Chapter 2:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Wata kyakkyawar matace zaune a daya daga cikin royal chairs din da ke parlourn, gabanta system ne tana video call dawani kyakkyawan saurayi, jiyo sassanyar muryarta nayi tana cewa “yade kamata kudawo sabida ayya tanace kan cewar kudawo kasarku” “insha Allahu zamuzo mamy zanyi convincing dinsa amma kinsan mutuminne da kafiyan tsiya “yafada yana murmushi, cikin wasa sai mamy tace “amanar tawa kake cewa haka” yana dariya yace “Allah ya huci ran mamyna, kwantar da hankalinki aikinsan aikin hannuna zan jawoshi muzo insha Allah” “na yarda da kai d'ana” “to mamy nima ina nawa amanar da take wajenki” ya tambaya cike da tsokana, murmushi mamy tayi a lokacinda ta dan juya gefe sai tace “ga amanar ta kama sai kaganewa kanka ja'iri kawai“.
Jabir ne ke hawa stairs cikin nustuwa yayinda waya ke kare a kunnensa bai tsaya a parlourn ba ya wuce wani corridor inda ya sadasa da wani karamin matakala, bayan yahau, nan ma wani karamin parlour ne hadadde sai yabude wani kofar daki ya shiga, dakin koina duhu sai ya kunna light ananne haske ya garwaye hadaddiyar dakin bai tsaya koina ba ya nufi sitting area yadauki pillow sai yaje yafara bugawa saurayin dake bacci akan hadaddiyar gadon da zai iya yin jarin wani talaka, bugamasa yakeyi tare da cewa”dalla malam tashi da baccin asarar da kake yi maybe ko sallar fajr ma ba kayi ba “adaidai time din saurayin yabude grey eyes dinsa ya zubawa Jay, irin kallon da yake masa ne yasa Jay tuntsurewa da dariya ba tareda ya shirya ba, bai tankasa ba ya mike ya wuce bathroom.
Jay kuma yayi kawanciyarsa akan gadon, ba zato ba sammani yaji saukan ruwan sanyi gaske akansa, a firgice ya mike yace “goooddd"yanda yaja ‘god'dinne yasa ‘AZAN’ yin dariya sai kuma yace"so u thought kai kadai ka iya mugunta right “sai Jay dake goge wayarshine yace ”to ai kai dama can mugune ji yanda kazo ka watsawa bawan Allah ruwan sanyi, kai niba wannan bama munyi magana da mamy akan zuwanmu Nigeria 🇳🇬 “nan take azan yabata fuska sai Jay yace “dude bafa gabada ya zamu komaba, ayya ce tasa mamy agaba kan cewar lalle sai mun dawo”budan bakin azan cewa yayi “nifa ba inda zani, am going no where “.