KURUCIYA

PAGE:9&10

by @xayyeesherthulhumaerath

Damƙo kanta ya yi yana fadin, "Beauty is all around you ba? Let's wait for the outcome inna aske wannan shirgin da har kike alfaharin nunawa, kazamiya kawai."

So take ta kwace kanta amman ta kasa cikin murya kuka ta ce, "Don't ever try to cut my hair, am telling you , leave me i said leave kar ka taɓa mun gashina kar ka taɓa."

Jan gashin ya yi ya fara guntulewa ba tare da ya saurareta ba, wata kara ta sake ta fisge kan ta tafi tana kuka, mirror ta fara zuwa ta duba ta ha ya fara aske mata bangare daya amman bai asku da yawa ba. Ta ja numfashi tana kallon fuskarta cikin madubi, "Ka mun sanadin idanuna,ka fasa mun baki gashi yanzu kana kokarin rabani da gashin kaina tsabar bakin ciki da hassada ba zan taba bari ka ci galabai akaina ba sai dai a komai mu tashi a daidai wannan askin kuwa kamar anyi an gama ma,wannan bakin halinka ma kadai ya kashe duk wata mai sonka wallahi anji jiki Black-black." Duk da kuka take amman share hawaye tayi ta dauko breast enlargement cream ta kara makawa a kirji ita ba za ta iya jira har sai dare ba gwanda tana shafawa lokaci bayan lokaci don ya yi sauri ya fito a wautarta.

Tattare gashin tayi da riboms sannan ta dau hula ta sa tana, "Mugu zan ga yadda zaka aske mun gashin ai."

Kamar an tsikareta ta fara jin alamar fitowar Abu a jikinta. Da gudu ta nufi toilet tana shiga ta ga Period ne, Mantawa ta yi ma da batun wai a toilet take ta fara tikar rawa tana fadin, "Ya tabbata dai girma ya zo ni Rusul Daman Ammie ta ce mun zai dawo yanzu duk wata zanna hutun sallah,Yes ko anki ko anso dai na zama big girl yan bakin ciki sai dai a mutu." Sai da ta tiƙi rawa son ranta sannan ta wanke jiki ta fito ta dauki Pad da Pant a hannu ta fice.

Dakin Majeed ta nufa, zaune yake ya tattara hankalinsa gabadaya kan waya yana game din ball.

Fara zagaye dakin ta yi taje ta dawo taje ta dawo ga Pant da Pad tana wasa da su a hannu. Jini sai diga yake duk inda ta bi, don irin masu zubar da jini sosai ne kuma wa inda basa ciwo sam a lokacin period sai dai suji zuwansa kawai.

Kamar ance ya dago ganin buruntun ya yi yawa idonsa ya fara tozali da jini kan tiles.

"What ? Idonki baya ganin abun da kike zubarwa ne ko tsabar kazantar taki ta shahara ne?" Ya karasa maganar yana tashi tsaye.

Cikin tsiwa ta ce, "abun da ka gani ne mana, Period nake so zuba yake kafin insa Pad din ai ban rike idonka nace dole sai ka kalla ba sai ka kautar da kai ai ehee Period dai sai wacce ta cika babbar mace take ,wasu ma in sun zama cikakkun mazan ko ya za a gane oho."

"Oh na gane ai kuwa yau zaki shanye jininki tas tunda ke baki da hankali kuma dakikancinki karuwa yake maimakon raguwa."

Tsaki ta masa ta ci gaba da kokarin sa Pad jikin Pant dinta.

Cak Majeed ya daga ta tana wutsitsil ya make ta sannan ya kwantar da ita a kasa tamkar ragon da ake kokarin yankawa ya bude mata baki ya bi kasa da ita duk inda ta zubar da jini saida yasa bakinta agun ta goge.

Yana gamawa ya direta kofar daki sannan ya turo kofarsa.

Amai ta fara ba kakkautawa take agun saida ta amayar da duk abun da ya shiga cikinta. Tana gama bakinta kuwa bai mutu ba ta ci gaba da fadin, "kai dai da bakin ciki zaka mutu wallahi girma ne nayi kuma ba a isa amaidani baya ba, karamin yaro kawai waya sani ma ko ni na baka Shekara ukun da ake cewa ka bani, in dai sunana Rusul Abdul-Aman Beer ba ka ci na banza ba."

Mai aiki ce tazo ta yi moping din wajen ita kuma taje ta canja kaya tasa pad din, dare ya fara nisa gashi barci yazo tana neman hanyar shiga ta kwanta amman ba dama, tsabar asalin mugunta ma kashe wutar dakin ya yi kuma ita bata son duhu ko kadan.

Kofar ta dunga Nocking kan ya bude mata ya yi tamkar bai ma san da batun ta ma, ga shi ba haske bare ta bi ta windown data saba.

