MATAR HEDIMASTA

PAGE-9

by @xayyeesherthulhumaerath

Haka suka dunga zagaye gidan daga ciki har waje, ko a jikinta ganin tana kokarin mai da shi karamin mahaukaci karfi da ya ya kyaleta yana numfarfashi ya koma daki. Kwanciya ya yi akan gado ban da haki babu abun da yake yi,ga azaban da goshin sa ke yi masa, ga shi kuma sai ƙulu yake karawa kamar wanda ake sawa yeast.

Ya rasa meke masa dadi,kwanciyar ma ya gagara,ya kwanta ya kifa kai, ya tashi ya juya yana kallon sama,ya koma gefe shi kadai dai yasan abun da yake ji ya rasa ina zai sa kanshi ya ji dadi.

A karshe wani barcin azaba ne ya dibesa ba tare da ya ankare ba. Ita kuwa Salma kitchen ta shiga dake ta iya kunna gas caraf ta kunna Tana, "mutum na jin yunwa baza a bashi abinci ba,dadinta ma ai nima na iya girkin yi zan inci in koshi abuna." Ruwa ta fara zubawa a tukunyar sannan ta dibo shinkafa ta ko aunawa batai ba ta zuba. Sauran man gyadan da ya dafa indomie da shi ta kwashe ta zuba a ciki. Sauran magin indomie dinma ta dauka tana, "bara muji wannaan kuma mene ne." Ta zuba a hannunta kafin ta lashe a baki, dariya ta fara tana, "aradun Allah dandanon girki ne, ji kamar madara madara." Ta juyeshi kaf a cikin shinkafar ta dauki ludayi ta juya,ta juya shi sosai kafin ta rufe ta fita falo tana, "umm kafin abincin ya yi bara inyi kallona ma." Bai fi minti daya ba taje ta kara dubawa ta diba ruwan ta dandana , "umm da saura gaskiya amman shinkafar nan zata yi dadi sosai." Ta kara rufewa kafin ta koma falon ta ci gaba da kallo. Tana cikin kallo barci ya sace ta. Abinci tun yana yi a hankali har ruwa ya tsotse ya fara konewa. Har hayaki da ƙauri ya fara karade kitchen din da falon tana ta sharban barcinta ko a jikinta. Saheer na barci kamar ance ya farka ya fara jiyo wani irin hayaƙi. Da sauri ya tashi aiko yana zuwa har kitchen din ma ya gama karadewa da hayaki ya cika fal.

Da sauri ya kashe gas din yana toshe hanci ban da tari babu abun da yake saboda ya riga ya shaƙi hayakin, Salma har lokacin bata san meke wakana ba barcinta take harda gwarti.

Sai da ya daidaici daidai duwawunta ya maka mata duka, a zubure ta farka ta zata fara masifa kuma da ta kalleshi ta kalli goshinsa bata san lokacin da ta fashe da wata irin makirar dariyar mugunta ba. Ƙara kula ya yi ya ce, "wai ke duk bayan mintuna shashancin naki karuwa yake? Ki daura abinci ki zo nan ki wage baki kina barci? Da yanzu kin ja mana gobara fa." Sai a lokacin ta tuna da da abincinta. "Innalillahi wayyo abincina." Ta fada tana wucewa ta gefensa ba tare da ta kula shi ba.

Tana zuwa ta sa hannu ta jefar da murfin tukunyar saboda zafi sannan tasa zaninta ta sauke tukunyar gabadaya ya kone yyi baki sai dan kadan a tsakiyan tukunyar da bazai wuce cokali goma ba. Bajewa ta yi a kasa kitchen din ta ja tukunyar gabanta tana kuka tana ci, "Ban da mugunta ace abar abincin mutum ya kone baza ana duba masa ba, wannan ai mugunta ne da son zuciya kuma aradun Allah sai na ci sai dai bakin ciki ya kashe mutum." Don takaici kasa kulata Saheer ya yi kawai ya zauna a falon ya yi tagumi.

