BARRISTER SUHAIL

95

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—95

Shiru ya mamaye falon

Kowa ya mayar da hankalinsa kan Suhail

Idanunsa suka cika da hawaye

A hankali 

Ya dubi Malam, sannan ya dubi Abba

Daga ƙarshe idanunsa suka tsaya kan Iman

Muryarsa na rawa ya ce

“Abba ina santa"

“Ba zan sake Iman ba"

Ya haɗiye wani irin ƙwallo da ya tsaya masa a maƙoshi

“Allah kaɗai Ya san irin wahalar da na sha tun ranar da ta bar gidana"

“Na rasa kwanciyar hankali"

“Na rasa farin cikina"

“Na rasa komai"

Ya share hawayen da suka gangaro masa

“Da ace na san kalmar da zan furta za ta raba ni da ita"

“Wallahi da ban taɓa buɗe bakina ba"

Ya juya ya kalli Malam

“Malam"

“Na yi kuskure"

“Na zalunce ta"

“Na kasa kare amanar da kuka ba ni"

“Amma wallahi har yau"

“Ba wata mace da take cikin zuciyata sai Iman"

ya durƙusa a gaban Malam.

“Don Allah"

“Ka taimaka mini"

“Kada ka raba ni da ita"

Hawaye suka cika idanun Malam

Abba ma ya juya gefe yana goge nasa hawayen

kowa ya tausaya masa banda Ammi

Malam ya dubi Iman

“Khadija"

“Kin ji abin da Suhail ya faɗa"

“Amma ba maganarsa kaɗai za mu saurara ba har da taki"

“Ke ce kika sha wahala"

“Yanzu ina so ki gaya mana"

“Shin kina son ku rabu?”

Falon ya sake yin tsit

Numfashin kowa ya tsaya

Iman ta ɗaga kanta a hankali

Ta fara kallon Malam

Sai ta kalli Abba

Idanunta suka sauka kan Ammi

Ta ga yadda fuskar Ammi ta cika da takaici da rashin jin daɗi

Daga ƙarshe

Idanunta suka haɗu da na Suhail

Ta ga yadda yake kallonta cikin tsoro

Kamar wanda ake shirin karɓe masa rayuwa

Sai ta sauke numfashi

A hankali ta girgiza kai

“A’a…”

Muryarta ta fito a raunane

“Ba na son mu rabu"

Nan take Suhail ya lumshe idanunsa

Hawaye suka gangaro masa

“Alhamdulillah…”

Shi kaɗai ya iya furtawa

Abba ya ɗaga hannayensa sama

“Alhamdulillahi Rabbil Aalameen.”

Sai dai…

Ammi

Takaici ya cika zuciyarta

Ta miƙe tsaye ba tare da ta ce komai ba

Ta kalli Iman

Ta girgiza kai cikin rashin jin daɗi

“Da alama duk abin da aka yi miki bai ishe ki darasi ba"

Ta juya cikin fushi

Ta fice daga falon

Kowa ya bita da kallo

Babu wanda ya dakatar da ita

Malam ya sauke ajiyar zuciya

Ya ce cikin natsuwa

“Maryama tana cikin fushi ne"

“In Sha Allah idan hankalinta ya kwanta, za ta fahimci cewa aure ba a gina shi da fushi ba"

Sai ya dubi Suhail da Iman.

“Amma kafin nan"

“Dukanku kuna buƙatar sake gina amana"

“Saboda amana idan ta karye… ba kalma ɗaya take gyaruwa ba.”

Suhail ya jinjina kai

“Na yarda Malam kuma nayi maka alkawari abun makamancin haka bazai sake faruwa ba"

Iman ba ta amsa ba

Sai dai ta share hawayenta

A karo na farko cikin watanni

Ta yi masa ɗan ƙaramin murmushi

Murmushin da Iman ta yi bai wuce na wasu daƙiƙu ba.

Sai ta sake sunkuyar da kanta.

Hawaye suka ci gaba da zuba daga idanunta

Malam ya kalli Suhail.'

Ya ce 

“Suhail"

“Allah Ya sake ba ka wata dama"

“Ba kowa ne yake samun wannan damar ba"

“Ka sani… amana idan ta karye tana da wahalar gyaruwa"

“Saboda haka, daga yau ina son ka tabbatar mini cewa ba za ka sake bari wani ya shiga tsakaninka da matarka ba"

Suhail ya share hawayensa

Ya jinjina kai

“Na yi alkawari Malam"

“Wallahi ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba"

“Ko da mahaifiyata ce"

“Ko da kowa ne"

“Ba zan sake yanke hukunci ba tare da na ji ta bakin Iman ba"

Ya juya ya kalli Iman

Cikin rawar murya ya ce

“Ki yafe mini"

