81
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—–81
A ƙofar gidan su Suhail ya yi parking
Shi ne ya fara fitowa
Ya amshi Ibrahim Khalil daga hannun Zeenah, domin ya lura da irin matsattsun kayan da ta saka, kuma ya san ba za ta iya riƙe jaririn cikin sauƙi ba
A haka suka nufi cikin gidan
Baba Haladu, mai gadi, ya yi saurin miƙewa.
“Barka da zuwa Yallabai.”
“Yauwa Baba Haladu.”
Ya amsa yana murmushi.
Kai tsaye suka nufi part ɗin Mami.
Tana zaune a falo
Da ta hango su, ta yi ƙoƙarin miƙewa zaune
Sai dai da ƙyar ta iya tashi, ta jingina da gefen kujera
Ƙafarta ta kumbura sosai
ta yi suntum tamkar za ta fashe
Da sauri Suhail ya ƙarasa gabanta
“sannu mami"
murmushi tayi masa
Ya durƙusa kusa da ita
Idanunsa suka sauka kan ƙafarta
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu
Kowace rana yana ganin kumburin na ƙaruwa duk da magungunan da take sha amman babu wani progress da ake samu
A hankali ya taɓa gefen ƙafarta
“Mami… har yanzu tana miki zafi?”
Ta yi murmushi tana ɓoye ciwon da take ji
“Ba wani abu ba ne Suhail zan ji sauki"
Ya girgiza kai
“A’a Mami, wannan ba ƙaramin abu ba ne ya kamata a san abin yi"
“Na ga kumburin ya ƙara yawa"
Ta ɗora hannunta a kansa.
“Kada ka damu "
Suhail ya sauke ajiyar zuciya.
“Amma Mami ya kamata munsake zuwa asibiti a duba kafar nan"
“Ko da za mu je wani wajen daban"
shiru mami tayi duk wani zance daya danganci asibiti bata san sa gudun kar suce zasu cire mata ƙafa
A lokacin ne idanunta suka sauka kan Khalil dake hannun mahaifinsa
Nan take fuskarta ta sake ta sa hannu ta karɓe sa
Iman ce ta fara gaishe ta Mami ta amsa cikin nutsuwa, amma hankalinta gaba ɗaya yana kan Khalil da ke hannunta
kafin zeenah dake gaishe ta cike da gadara
mami ta washe mata baƙi "kun sha hanya ai daya faɗa min zaku zo da na shirya maku tarba ta musamman"
A wannan lokacin Iman ta ji kamar ba ta cikin falon Duk hirar Mami ta koma kan Khalil da Zeenah, ita kuma ta zauna cikin nutsuwarta ba tare da ta nuna komai ba
koda aka tashi tambayar mi za'a kawo masu zeenah aka tambaya daya ke tafi Mami iya bariki ta ce"a koshe take"
take gwiwowin ta suka yi sanyi
suhail nan Barsu ya fita valcony domin yin waya da wani abokin ƙaratun sa wato dr Nasir wanda ya ƙaranci bangaren ƙashi wato othopedic
bayan sun Gaisa ya fada masa cewa mahaifiyar sa ce ke fama da ciwon ƙafa shekaru masu dama Wanda ya kai ga yanzu ko tafiya bata iya yi
dr Nasir ya ce"Subuhanallahi,Allah ya bata lafiya sai yanzu ina india amman next week zan shigo Abuja,in yaso sai ka kawo ta nan asibitin mu a dubata"
cike da gamsuwa suhail ya ce"to dr Nasir Nagode sossai"
bayan sunyi sallama ya kashe wayar ya koma ciki
koda ya zauna yake fada wa Mami tare zasu tafi Abuja gobe sati mai zuwa akwai likitan ƙashi da zaizo daga India zai dubata ta
badan hankalin ta ya kwanta ba ta amsa masa da "To Allah ya kaimu"
part din Abba ya nufa ganin motar Sa parking space ya tabbatar masa da yana ciki
bayan sun gaisa ya ke faɗa masa zai tafi da mami zuwa Abuja domin a duba lafiyar ƙafar ta
ajiyar zuciya Abba ya sauke yafi kowa sanin halin matar sa laila yana gudun kar ta zauna a gidan Suhail tazo ta hada masa abinda ba shi kenan ba
karfin hali yayi ya ce"Suhail kana Ganin zaman laila tare da ku ba wata Matsala"
murmushi Suhail yayi ya ce"in sha Allah babu wata matsala Abba"