Shima wata azababbiyar yunwa ya fara ji gashi bazai iya shiga kitchen din ya yi girki ba. Tashi ya yi kawai ya fice masallaci ya fara zuwa ya yi sallah sannan ya wuce 3D Resturent ya ci abinci har ya fito kuma sai ya koma ya yi takeaway ya sa a mota. Bai koma gidan ba har sai da dare ya yi. Yana komawa yaga gidan da dakin kaca-kaca har wani hamamin wari ne yake tashi. Ita kuwa tana zaune gaban tv tana kallo tana ta sheƙa dariya ko a jikinta. Har ya shigo bata sani ba sai da ya kashe tv kafin ta juya tana , " wani dan iskan ne ya kashe mun kallona." Tana rufe baki suna hada ido.

Ya ce , "Dan iska ko? Inaga dai duk ranar da na fasa miki bakin nan naki zaki setu ki rage rashin kunyar nan da fitsara kuma maza ki tashi ki gyara gidan nan tas domin ni ba dan aikin ki bane."

Bin falon da kallo ta fara yi kafin ta kalleshi, "ina za a gyara me ye ya faru a gidan?" Saheer ya ce, "kin makance ne? Na ce ko kin makance ne ko kazantar taki ce ta shahara?"

"Yoo shahara na nawa kuma? Ai ni sunana ma a kauye shahararriya salame." Salma ta fada tana murguda masa baki.

Kasa hakuri ya yi ya cire belt dinsa zai maka mata cikin Muryar sauri ta ce, "zan yi wallahi zan gyara." Ya nuna mata kitchen da hannu. To maza muje ki fara da nan sai kin wanke komai kuma kinyi moping. A kanta ya tsaya da belt din a hannunsa ya na yi mata direction yadda zata yi tana yi tana kuka. Domin ba saba aiki tayi ba ta wanke ya ce bai wanku ba ta sake wankewa a haka har ta gama wanke wanken. Mopping din kuwa da rarrafe ta karasa tana yi tana zufa. Tana gama gyara kitchen din ya ce su dawo falo ma ta gyara, nan ma haka ya tsaya sai da ta gyara shi tsaf. Don dole bakinta ya mutu ta kasa magana bare motsawa a inda ta zauna. Ganin dare ya yi takeaway din da ya tawo da shi ya bata. Aiko tana karba ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama ci ta baje agun sai barci. Saukar ruwa taji a fuskarta Saheer na fadin ta tashi taje tayi sallah. Tsaki tayi tana kokarin komawa. Ganin ya dauko belt ai tuni ta tashi aranta tana, "aradun Allah duk abun da ka mun yau sai na rama ai kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha."

Sai da yyi sallar isha kafin ya dawo gidan ya kunna TV tana zaune a gefe yana zama ita ma taje kusa da shi ta zauna. Tsawa ya dakata mata yana, "wani irin iskanci ne wannan? Dallah nemi wajenki ki zauna." Bata kula shi ba kuwa ta zauna a gefe tana kallonshi. Can anjima ta kalleshi sai sun hada ido sai tayi kwafa sai ta kawar da kai haka ta dinga yi har sai da ya kashe tvn yaje ya kwanta ita kam tana zaune. Lakashi tayi sai da ta tabbatar ya yi barci sannan ta jura farar jallabiyarsa a jikinta ta shafa farar hodo a fuskarta ta bude kanta gashinta kamar hamtar yan iska a tsattsaye. Wutar dakin ta kashe sai na falon kadam kadan dake haska dakin. Ta shiga dakin tana Wata irin ƙatuwar muryar tana kiran sunan shi, "SAHEERUUUUUU SAHEEERUUUU SAHEERRUU." Kamar a mafarki Saheer yaji yana kiran shi aiko yana bude ido me zai gani.....

*Gobe zamu gama free pages In sha Allah* 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank

Evidence of payment to *** [7/3, 9:53 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ****

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*