“Na san kalmar ‘haƙuri’ ba za ta goge duk abin da kika sha ba"

“Amma ina roƙonki"

“Ki ba ni damar gyara abin da na lalata"

Iman ta lumshe idanunta

Kalaman Suhail suna shiga zuciyarta ɗaya bayan ɗaya

Ta tuna ranar da ya kore ta

Ta tuna yadda ta fita daga gidansa da cikin Khairiya da ita kanta batasan tana dashi ba

Ta tuna yadda ta yi watanni tana kuka cikin dare

Sai kuma ta tuna

Yadda kullum yake zuwa gidan Malam duk da taso ace ko sau Daya ya nemi ganin ta

Yadda bai taɓa daina tambayar lafiyarta ba

Yadda ya kusa rasa ransa saboda damuwar rasata

Ta sauke numfashi

A hankali ta ce

“Na yafe maka yaya Suhail"

“Amma"

Ta ɗan dakata

“Zuciyata tana buƙatar lokaci kafin komawa gidan ka"

Suhail ya jinjina kai da sauri

“Ko shekara za ta ɗauka"

“Zan jira"

“Matuƙar kina tare da ni"

Abba ya yi murmushi

Sai dai…

Har yanzu Ammi ba ta dawo falon ba

Khairiya ta fara kuka

Suhail ya karɓe ta ta karɓe ta daga hannun  iman

Ya karɓi Khairiya karo na farko a rayuwarsa

Da ya kalli ƙaramar fuskarta

Hawayensa suka zubo ba tare da ya iya tsayar da su ba.'

Ya sumbaci goshinta.l

Cikin sanyin murya ya ce

"ummulkhairi"

ita kuwa

Kamar ta san muryarsa

Sai ta buɗe idanunta kaɗan

Ta kalle shi

Sannan

Ta yi wani murmushi

Duk waɗanda suke falon suka yi shiru 

suna kallon ikon Allah

Bayan Malam ya ba Suhail da Iman damar yin magana su kaɗai…

A hankali kowa ya miƙe

Abba ya tafi ba tare daya jira Suhail ba dan dama a mota daban daban suka je

Hafsat ta shigo ta ɗauki Khairiya ta fita tana murmushi

Malam ma ya nufi ɗakin Ammi.

A cikin falon

Suhail da Iman kawai suka rage

Shiru ya mamaye wajen

Shirun da ya fi kowace magana nauyi

Na wasu daƙiƙu

Babu wanda ya iya buɗe baki

Suhail ne ya fara karya shirun

A hankali ya matsa kusa da ita

Bai zauna kusa sosai ba

Ya bar tazarar da ta dace tsakaninsu

Cikin sanyin murya ya ce

“Iman…”

Ta ɗago idanunta a hankali

Ya yi murmushi mai rauni

“Na daɗe ina jiran ranar nan"

“Ban taɓa tunanin zan sake samun damar zama kusa da ke haka ba"

Iman ta sauke idanunta

Suhail ya ci gaba

“Kin san abin da na fi tsoro?”

Ta girgiza kai

“Ranar da na shiga ɗakinmu…”

“Na tarar babu ke"

Ya yi murmushin takaici.

“Komai yana nan.”


"hatta wayar dana siya maki kin barmin"

“Amma ke…”

“Ba ki nan"

Ya runtse idanunsa

“Wallahi Iman"

“A ranar na gane darajarki"

“Na gane cewa gida ba gini ba ne"

“Ke ce gidana"

Muryarsa ta soma rawa

“Na yi rayuwa…”

“Amma ban sake rayuwa ba bayan tafiyarki"

“Ko abinci bana jin daɗinsa"

“Ko barci bana samun sa"

“Kullum idan dare ya yi…”

“Sai na tuna ranar da kika fita daga gidana"

Hawayensa suka zubo

“Wallahi…”

“Da ace zan iya mayar da lokaci baya"

“Da ban bari komai ya faru ba"

Ya ɗaga kai ya kalleta

“Kin san me ya fi kashe ni?

Iman ta girgiza kai

“Tun da kika tafi…”

“Ba wanda ya sake kirana"

‘My Counsel"

Da jin kalmar…

Iman ta fashe da kuka

Sai ta rufe fuskarta.

“Don Allah"

“Kada ka tuna min da waɗannan abubuwan"

Suhail ya matsa kaɗan

“Ki yi haƙuri"

“Na rantse da Allah…”

“Ba zan sake bari wani ya shiga tsakanina da ke ba"

“Ko da duniya baki ɗaya za ta haɗa kai"

“Zan tsaya a gefenki"

Iman ta share hawayenta

Ta ce cikin rawar murya

“Ka san me ya fi bani ciwo bayan rabuwar mu"

Suhail ya ce,"

“Menene?”