"to shikenan,Allah ya bada sa'a ya kuma bata lafiya Kai kuma Allah yayi maka albarka"
Suhail ya Amsa da amin
ya tashi ya tafi har ya fita Abba bai sauke idanun sa daga kanshi ba
abubuwa da yawa ke masa yawo a kai dan ganen da zaman da laila zatayi a gidan sa ƙasa fada masa matsalar dake hango wa yayi
dan ransa bazai mai daɗi ba kar yaga kullum kamar yana yi wa mahaifiyarsa mummunan Zato
Wanda a zahiri ba hala bane
yafi kowa sanin halin laila tun kafin a haifesa yasan Abinda zata aikata da Wanda bazata aika ba
Amman koma minene yana musu fatan Alkairi
a daren ranar suhail ya sa mai aikin mami ta haɗa mata kayan ta da duk zatayi amfani dasu ,aka shirya mata komai cikin trolley
Zeenah kadai aka ba wajen kwana tare da yaron ta
ganin haka Suhail ya cewa iman su tafi dakin sa ta kwana a chan
washe gari aka soma shirye-shirye tafiya Abuja Abba ya zo har Dakin mami yayi mata sallama
aunty Fauziya duk da magana ke hadasu ba tayi mata sallama tare da fatan samun sauki
Suhail ya kawo matarsa a kofar dakin da taimakon shi da Abba suka sakata cikin motar
iman ta raɓe a gefen ta zeenah da Khalil suka zauna seat din gaba
karfe goma suka isa garin Abuja
a hankali motar ta isa harabar gidan
Suhail ya buɗe wa mami kofa
da kyar take taka kafar
iman ta ɗaukar masu trolley din
zeenah kuwa
kai tsaye ta nufi cikin gidan ba tare da ta waiwaya kowa ba
Suhail ya lura sai dai ya share abin a ransa
a wannan lokacin lafiyar mami ce a gabansa
koda suka shiga falon Suhail ya zaunar da Mami kan kujera
ya kallli jennifer ya sanar da ita ta gyara dayan part din chan Mami zata zauna
cikin ƙanƙanin lokaci jennifer ta gyara dakin ta shiya komai yadda ya kamata
aka maida mami chan bayan Suhail ya tabbatar da an saka mafa duk wani abun da zsta buƙata
bayan ya dawo daga sallar la'asar ya tara matan sa Gaba ɗaya
ya dubi zeenah ya ce" kece zaki kula da abincin da mami zata ci, Saboda ciwon sugar dinta bazata ci Abinci daidai da namu ba"
ya juya kan iman ya ce"ke kuma zaki kula da gyaran dakin ta"
zeenah ta ce"wannan ai san kai ne miyasa ni zaka dora min girki, Wanda ko a gidan nan ma jennifer ke girka mana kuma kafi kowa sanin wahalar dafa abinci masu diabeties dan haka ni ban dauka ba sai dai ka sama mata kuku"
Suhail ya ce"Zeeenah zaki fi lu'a da mami fiye da iman tunda kin fita shekaru"
zeenah ta ce"wallahi tunda har ta iya kwana da miji ya zama dole ta dauki dawainiyar uwarsa ka barni da renon Khalil ya isheni ba sai an hadamin da na wata katuwa ba"
wannan karin ba Suhail ba hatta iman sai da ta daga kai ta kalli zeenah yanzu uwar mijin take kira da ƙatuwar
anan ta tashi ta barsu ta koma ciki
iman ta ce"zan iya duka aikin"
Suhail ya juyo ya kalleta kin tabbatar zaki iya ko dai na samo yar aiki sai ta taimaka maki
kai ta Girgiza masa ta ce"ba sai ka samo ba mami tamkar Ammi nake kallon ta"
Suhail ya ci gaba da kallon Iman na wasu daƙiƙu
Wani irin natsuwa da tausayi suka cika zuciyarsa.
Ya san ba don ya umurce ta ba ne ta faɗi hakan
Halinta ne
A hankali ya ce
“Allah Ya saka miki da alkhairi"
Ta yi murmushi
“Amin"
a ranar suhail ya fita yayi wa mami cefanan kayan abinci ta
Suhail ya zaunar da iman ya nuna mata komai da yadda zatayi amfani dasu
Tun daga wannan ranar…
Iman ta fara kula da Mami kamar yadda take kula da mahaifiyarta.
