BARRISTER SUHAIL

74

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----74


daren ranar haka iman ta kulle kanta a daki har lokacin bata kula kowa ba 

washe gari 

tun da safe Mubarak ya kamo hanyar kaduna 

karfe takwas na safe ya iso gida hafsat na tsakar gida tana shara 

Ammi kuma na Kitchen,tana haɗa abin kari 

da sallama ya shigo 

hafsat ta amsa cike da fara'a "sannu da zuwa yaya Mubarak"

jin an kira Sunan Mubarak ammi ta fito

"Mubarak har ka iso kenan"

murmushi yayi ya ce"Ammi ina kwana"

"lafiya qlau Mubarak,ya hanya" 

"Alhamdullilah, Ammi ina iman din"

nuni tayi masa da Dakin ta ta ce"tana ciki"

Ya tarar ƙofar a rufe Ya buga sau da dama amma ba ta buɗe ba Sai da Ammi ta kira ta ta ce Mubarak ne ya zo, sannan ta buɗe masa ƙofar a hankali Ya shiga ciki 

iman na zaune a gefen gado ta rungume ƙafafuwan ta tana kallon ƙasa

Idanunta sun kumbura, fuskarta kuma ta rame fiye da yadda ya santa
Ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu
Zuciyarsa ta yi zafi

waje ya samu gefe guda ya zauna ta yadda zai fuskance ta 

ɗago idanunta tayi ta kallesa
 cikin Muryar ta da ta soma disashe wa ta ce"yaya Mubarak ina kwana"

bai amsa taba ya ce"iman mike damunki jiya Ammi ta kira ni ta faɗa min duk Abinda ke faruwa"

"matukar kin dauke ni a matsayin babban yayanki"

Nan take hawayenta suka sake zubo.

Amma har yanzu bakin ta ya ƙi buɗewa

Mubarak ya yi shiru na wasu sakanni

"iman ki sani bazan tilas taki kiyi magana ba kamar yadda bazan hana malan ya kira mijinki ya tafi dake ba"

jin hakan tayi saurin dago jajayen idanunta ta kalle shi 

"yaya Mubarak,dan Allah ka taimakeni"

"Khadija ta ina zan fara taimakon ki bayan bansan abinda ke damunki ba"

“Amma ki sani, duk abin da yake damunki ba ke kaɗai za ki ɗauka ba dole ki sanarwa wani ko zai iya taimakon ki

"Kina da ni"

“Kina da Hafsat"

“Kina da Ammi"

“Kina da Malam"

Kalaman nasa suka ƙara karya mata zuciya

Ta fashe da kuka

Sai dai har yanzu ta ƙi faɗin komai

Mubarak ya share mata hawaye da gefen tafin hannunsa

"iman Suhail sakin ki yayi ne kika ƙasa fadawa kowa"

kai ta Girgiza masa ta ce"a'a"

cikin fushi ya miƙe ya ce"iman bazan lamin ci wannan sakarcin ba, idan bazaki fada ba ni da kaina zan kira Suhail yazo ya dauke ki"

ganin yana shirin fita ta riƙe bayan rigar sa cikin kuka ta ce"yaya zan fada maka"

dawo yayi ya zauna ransa a hade ya ce"ina jinki"

cikin shasshekar kuka ta ce"yaya Suhail baya sona,tun da muka je asibiti likitoci suka tabbatar da bana haihuwa, komai ya chanza,duk da bai fadi da baki ba amman ya nuna a aikace"

"kamar ya ,chanza"

shine yanzu dan matar sa ta samu ciki ya fara juya min baya har matarsa ta fara kirana da juya"

kuma tana min gorin ce wa"ai ba Suhail bane ya gani ya ce yana sona"

"yaya Mubarak ka taimaka min Ni wallahi bana so in koma idan kuma so kuke a kawo gawata ku matsamin sai na koma gidan sa"

ajiyar zuciya ya sauke tare da fitar da wani hucci mai zafi

tun farko Abinda ya hango tun farkon auren iman da Suhail yasan tabbas wata rana za'ayi mata gori 

gashi kuma tun ba'a je ko ina ba matar tayi mata gori amman abu ɗaya yafi tsaya masa a rai maganar rashin haihuwa


kallon ta yayi ya ce"iman wanene ya ce baki haihuwa"

share hawayen tayi ta ce"Asibiti muka je da aunty Zarah anan suka faɗa mana"

dafa kafardar ta tayi ta ce"aure, haihuwa da mutuwa gaba dayan abu ne na Allah koda likitocin Duniya suka tabbatar da bazaki haihu ba idan Allah yaso zaki haihu dan haka ki cire wannan tunanin a Ranki"