Ta ce

“Ba ranar da ka kore ni ba"

“Ba ranar da na bar gidanka ba.”

“Abin da ya fi bani ciwo"

“Shi ne…”

“Na yi ta jira"

“Na yi ta jiran ka zo ka ce min in yi hakurii ina dawo gidan ka"

“Amma ba ka zo ba"

Suhail ya dafe kansa.

“ko da nazo na kan rasa kalmomin da zan fadawa malan"

“Kusan kowane kwana uku ko huɗu ina zuwa"

“Amma ban taɓa samun damar ganinki ba"

“Na yi ta dawowa da zuciya a karye"

“Na kan daɗe zaune a cikin mota"

“Ina kallon ƙofar gidan ku"

“Ina fata ko zan hango ki"

“Amma ban taɓa ganinki ba"

Iman ta ɗago da sauri

Iman ta yi shiru

Ta yi murmushi cikin hawaye

Ta ce

“Ni ma…”

“Kullum"

“Babu ranar da sunanka bai dawo sabo a raina ba"

“Duk lokacin da na yi sallah…”

"Ina yi maka addu’a"

“Duk lokacin da na kalli Khairiya…”

“Sai na ga kamarka"

“Na yi ta ƙoƙarin tsanarka"

“Amma zuciyata ta ƙi"

Suhail ya lumshe idanunsa

“Alhamdulillah…”

Shi kaɗai ya iya furtawa


A ɗakin Ammi kuwa

Malam ya shiga a hankali

Ya same ta zaune kan gado

Idanunta har yanzu sun kumbura saboda kuka

Ya zauna kusa da ita

“Maryama"

Ba ta amsa ba

Sai ya kama hannunta

“Na san dalilin da ya sa kike tsoron komawar Iman"

A hankali ta ɗago kai

“Wallahi Malam…”

“Ba na ƙin Suhail"

“Yaro ne mai kirki"

“Amma…”

Muryarta ta karye

“Na ga abin da ’yata ta sha"

“Na ga yadda ta dawo gida"

“Na ga yadda take kuka cikin dare"

“Na ga yadda take riƙe cikinta tana cewa"

‘Ammi, zuciyata na ciwo"

Hawayenta suka sake zuba

“Yau idan na sake mayar da ita…”

“Na sake ganin an dawo mini da ita haka…”

“Wallahi ba zan iya jurewa ba."

Malam ya shafa bayanta

“Maryama…”

“Ke uwa ce"

“Tsoranki na uwa ne"

“Amma kin lura da wani abu?”

Ta girgiza kai

“Tun da Suhail ya shigo…”

“Kin ga yadda Iman take kallonsa?”

Ammi ta yi shiru

“Kin ga yadda ta kasa ɓoye hawayenta?”

“Kin ga yadda muryarta ta canza idan yana magana?”

“Wallahi…”

“Yarinyar nan har yau tana son mijinta.”

“Idan muka hana ta komawa saboda tsoronmu…”

“Wataƙila mu ne za mu hana ta farin cikinta.”

Ammi ta rufe idanunta

Ta sauke wani dogon numfashi

“Allah ya basu zaman lafiya"

Malam ya ce cikin natsuwa,

“Amin.”

“Mu bar hukuncin a hannunta"

“Domin wannan karon"

“Ba mu ne za mu zaɓa mata rayuwa ba ita zata zaba wa kan ta "

Har dare Suhail bai tashi daga gidan Malam ba

Shi da Iman suna zaune a falon cikin nutsuwa

Sau da yawa sukan yi shiru suna kallon junansu

Kowanne yana jin kamar shekarun da suka yi ba tare da juna ba suna dawowa a wannan dare.

Har aka kira sallar Magariba

Suhail bai tashi ba iman ta kawo masa ruwa yayi alwala yayi sallar sa a ɗaki

Malam ya lura

Ya yi murmushi kawai

Har aka yi Isha’i

Sai Malam ya ce da Iman 

“ya kamata Ki raka mijinki ya tafi"

Iman ta ɗauko  mayafinta

Ta bi bayansa har ƙofar gida

Da suka tsaya kusa da motarsa

Na wasu mintoci babu wanda ya yi magana

Suhail ya kamo hannunta a hankali

“Kina sane"

“Kwana bakwai da suka gabata sun fi kowanne tsayi a rayuwata.”

Iman ta sauke idanunta

Ya ɗan yi murmushi

“zan dawowa nan ba da jimawa ba"

Ta jinjina kai

“Ina jira"

Ya sake kallonta

“Ki kula da kanki"

“Da ummulkhairi.”

Kai ta jinjina masa

Sannan ya shiga mota

Har ya kunna motar

Sai ya sake sauke gilashi

“Iman…”

Ta ɗago

“I love you"

Kunya ta sa ta kasa magana

Sai murmushi kawai ta yi.'