Zama tayi kawai abakin kofar tana sharban kuka.

Aikuwa haka ta yi kwanan zaune a gun barci na daukanta take farkawa a razane ta ci gaba da kuka.

Sai da ya fito za shi masallaci ya ganta tsaki ya yi ya wuce ita ma ta bisa da tsaki, "Mtss fool-fool."

Ranar tunda ta shiga daki ba ta kara fitowa ba ko breakfast da Lunch ma kai mata ake teddies dinta ta jera tana wasa da shan Chocolates tana halkance dare na kara yi daidai lokacin da Majeed ya tafi sallah tuni ta shige dakin ta kwanta ta yi rikimo ido a rufe kamar ta yi barci. Sai da ya yi isha ya dawo bai lura da ita ba saboda ta shige cikin blanket irin mai jikin kuliyan nan mai kauri.

Ajiyar zuciya ya yi yana shirin kwanciya aransa dadi yake ji yau baiyi gamo da waccer mayyar yarinyar ba.

Kwanciya ya yi kawai yana jan bargo yaji an kankame.

Da karfi ya fisge yana, "Ya Allah na gode ke kam anya mutum ce kuwa? Don mutane na da zuciya amman ban da ke."

"Mutum ce mana,mutum ma kuwa farar fata ba bakin gawaye ba, da ace zan iya barci ni kadai kai ka isa ma ka ga kyallins ne bare ni dinma duka,ai ka godewa Allah Mtss." Ta fada tana juyawa abunta.

"Alright zan ga yadda zaki yi barci yau adakin nan kuwa."

Ya fada yana ficewa daga dakin.

Tsaki Rusul ta kara yi tana gyara kwanciya, "Can ta matse ma koma me zaka yi barci kam ba fashi anan zan yi mtsww."

Yana fita ya ci karo da tuzurun mage kuma yasan Rusul ta tsani Kuliya abu uku lizard,Jaɓa,mage wa innan abubuwan suna iya sawa ta fita a hayyacinta.

Aikuwa Murmushin mugunta ne ya bayyana a fuskarsa tuni ya damƙe tuzurun nan gashi katoto baki irin mai shiga gidajen mutane cikin daren nan ganinsa kadai abun razana ne.

Yana shiga ya jefa mata kanta,ba tare da ta bude ido ba ta ce, "aikin banza aikin wofi ka yi ka ga....

Kafin ta karasa ta ji sautin kukan Tuzuru akunnenta cikin sauri ta bude ido tana kokarin yaye bargo ta gudu.

Shi ko tuzurun ɗane mata kafada ya yi ya riketa gama, cikin firgici take fadin, "na shiga uku shikenan na mutu wallahi,na mutu,Mom big Daddy,ku zo na shiga uku."

Zuwa tayi ta kankame Majeed cikin sanyayyar murya tana, "Don Allah ka cire mun Don Allah ka cire mun wallahi mutuwa zan yi na shiga uku."

Hankadeta ya fara yi yana dariyar mugunta. Numfashinta ya fara kokarin daukewa tun tana kokarin kawar da Magen har ta gagara gashi ban da kuka ba abun da tuzurun keyi irin gigitaccen kukan nan yana kara kankame mata jiki.

Wani irin riko ta kara yiwa Majeed nan take ta suma.

"Mtss Ashe karyar rashin kunya kike dalla sakeni kazamiyar banza."

Ya fada yana kara hankadeta.

Ji ya yi gabadaya jikinta a sake ya yi tsaki ya janyo bottle watern da ke gefen bedside dinsa ya bude ya watsa mata irin watsawan wulakancin nan amman ko alamar motsi babu ya kara sakin tsaki , "Mtsw Allah sa ma a wuce can lahirar daga nan."

Duk yadda zaiyi da ya cireta a jikinsa ya kasa.

Kamar wasa har karfe biyun dare ba alamar motsi Rusul bata farka ba kuma ba alamar farkawa.

Tun Majeed bai damu ba har ya fara shiga damuwa a zuciyar sa yake saƙa yadda zai kasance in Ammie da Small Dady suka ji labarin shi ya yi sanadin Rusul.

Zufa ce ta fara keto masa ta ko ina idanu suka kara fitowa fili gashi sunyi jajir tamkar dan kwaya.

Jijjigata yake amman sam ta gagara motsawa yadda take dai haka take.

Har gari ya waye suna zaune tana kankame a jikinsa kawai ya zura mata ido yana kallo yama rasa abun cewa duk ya fita a hayyacinsa.

Ji ya yi kawai an turo kofa,Mom, Ammie, big Daddy da Small Dady ne tsaye gabansa..... [26/07, 1:37 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *ƘURUCIYA* ♥️

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*

Bismillahir-Rahmanir-Rahim