Da sassafe take shiga ɗakinta ta gaishe ta ta kuma tambaye ta abinda take so ta girka mata
haka take wuni bauta mata duk da hakan ba godi bare na gode
sai Complain ma kullum da take yi Abincin ba maggi ko gishiri yayi yawa
duk da hakan ran iman baya ɓaci tayi mata uzuri akan rikicin tsufa ne kawai kuma zatayi ƙoƙarin su rabu lafiya
zeeenah ko sai tayi kwana biyu bata leka dakin taba ko ta aika a kawo Khalil sai taƙiya ko ta ce yana bacci
ita kuma kawai kyarmar mamin take yi bata son danta na zuwa inda take
bayan zagayowar sati Suhail ya kaita Asibiti wajen dr nasir aka gudanar da duk wasu gwaje gwaje
duk wani gwaji da aka mata abu daya ke nuna wa duk wasu jijiyoyin kafar sun daina aiki
masalaha ɗaya ce kawai a yanke kafar Gaba ɗaya idan ba haka ita da kanta zata fashe
jin haka yasa mami ta amince da a cire kafar
kwananta ukku a asibitin aka cire kafar duk wannan kwanakin datayi zeenah bata jeba iman kuwa tayi zuwa kadan take sau biyu a rana
dangi na kusa duk sunzo dibata harda aunty Zarah ma da mijinta
kudi masu yawa Suhail ke kashe a asibitin
bayan kwana biyu aka sallamesu
bayan ya fadawa iman duk abinda ya kamata a rinka tana ci banda yaji,zagi da kuma tsami
dan a iya dan zaman da sukayi a asibitin ya kula da hankali ta ya kuma lura da Yadda take tsaye kan mami da kula da abincin ta
kwana biyu da dawowar su zeenah ta shiga ta dubata daidai lokacin iman na fita zeeenah ta shigo take ta kai mata wata irin bangaza sauran kadan ta fadi ƙasa
ta ture ta ta shiga duk abinda ya faru akan idon mami ta ce"ke zeenah banda abinki ina ke ina haɗa ƙafada da juya talakka ko so kike ki gogi talauci ci"
iman ta juya ta kalli mami cike da jin zafin maganganun ta
hawaye masu zafi ke sauko mata kan fuskar ta
ta rasa tsanar da Mami tayi mata duk yadda take ƙoƙarin ganin ta faranta mata amman abin ya gagara
tashi tayi da kyar ta fita har wani jiri take jin yana neman kaita ƙasa
zeenah ko ko minti biyu batayi ba ta fita
iman na koma dakin ta take taji wani zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ga wani irin ciwo kai da bata taɓa jin Irin saba
har karkarwa take kwanciya tayi a kan gado ta rufe jikin da duvet
har Magariba kafin taji ya dan sauka tatashi tayi sallar
ta fita Kitchen dora girkin mami na dare
a kyar ta iya dafa abincin ta kai mata tana zaune a falo tana kallo ta shiga
ko sallama batayi ta ajiye tray ta fita har Yanzu bata manta abinda tayi mata da rana ba
Mami ta janyo Abincin zata fara ci lomar farko ta furzar da abincin
"ke yar malan" ta kira Iman da har ta kai bakin kofa
"ni zaki cikawa yaji a abincin wato so kike kiga bayana ko"
cikin dakiyyar murya iman ta ce"sai ki ajiye idan bazaki ciba ko ki kira mai haihuwa yar masu arziki ta dafa maki wanda kike so"
mami ta zaro ido karin farko da iman ta fada magana makammanciyar wannan
"ke ni kike fadawa wannan Maganar"
Suhail ya shigo dakin ganin sa mami tayi ta fashe da kuka
Suhail da sauri ya ƙarasa wajen ta mami lafiya miya same ki
ya tambayi iman dake tsaye "miya same ta"
"nima ban sani ba,ai gatanan a gaban ka sai ka tambaye ta"