Wannan murmushin kaɗai ya wadatar masa

Ya ja motarsa ya kama hanyar Abuja

Cikin dare ya isa gidansa.'

Sai da ya faka motar

Ya sauke numfashi

Kimanin sati guda kenan bai dawo gidan ba

Yana shiga harabar gidan

Sai ya ji gidan kamar ba gidansa ba

Shiru

Babu walwala

Da ya shiga falon

Khalil ne ya fara ganinsa

“Abba!”

Yaron ya yi gudu ya rungume shi da ƙarfi

Suhail ya ɗauke shi

Ya manna shi a ƙirjinsa

A lokacin ne zuciyarsa ta soki wani abu

“Me na yi wa wannan yaro haka"

“Har kwana bakwai ban kira ba…”

“Ban tambayi lafiyarsa ba…”

Ya sumbaci goshinsa

“I’m sorry, son for not see me"

Jennifer ta fito daga kitchen

“Sannu da zuwa Sir"

“yww Jennifer"

Ya kalli falon

“Ina Zeenah?”

Jennifer ta yi shiru

Ta kalli agogon bango

Karfe goma na dare

Suhail ya haɗe gira

“Har yanzu ba ta dawo ba?”

Jennifer ta sunkuyar da kai

“Sir…”

“Tun bayan tafiyarka"

“Hajiya tana yawan fita"

“Wani lokacin ma har kwana take a waje"

“Idan za ta dawo"

“Sai cikin dare"

Suhail ya yi shiru

Wani irin tunani ya fara yawo a ransa

Bai sake tambaya ba

Ya ɗauki Khalil

Suka nufi ɗakinsa

Ya yi masa wanka

Ya canja masa kaya

Ya kwantar da shi

Sai da Khalil ya yi barci

Amma shi

Barci ya ƙi zuwan masa

Tunani kawai yake

“Ina Zeenah take zuwa?”

“Me take yi?”

“Me yasa babu wanda ya taɓa sanar da ni?”

Ya dafe kansa

“Komai ma mene ne"

"Sai na gano.”

Karfe sha biyu na dare.

Sai ya ji ƙarar  motar ta ta tsaya a harabar gidan."

Ya kashe fitilar ɗakinsa

Ya tsaya bakin labule

Ya hango Zeenah tana fitowa daga mota

Sanye take da wata doguwar riga mai tsada

Ta yi kwalliya sosai

Ta shiga cikin gidan kamar ba abin da ya faru

Jennifer na zaune a falo

Da ta ga Khalil bai nan

Sai ta tambaya

“Jennifer…”

“Ina Khalil?”

Jennifer ta amsa

“Yana ɗakin Yallabai.”

Gaban Zeenah ya faɗi.'

Amma ta danne komai

Ta gyara mayafinta.

Ta nufi ɗakin Suhail

Ta turo ƙofar

Sai ta same shi zaune bakin gado.

Idanunsa na kanta

Shiru ya mamaye ɗakin

Daga ƙarshe Suhail ya ce

“Ina kika je?”

Ta ɗaga gira

“Wannan tambayar kai ya kamata ayi wa tun kwanaki bakwai da suka wuce"

Suhail ya ce cikin nutsuwa

“Ina tambayarki yanzu"

Ta yi murmushin takaici

“Inda nake samun farin ciki"

“Saboda kai ba ka ba ni sh"

Ya yi shiru

Ta ci gaba

“Yanzu ka tuna kana da mata?”

“Ko saboda kana wajen matar da saki ta shiga tsakaninka da ita ka "

“Da ’yarka da aka haifa maka?”

Suhail ya sauke numfashi.

“Zeenah…”

“Ki saurare ni"

Ta katse shi

“suhail Yanzu ka zo kana son in saurare ka?”

“Lokacin da kake can"

“Ni da Khalil muna nan muna jiran ka"

Suhail ya matso kusa da ita

“Ki yi haƙuri"

“Na yi kuskure"

Ta girgiza kai

“Haƙuri ba ya mayar da kwanakin da suka wuce"

Ta juya zata fita

Suhail ya kira sunanta

“Zeenah.”

Ko waiwayowa ba ta yi ba

Ta fita

Shi kuwa

Ya tsaya yana kallon ƙofar

Ya san akwai wata magana da ba a faɗa masa ba

Washegari da safe…

Tun ƙarfe takwas.'

Zeenah ta shirya cikin wata doguwar abaya

Ta ɗauki jakarta

Ta fita

Sai dai

Ba ta san cewa

Tun kafin ta fita daga gate

Suhail ya riga ya kunna motarsa ba tare data lura dashi ba

A hankali

Ya bi bayanta daga nesa

Yau
Sai ya gano inda take zuwa
Tun daga nesa

like share and comment