PAGE-6
Cikin bacin rai Saheer ya hular da kafarta gefe ya tashi ya daka mata duka abaya. A zabure ta farka tana, "wayyo wayyo Allah na." Ya daka mata tsawa, "ke dalla yi mun shiru, ke wai baki da hankali ne? Haka ake kwanciya? Wai ma waya baki damar kwanciya mun akan gado ne?"
Sai da ta gama kare mishi kallo kafin ta Wage baki tana hamma tukun ta ce, "Mtsww aradun Allah ni na zata ma wani abun ne yake hwaruwa, gado kuma ai na mijina ne ko ance ma mata da miji na rabuwa ne? Inna ta ce a tare zamuna kwana kuma manne da juna ma kuwa muna shakar numfashi saboda yana kara dankon soyayya." Ta fada tana komawa ta kwanta daf da shi. Cikin zafin rai ya tureta gefe sai da ta fadi akan gadon. Ta tashi tana, "Kambala'i ashe za ayi ruwan bala'i da masifa cikin daren nan tureni ka yi fa har na fadi? To da na gurde fa? hmm ka ci sa'a barci nake ji amman ka sani bashi ka ci kuma sai na rama babu fashi." Ganin da gaske dai bazata bar gadon bane yasa Saheer daukan filo ya fita falo dake gidan karamine bed room dayane kadai. Ita ma filon ta dauka ta bi bayan shi. Yana kwanciya akan 3sita kawai ya ganta tsaye akanshi tana, "matsa mun to nima." Kallonta ya yi ya kara kallon inda yake kwancen A zuciyarsa ya ce, "ina ga dai wannan yarinya ta tabu." Ya rufe idonsa zai koma barci. Jinta ya yi kawai ta kwanta akan shi kamar an jibga kayan wanki. Ya hankadata ta fadi kasa ya tashi ya sake mata wani gigitaccen mari biyu ta kowanni bangare. Ihu ta fara tana birgima. Saheer ya ce, "ke wai wacce irin mayyace? To wallahi kika kara bina ko kika kara kuskura kika zo inda nake bare har ki taba jikina sai na baki mamaki."
Rike hannunta tayi afuskarta tana, "na shiga uku wayyo ni wayyo Allah na,kuma wallahi sai na fadawa Inna ka ce kai baza kana kwana dani akan gado ba wallahi sai na fada." Saheer bai kara kulata ba har ta gama kukanta da sambatunta barci ya yi awun gaba da ita a falon.
Asuba na yi ya tashi zaije ya yi sallah ya ganta yashe baki a wangale ga gwarti ga yawon barci ga kafofi duk a wangale. Tsaki ya yi ya wuce ta gefe yaje masallaci ya dawo . Ruwan sanyi yaje ya dibo ya watsa mata domin bai son ko hannunshi ya tabata. Aiko a firgice ta tashi. Ya ce, "maza ki tashi kije kiyi sallah kiyi wanka ki shirya zamu fita tare muje School."
Da magagi take tana kokarin komawa amman tunda ta ji ya ce za su fita tare da sauri ta tashi tana washe baki tana , "To Miji... miji...mijinaaaa."
Tana cewa mijin nan wani takaici ne ya kara tokaran saheer a kirji. Tsaki ya yi kawai ya nufi kitchen. Indomie ya dafa masu da kanshi ya zuba mata sannan shi ma ya zuba na shi.
Ajiye mata ya yi,bayan tayi wanka tana sallah idonta na kan indomie tana yi mi shi gyaran murya. Ko kallon inda take bai ba bare ya kulata aiko da sauri ta dungura sallar nan ta tashi ta fara nakar indomie. Tana ci tana, "cab miji ashe ka iya girki, amman ko ni naji dadi ashe Inna ta iya zabe,ita tasan me ta hango tace sai munyi aure ji taliyar yaran nan kamar karta kare caii dadi iya dadi, aure dadi miji dadi." Ta na magana Saheer ji yake kamar ya tura ta cikin rami ya boye. Ta cinye tas sauran romon kuwa daga filet din ta yi tasa a baki ta shanye tas. Ko wanke hannu bata yi ba taje ta zumbula wata katotuwar rigarta duk da cewar tana da jiki amman yawo take a cikin kayan. Ya dauki hoda ta mulla ta kara kwaba farar hodar da ruwa tasa a bakinta. Gaban Saheer ta tsaya tana, "miji kalleni na yi kyau?" Daga kan da zaiyi sai da ya zabura domin ta koma kamar wata fatalwa. Rai baci cikin daga murya ya ce, "common jeki goge wannan shirme da haukan naki baza ki bini da wannan haukar ba." Da gudu taje ta wanke tana"cab yanzu haka kishi yake yi na yi kyau kar a kalle mai ni ,yoo da yaki fita dani ai gwanda inje in goge ,ysn kishi yake ya ga kyakkyawar mata." Saboda ta riga ya gama caba fuskar raguwa dai hodar tayi amman da sauran fari farin. Ta koma tana washe baki, "Mijin na goge." Bai ce komai ba ya tashi. Ita ma ta bi bayan shi.