cikin kuka mami ta ce"kaji ko Suhail matar ce kawo min Abinci nace mata yayi yaji shine ta hau zagi ma ta uwa ta uba wai idan banzan ciba in ajiye har ta kirani da tsohuwar banza ,ni kaidai nasan mi nagani tun farko a wajen Yarinyar nan shiyasa na tsane ta"
baki iman ta rike tana mamakin kalaman mami wai ta zage ta
Suhail ko bai yarda badan ko wani bai ce iman zata iya zaga ba bare mami
Suhail ya ce"mami gaskiya badai iman ba"
wani sabon kukan ta fashe dashi ta ce"shikenan yar malan ta asir cemin yarona"
kuka take tana ihu tana fadin"zata haɗa kayan tabbar masa gidan sa
duk lallashin duniya babu wanda Suhail bai mata ba
ta bari idan an gama mata dressing sai ya mai data ta ce"ina ruwan sa idan ma kafar zata ruɓe ai tata ce"
da kyar Suhail ya shawo kanta ta ce"zata haƙura,Amman sai dai ya zaba ko ita ko yar Malan"
gaban ya fadi ya ce"mami me kike nufi"
"ina nufin ka sake ta ta kama gabanta tunda ba haihuwa take ba"
Suhail idanun sun kada zufa ke keto masa ta ko ina
"mami kiyi haƙuri bazan iya sakin taba tunda ba Abinda tamin"
a fausace mami ta ce"idan har baka saki wannan yarinyar ba ban yafe maka ba"
jin maganar yake Tamkar saukar ara du
gangar jikinsa ta daina aiki na dan lokaci ƙwaƙwalwar sa ta tsaya cak
numfashi ke ƙoƙarin kwashe masa
ya kafe mami da ido
ganin ta yake tamkar wani dodo a gaban sa
iman ma haka jin furucin Mami take Tamkar an buga mata guduma
a watannin baya zata ce tana son Suhail ya sauwake mata amman a yanzu
kalmar tayi mata nauyi a zuciya , Idanun ta sun kafe kaf
da sauri ta dawo gaban suhail ta ce"na roƙe ka bi umarnin mahaifiyarka ka sake ni"
"kona huta da baƙin cikin da kuma gorin dake min nida iyayena"
"yaya Suhail ja gaji da zama da kai, Mahaifiyar bata kauna ta haka ma dangin ka aunty Zarah da Abba kadai suke sona"
"ka sake ni na koma wajen talakkawan iyayena na Domin nasan su ba zasu min gori na kuma suna kaunata fiye da komai a duniya na gwanmace na koma wajen su koda kuwa zamu kwana bamu ci komai ba"
Suhail ya dube ta hawaye kw sauko daga idanun sa karin Farko data gan shi yana kuka tun bayan auren su
"yaya Suhail ka sake ni na tafi"
bakin sa na rawa ya ce"Iman na .... Maganar ta ƙasa fitowa"
Hawaye suka ci gaba da zuba daga idanun Suhail.
Ya kasa magana.
Ya kalli Mami.
Ya sake kallon Iman.
Ji yake kamar zuciyarsa za ta rabu gida biyu.
Muryarsa na rawa ya ce,
“Mami… don Allah kar ki saka ni cikin wannan jarabawar.”
Mami ta ce,
“Zaka yi ne… ko sai na kai ga tsine maka?”
Wani irin shiru ya rufe falon.
Iman ta share hawayenta.
Ta matso gabansa.
Cikin sanyin murya ta ce,
“Yaya Suhail… kada ka sa mahaifiyarka ta yi fushi da kai saboda ni.”
“Idan tafiyata ce za ta dawo mata da farin ciki… zan karɓa.”
“Allah Shi ne shaida… ban taɓa nadamar aurenka ba.”
“Amma idan rabuwarmu ce za ta sa ka samu yardar mahaifiyarka… ka yi abin da ya dace.”
Suhail ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro.
Ya buɗe baki cikin rawar murya.
“Iman… na sa…”
Kalmar ta makale masa a maƙoshi.
Ya yi wani irin nishi mai ƙarfi.
Idanunsa suka juya.
Gangar jikinsa ta yi sanyi.
Cak!
Ya faɗi ƙasa sumamme…
Ba tare da ya iya ƙarasa kalmar da yake son furtawa ba
wallahi da hawaye na ƙara sa wannan page din Allah ya raba mu da ƙaddarar uwar miji
like
share
and comment