ci amarcinsu ni zan zauna anan sai ta haihu sai inje can in mata wanka."
Dady ya ce, "In sha Allah yanzu ma zan kira Saheer din muyi magana."
Zuciyar Inna fara sol domin ta samu abunda take so.
★★Jiki a sanyaye Saheer yake durkushe gaban iyayen na shi. Dady ya ce, "na san cewa an wuce zamanin auren dole, don haka ina so kasa aranka cewa kai ba auren dole aka yi ma ba, auren biyayya da kuma sadaukar ne, sannan ina so ka mai da Salma makaranta ku dinga tafiya tare domin tamkar ceto rayuwarta zaka yi ,a cire ta daga duhun jahilci da kuma abubuwan da take wanda sam basu kamata ba dole sai ka yi hakuri amman ka sani akwai ranar yin murmushi da farinciki mara misaltawa da ikon Allah don haka zan baka keyn wancen gidan zaku tare acen an gyara anyi komai yau da dare In sha Allah acen zaku kwana." Saheer bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron iyayen nasa har suka gama yi masa nasiha ya yi godiya sannan ya tashi.
Tun yamma Inna ta daurewa Salma tsimmokaranta a tsimma suka zauna suna jiran Saheer yazo ya dauketa. Harda kular dafaffen abinci. Ba yadda ya iya kuwa hakan aka yi ta shiga mota. Sai tabe tabe take tana yi masa sambatu shi kuwa aransa ji yake kamar ya jefar da ita ta windown. Suna shiga gidan ya shige daki ya barta a falo ta baje kular abincinta ta fara naƙa sai da ta ci ta koshi bayan nan kuma ta bige da kallo. Da taga ta fara jin barci ta bishi ciki. Tana shiga ta tarar shi kam Saheer ya jima a duniyar barci daga shi sai singlet da gajeren wando. Itama afkawa kan gadon tayi ta baje tana barci. Tana daga kafarta sai cikin bakin shi. Ga wani gwarti da take gabadaya ya mamaye dakin. Baki a bude duk ta wage jikinta kan gadon. Jin abun da ya yi a bakinsa yasa shi saurin bude ido......
*** [6/29, 11:12 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*