"babu wanda ya isa yayi miki abinda Allah bai maki ba"

"ki kwantar da hankali ki bar kome a hannu na"

sai lokacin ta dan ji sanyi a zuciyar ta 

Mubarak ya miƙe zai fita"bari na sami Malan din muyi magana"

Mubarak ya fito daga ɗakin Iman zuciyarsa cike da damuwa

Ko wajen Ammi bai tsaya ba

Kai tsaye ɗakin Malam ya nufa

Ya same shi zaune kan kujera yana jan carbi 

Da sallama ya shiga

malan yayi masa nuni da kujera ya zauna

dan tun zuwan sa suka da malan a kofar gida kuma ya faɗa masa dalilin zuwan sa

Ya zauna, amma fuskarsa ta nuna akwai abin da yake damunsa

Malam ya kalle shi ya ce

“To, ta gaya maka abin da ya sa ta ce bazata koma ba"

Ajiyar zuciya ya sauke

“Eh Abba"

“Meye dalilin"

Cikin nutsuwa ya ce"


“Abba… tun bayan da suka je asibiti aka fada musu wai Iman ba za ta iya haihuwa ba, tun daga lokacin take ganin Suhail ya canza mata"

Ya ɗan dakata kafin ya ci gaba

“Kuma yanzu da matar Suhail ta samu ciki, tana yi mata gori Wannan ne ya sa take tsoron komawa"

malan ya jima yana kallon Mubarak

ya ajiye charbin hannunsa

"Mubarak"

"na'am malan"

"ka bani mamaki ina hankalin da tunanin ka suka tafi"

Mubarak ya sanda kansa ƙasa

“Wannan dalilin marar tushe ne har za ku biye mata?”

"in an ce ba za ta haihu ba, shi ya sa za ta ce ba za ta koma gidan mijinta ba"

Mubarak ya yi ƙoƙarin yin magana

“Amma Abba…”

Malam ya ɗaga hannu ya dakatar da shi

“kamin shiru Mubarak"

"idan har kaga iman ta cigaba da zama a gidan cikin ɗayan biyu kodai Suhail ya ƙoreta ko kuma ya ce ya sake ta"

"wannan dalilin ne kawai zai sa ta cigaba da zama a gidan nan"

Muryarsa ta ƙara ɗan ƙarfi

“Wannan ba Aikin hankali ba ne"

“Wallahi ba zan yarda da wannan ba"

Mubarak ya ce cikin ladabi

"Allah ya huci zuciyar ka Abba"

Malan ya ce

“Yanzu ma zan kira Suhail.”
“Ya zo ya tafi da matarsa.”
Mubarak ya yi saurin cewa

“Abba, kafin ka kirasa ko ba za mu sake magana da ita ba?”

Malam ya ce

“Ba wata magana da za a sake"

"Matar aure ce kuma gidan ta zata koma"

Mubarak ya yi shiru

Ya fahimci babu abin da zai ce da zai canja ra’ayin Malam

A hankali ya miƙe tsaye

“Abba za koma"

"Allah tsare hanya" malann ya faɗa

Ya juya ya fita

Kai tsaye ɗakin Iman ya koma

Har yanzu tana zaune inda ya barta

ta na gannin shi, ta miƙe cikin sauri
“Yaya…”

Kallon ta ya yi cike da tausayawa.
A hankali ya ce

“Na yi magana da Malam"

Fuskarta ta dan sauya
“Me ya ce?”

Ya sauke numfashi

“Bai yarda da dalilinki ba"

“Ya ce wannan ba hujja ba ce"

"Kuma…”
Ya ɗan yi shiru
"ya ce zai kira Suhail ya zo ya tafi da ke"
Nan take idanun Iman suka cika da hawaye
Ta koma ta zauna a bakin gado
Hawaye suka fara zuba ba tare da ta iya tsayar da su ba
Mubarak ya ji zuciyarsa ta yi nauyi

Ya san ƙanwarsa tana cikin wani hali da ba kowa zai fahimta ba

Amma ya kasa yin komai

A hankali ya ce
“Ki yi haƙuri"

"Allah ya kawo maki mafita,zan taya ki da addu'a idan akwai Alkairi a zaman ku Allah ya barku tare idan babu Allah ya kawo dalilin da Suhail da kansa zai sake ki"

bai jira amsar taba 

ya juya yayi fitar sa ba tare da yayi wa kowa sallama ba 

ya kama Hanyar Kano