PAGE-7
Saheer ya kau da kai kamar bai ji me take fada ba. Ya ci gaba da yi musu bayani. Karasawa gabansa ta yi ta ce, "Mijin na ce ma an fito tara ka bani kudi inje in siya abu nima in ci." Ganin hankalin kowa agun ya koma kanta yasa shi yin gyaran murya ya ce, "Sorry guys she's our new student and she comes from villege,so she may not be familiar with our way of behavior." Yana karasa maganar ya duba aljihunsa daga 500 sai 1000 , 500 din ya mika mata domin damuwarshi kawai ta fice daga office din ne a halin yanzu. Aiko yana mika mata ta fisge da sauri ,ta juya zata tafi Coke din ta gani gaban bakin ta koma ta kallesu sai da suka hada ido kafin ta dauka ta zura aguje.
Sai da taje bakin kofar zata fita kafin ta juyo ta kallesu ta yi gwalo kafin ta ce, "in kana da karfi kazo ka kwata." Ta arce a dari. Dariya suka fara ban da Saheer da ya kulla. Ya yi gyaran murya ya ci gaba da maganarsa. Ita kuwa tana fita school shop din ta nufa inda ta ga yara na siyan abubuwa.
Tana zuwa ta mika kudin tana abani, "fanke." Tsayawa kallon ta matar tayi domin ita bata fahimci me take fadi ba. Da salma ta ga haka ta ja robar fanken ta ce, "ki bani wannan fanken guda uku." Sai a lokacin ta gane ta zuba mata uku a leda sannan ta bata canjin dari biyu dake dari dari ne. Salma na karba ta baje school compound . Gabadaya ta wage jiki kamar an aje kayan dauda. Ta sa bakinta ta bude coke din, ta fara cin fanken tana hadawa da coke din hankalinta kwance tana waƙa. Sauran student din sai binta da kallo suke tamkar tv. Wata ta zo wucewa tana kallonta. Bakinta cike fal ta fara galla mata harara tana, "ke dilla ya da kallo? Na ci tuwon gidankune ban wanke kwano ba? To mijina ne ya bani kudin tara na siya ehee kwadayayya kawai." Ta kara galla mata harara.
Tsayawa yarinyar tayi tana mata kallon tara saura kwata ta ce, "villege girl."
Salma bata fahimta ba ta ci gaba da zakan coke da fankenta. Sauran kawayen yarinyar ne suka hadu su biyar suna kallonta suna dariya suna fadin villege girl. Daya a cikinsu ta ce, "She's not getting it, she only speaks hausa, so let's switch langauges." Suka fara fadin, " 'Yar Kauye kawai , katuwar banza ji beta ta wani baje tana shan coke." Salma na jin jawabansu ta tashi ta ajiye coke din da sauran fanken gefe ta cire karamin dankwalin dake kanta ta daura a ƙugunta ta ce, "ni kuke cewa yar kauye? Ni kuke cewa wawiya?" Nunata da hannu suka yi suna dariya, "e din wawiya yar kauye ka....
Kafin su karasa rufe baki Salma tayi kansu gabadaya dukansu take ta ko ina ba ji ba gani gasu su biyar ita daya amman ta gagare su. Da gudu sauran yaran dake gefe suka kira displine master din school din. Aiko dakyar ya kwacesu a hannun salma. Daga mai fasasshen baki sai masu kumburarren goshi duk ya yi ƙulu rudu rudu domin dukansu take ta ko ina harda wacce ta ciza kumatu. Sai numfarfashi take tana fadin, "ba ku kun iya raini ba? Iye ku kun iya raini? Ance muku ni sa'ar kuce? Mijine dani e mijine dani." Sai da displine master din ya zabga mata bulala kafin ta yi shiru tana cuno baki tana sosa baya. Kamar bakin ya mutu sai kuma ta ci gaba da sambatu, "gaba kwa kuma waya ce muku ni ana kawo mun wargi wallahi zan balballa yarane gida saba in ba tara, ni ba sa'ar wasanku bace ko a kauye ma ni ba saar yara bace bare nan." Kallonta displine master din ya yi ya ce, "After all this nonsense you've done, you should be ashamed to speak further. You ought to be more reflective,Oyaa get on your knees." Kura masa ido ta yi tana kallonsa, kafin ta ce , "ni kuma? ni na yi me? Su fa suka rainani ni ban kulasu ba cin kayan dadina nake kawai suka fara tsokanata." Dafe kai ya yi, ya ce, "ki durkusa akan gwiwarki yanzu nan zaki dauki hukunci."
Salma ta zare ido , "cab hukunci? Hukunco aradun Allah ba mai dukana kuma naki dukawa kan gwiwar." Kara zabga mata dorinar hannunsa ya yi da ta saki wani sauti sai da ya karade School din. Jin hayaniya tayi yawa yasa Saheer saurin fitowa. Salma ya gani tsaye tana rike da baya tana bambami ga sauran student mata biyar jina jina sun bugu wata har bakinta ya kumbura mai kumatu ma ya yi combis haka ma goshi sai kyalle yake na azaba.
Yana zuwa Salma da gudu ta koma bayan shi ta tsaya tana rike shi, "mijin wallahi su suka raina ni yaran can kuma ka ce musu ni matar aure ce,kuma kai ne mi......
Kafin ta karasa ya mata wata irin gigitacciyar tsawar da sai da ta razana. Ya ce.....
Saura page daya free pages su kare maza hanzarta ki fara biyan naki domin har yanzu ba a fara asalin wasan ba😻 shagali na gaba. 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank
Evidence of payment to *** [7/1, 8:43 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*