Suna shiga motan sai ga kiran Dady ya na cemai su biyo ta gida kafin su wuce zai bashi sako.
Suna zuwa gidan Salma ta shige a guje ta rugume Inna. Inna ta ce, "ke wai har kin gama amarcin ne ya haka?" Sallamar Saheer ce ta katse su Da yake duka Momy har Dadyn ma suna falon. Dady ya ce, "e zasu je makaranta ne zata fara zuwa Inna kinga ba dadi abarta a gidan ita kadai." Inna ta ce , "Ah eeh kuma kam hakane ya yi kyau."
Bayan duk sun gama gaisawa Dady ya bawa Saheer Files din da yace ma shi yazo ya karba. Zai tashi kenan Salma ta ce, "Yawwa Inna ba kin ce gado daya zamuna kwana ba?" Inna ta ce, "kwarai kuwa yo mene ne auren in ba kwana gado daya ba?" Salma ta ce , "aradun Allah cewa ya yi wai shi bazai kwana dani ba har da tureni a kasa kuma wai ko jikinshi kar in kara tabawa."
Kuka Inna ta fashe da shi, "Oh Allah oh duniya yanzu Sahaaru abun da za ka mun kenan? Ka ce baza ku kwana gado daya ba? Sahaaru in baka kwana da matar ka ba dawa zaka kwana?bakin ciki kake mun da ganin yaran salame kafin in bar duniya? Sahaaru anya kana so ka ga Annabi kuwa? Wato da so kake ka ci bulus ka ci bati siddin anki an rufa ma asiri shine bari mu ka tona mana" Ta kara fashewa da kuka. Dafe kai Dady ya yi,ya kalli Saheer ya ce, "Ka bawa Inna hakuri kuma daga yau kar ka kara cewa ba za kwana da matarka ba kar in kara jin abu makamancin wannan." Saheer ya ce, "kiyi hakuri Inna in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba." Share hawayen ta yi ta ce, "to too Allah yasa, ku tashi ku tafi."
★★Suna zuwa school din ta fara washe baki tana, "mijin nan ne makarantar da zaka sani?" Wani gigitaccen kallo ya bita da shi da yasata yin shirun dole. Office dinsa ya wuce da ita kai tsaye sannan ya kira wata teacher ya ce mata ta je ta mata interview kafin a bata class.
Rike mata hannu tayi suka fita suka shiga wani office din. Ta mika mata takarda da biro ta ce, "Oya write ur name." Kallonta salma ta yi da mamaki tana, "namai? Namai kuma?" Teacher din ta yi murmushi ta ce, "Sorry rubuta mun sunanki." S din ta fara rubutawa tana kallon gabas kafin ta rubuta a na kallon yamma l din kuwa tun daga kasa har sama aka rubuta anan ta tsaya. Ta washe baki tana, "gashi nan malama." Teacher Hafsat ta ce, "mene ne sunan naki?" Salma ta kara washe baki kafin ta ce, "Salamatu amman Inna na ce mun salame amman yan garin nan gidan yan uwanmu ce mun suke salma."
Teacher Hafsat ta jinjina kai kafin ta ce, "to zaki iya rubuta mun Abcd yanzu?"
Salma ta girgiza kai, "cab aradun Allah ban iyawa duka na dai iya rerawa da waka duk."
Bayan Teacher ta gama yi mata tare suka koma office din Saheer ta ce, "Sir gaskiya akwai matsala bata iya abubuwa ba da dama infact ma zan iya cewa tana bukatar sabin darusa ne indai ana son karatunta ya tashi da sauri." Saheer ya ce , "ok Teacher Hafsat amman me kike ganin ya dace a mata a yanzu?" Teacher Hafsat ta ce, "ehto ina ganin akaita primary four amman kuma a bawa iyayenta shawarar ana mata lesson a gida domin zamanta a primary 1 to 3 zai iya durkusar da ita maimakon so da ake ta tashi tunda duk yarana kananu sosai, in akace sa'a kuma ta maida hankali ina ganin za a iya samun abun da ake so."
Saheer ya ce, "Ok to ki kaita class din yanzu sai kije ki duba ko za asamu uniform daidai nata da duk wasu materials ki hada ki kawo mun nan."
"Ok sir." Ta amsa kafin su suka fice.
Salma na shiga class kallon kallo take da yan ajin kusa da wani namiji da girman jikinsu ya kusan zuwa daya ta zauna. Ya daga mata hannu. Ta washe masa baki tana, "sunana salame kai fa." Ya ce , "Habib." Dariya ta yi ta ce, "Habibu."
Kwanciya tayi akan desk ta fara barci har sai da lokacin break ya yi Habib ya tabata. Tana fita ta yi office din Saheer. Cike yake da mutane ya yi baƙi ko a jikinta ta bankada ta shige tana, "Mijin an fita tara,ka bani kudin tara......