79
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----79
Naima da Meerah suka kalli juna
Babu wacce ta ce komai
Jennifer kuwa ta na tsaya riƙe da akwatin da ke hannunta, ta kasa motsi
naima ta wa meerah "sai suwa za'a kai boys quarters,ko dai zeenah batan Matsayin mu bane a gidan"
meerah ta ce"ba wani nan ta sani zabagen iskanci kawai da Rashin mutunci ni gaskiya bazan iya jurar rashin mutuncin nan ba tashi zanyi na tafi"
Naima ta ce"haba meerah,idan kika tafi yau Mami zatayi tunanin akwai matsala tunda already mun fada mata kwana biyu zamuyi amman daga gobe nima bazan ƙara kwana ba in yaso idan ta tambaya sai mu nata wani excuse din
Suhail na barin dakin zeenah ya nufi wajen iman ya faɗa mata da zuwan su Naima
sannin ba lallai suzo inda take ba yasa ta dauki hijabin ta dora kan rigar jikin ta ta nufi falon
sunan nan zaune kowa yayi ragam babu mai wata walwala a cikin su
iman ta shigo ciki dauke da sallama a bakin ta
Naima ta amsa
meerah ko ta juya kanta gefe tunda take magana bata taɓa hana ta da iman ba har yanzu tana kishin ta akan auren Suhail da tayi
waje ta samu ta zauna cikin natsuwa
ta ce"ina yinin ku, ya hanya
Naima ta amsa da "lafiya" shine kawai amsar da iman ta samu
ta zauna kusan minti goma babu wanda ya kulata haka ta karaci zaman ta tashi
meerah ta bita da harara har ta ɓace wa ganin ta kafin ta ja Wani dogon tsaki a ranta ta ce"ko ina yaya Suhail ina wannan yarinyar marar class,komai ma zata nuna min oho"
jin tsakin da taja naima ta ce"ke lafiyar ki kuwa"
yatsine fuskar tayi ta ce"babu"
iman na fita ta koma dakin ta tayi kwanciyar akan gado ta cigaba da ɗan na wayar ta
Suhail ya fito daga dakin sa ganin su Naima da meerah na zaune yadda ya barsu
ya ƙarasa kusa dasu ya tambaye su ko an kawo masu wani abu
Naima ta ce"yaya wallahi ko ruwa bata bamu ba"
jennifer ya kira ya tambaye miyasa bata basu abinci ba
ƙasa tayi da kai ta ce"sir,daman inaso na gama kai kayan su boys quarters sai na kai masu Abinda zasu ci"
cikin mamaki ya ce"Kayan wa kika kai chan"
nuni tayi masu da su Naima ta ce"oga Hajiya ta ce na kai su chan"
ba tare daya kara magana ya nufi dakin zeenah
tana zaune bakin gado tana duba Dinkin sunan da tailor ya kawo mata
bakin gadon ya ƙarasa ya ce"ke kika ce akwai su Naima boy quarters"
"Eh" kawai shine Abinda ta ce ba tare data kalle shi ba
"ko zaki iya fada min Dalilin nayin haka"
"Kana so su zauna a cikin gida ne alhali akwai boys quarters da aka tanada domin baƙi? Ai ba wani suka fi ba idan sun ga da taƙura they can park their belongings an leave"
kai ya girgiza ya fita
“Rashin mutuncin Zeenah yana ƙara bayyana a gidan kullum Yanzu ba Suhail kaɗai abin ya shafa ba, har ya fara taɓa iyalansa"
yana fitowa ya dawo wajen su ya ce"ku tashi in kai ki dakin iman dan nasan ita baza taɓa wulakan taku ba"
Naima ta kalli meerah sun tuno yadda suka amsa mata gaisuwar da kuma tsanar da suke nuna mata na babu gaira babu dalili
meerah ta ce"Naima kina ganin zata amshe mu kuwa"
naima ta ce"koma minene da in kwana a boy quarters gara na je chan din ko zata kwana tana dukana"
duk abinda suke fada Suhail baya jin su
ya dubi jennifer ya ce"ta dauko kayan su ta kai masu dakin iman"
Suhail na gaba suna biye dashi har suka karasa dakin iman
a falo suka zauna ya shiga ciki
ya fada mata gasu Naima nan zasu kwana a part din ta
"okay, yaya Suhail"
tare suka fito falon shi ya fice ita kuma ta zauna wajen su
a'lamun su data gani kamar basu ci komai ba
ta nufi Kitchen ta hado tray guda mai dauke da snacks da drinks ta ajiye a gaban
daga Naima har meerah mutuwar zaune suka yi kowa ya ƙasa cewa komi
bayan ta ajiye masu ta ce"ku ci wannan kafin na girka maku abinda zaku ci"
Naima ta jinjina kai
ta sake duban su ta ce"ko Akwai Abinda kuke so ku ci"
kan ta rufe baki meerah ta ce"ni fatan doya zanci"
murmushi iman tayi ta ce"ba damuwa"
meerah ta fadi hakan ne domin kawai ta walahar da ita
iman na fita meerah tabi ta da kallo
cikin kasa sa awa guda ta kawo musu Abincin
wani eromatic kamshin ke fita daga cikin kular wanda ya ka rade Gaba ɗaya falon
meerah ko kamar jira take a ajiye abincin
dandan ta cika plate ta hau ci
haka Naima duk da ba sosai ta fiye cin abinci a wannan lokacin ba taji bazata iya haƙura bata dan dana wannan faten doyar ba
iman na ajiye musu ta shiga ciki dan basu damar da zasu sake
Naima ta ji kunya fiye da da
Ta tuna sau nawa take yi wa Iman baƙar magana har da lokacin datayi ƙoƙarin bugeta a gidan mami
Amman yau
Ita ce ta fara tambayar ko sun ci abinci ba zeenah ba da domin tane suke anan
Ita ce ta ba su wajen kwana ba zeenah ba da duka dauki son Duniya suka dora mata saboda kawai ta fito daga gidan masu kudi
yau gashi ƴar Malan din da duka ɗorawa karan tsana ita ce ta amshe da mutunci
koda dare yayi Iman ta basu bedroom ta suka kwana ita kuma ta koma dakin Suhail
washegari
tunda safe iman ta soma hada masu abin kari mai rai da lafiya
bayan sunci sun gama suka fara shirin komawa kaduna
iman na zaune a falo suka fito da jikkunan su
babu wanda ya kalleta bare suyi mata sallama
haka suka kuma dakin zeeenah suka yi mata sallama basu samu amsawar arziki daga wajen taba duk da hakan kuma basu damu ba
driver yazo suka kama Hanyar kaduna kowa da Abinda yake saƙawa a ransa