PAGE-8
"Ki mun shiru kar in kara jin bakinki anan gurin."
Salma ta cuna baki tana un uni kasa-kasa.
Saheer ya ce, "Oya ka daukesu aje ayi ma wajen da suka ji ciwo dressing in an gama kuma su zo office su sameni."
Salma dai tanata magana kasa-kasa , "aradun Allah yara suka ƙara rainani sai na ci musu mutunci marasa karfin banza da wofi kawai." Jan hannunta Saheer ya yi ya shiga da ita office dinsa sai da ya rufe kofar kafin ya rike bakinta da hannu, "kin ga wallahi in kika kara cemun wani mijin ko miji a cikin makarantar nan sai na yanke miki baki sai na farfasa miki shi ya yi caɓa-caɓa."
Kokarin fara bude baki ta cijeshi tayi ya yi saurin sake mata bakin. Murgudawa ta yi kafin ta ce, "to karya na yi? Ai ba karya na yi ba kai mijina ne ko kaƙi ko kaso ehee kai mijina ne mijin Saheeru mijin Salma e." Ta fada tana juya jiki. Ganin ya ciro wata dorina yana fadin , "au ba za ki daina din ba kenan ko?" Da gudu ta bude kofar office din ta fice tana, "ai ba karya nake fada ba bare ace ba kyau indaina." Ta wuce class abunta. Tsaki Saheer ya yi ya koma ya zauna. Lokacin tashi kuwa na yi da gudu ta koma office din tana fadin, "an tashi,ka zo mu tafi gida mi...." Kallon da ya bita da shi ne yasata yin shirun dole ta tsaya tana murmurguda baki tana wurgi da hannu. Keyn motarshi ya dauka yana, "daga yau ba tare zamuna zuwa ba da kafafunki zakina zuwa school dinnan kuma kar ma ki kara nuna kin sanni." Taɓe baki ta yi , "unm oho ohon maka dai." Ta bi bayanshi ta shige motar ta zauna. Da sauri ya janye motar ya bar School din domin bai son kowa ya fahimci tare suke. Aiko suna zuwa gidan ta baje a falo zata yi kuka, "yunwa nake ji ni wallahi,yunwa nake ji." Ji ya yi kamar bai san me take fadi ba ya wuce cikin daki ya shiga toilet. Ta bi bayanshi tana zuwa ta bankada toilet din ya tuɓe wando kenan zaiyi fitsari. Idonta idon jikinsa. Wata kara ta sake tana rufe baki da hannu. "Na shiga uku na mutu na lalace kai kuma naka abun macijine zabgege ashe." Sambatu ta fara barkate kuma tana tsaye ta kura masa ido taki tafiya. Cikin fushi ya tura kofar sai da ya buga mata goshi. Ta rike goshin tana tsaye agun, "mugu kawai mai maciji aradun Allah sai na rama ji zaka fasa mun goshi." Gaban mirror taje tana kallon goshinta. Kwafa ta yi ta ce, "kyakkyawa dani yana son ya cuceni ya bata mun fuska,zan yi maganinka ysn." Man shafawa ta dauka taje daidai tais din dake bakin toilet din inda yana fitowa zai fara takawa a hankali ta shafa man. Sai da ta tabbatar ta shafa yadda mutum na takawa santsi zai ja shi ya fadi kafin simi simi ta fice a dakin ta tsaya a bakin kofar tana leƙe.
Aiko yana fitowa da santsi ya ja shi ya yi wata irin sulewa sai ga kanshi a gefen gado ya bugu daram. Har cikin ranshi yaji wata irin azaba na ratsa shi yana sa hannunshi a goshi ya ji kamar an daura masa wani tulu. Salma mai zata yi ban da dariya harda rike ciki. Musamman da ya tashi ta ga goshin shi ya kumbura har tana birgima a kasa. "Wayyo ni da fatanya sunan wani abu, ji kai har wani sheƙi yake kamar naman akuya wayyo cikina,maganin mutum ai kenan in dai mutum ya ce shi mugu ne zai ga mugunta."
Saheer bai kulata ba har sai da ya kalli kanshi a madubi. Lokaci gudu yanayin kamaninsa har ya canja goshi ya kumbura sintim. Yana kallonta ta kara shekewa da dariya. Binta ya yi a guje ita ma ta fara gudu......
*Da dai na so in tsaya da free pages 8 Dinnan amman yanzu saura 2 pages zamu kai page 10 In sha Allah a hanzarta a gama payment masoyan asali nice matar Hedimastan ga fa ko kun daina kaunata ne ban sani ba? Inga ruwan alert mussaman Xh Narrative Nest members*😻😂
MATAR HEDIMASTA
500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank
Evidence of payment to *** [7/2, 12:57 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*