Chapter 3:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Ammie ce ta bude kofar dakin ruhy sai ta ganta kwance akan sallayarta bacci yafara daukanta, tasarta tayi tareda cemata “ruhaina lokaci ya tafifa ko yau bazaki fita bane “ mutsitsika ido tai tareda cewa “wallahi ammie kasala yau nakeji dakyar in zan iya fita” kafin ammie tabata amsa wayarta tafara ringing, dauka tayi tareda sallama sai tayi shuru tanajin nacikin wayar sai tace “ok toh gani nan zuwa” bayan ta sauke wayan ta bata fuska tana kallon mamartata “me kuma yafaru” cewar ammie “costumers ne suka kirani wai wajen arufe gashi yau bana jin fita” “to yakika iya, tashi ki shirya kitafi tunda har sun zo suna jiranki” tashi tayi tashiga bathroom, sai ammie ma tamike ta fita,.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin abaya milk colour tayi kyau iya kyau dukda bawani kwalliya tayiba, fitowa tayi tareda yiwa ammie sallama, kafin tafita a parlourn tajiyo muryar huda tana cewa “adda yau zaki fita shine ko nemana bakiyiba” juyowa tayi tana murmushi mai qayatarwa tayi hugging kanwartata da a shekaru bazata wuce 6 ba “ai na zata autar ammie bacci take, yanzu sauri nake bara naje nadawo kinji” “toh adda amma kizomin da abu mai dadi” “karki damu good girl sai nazo, byyee”.
Jay ne ya juya ya kallesa cikeda mamaki yace “banganeba cewa fa kayi u are going no where, what do you mean maganar mamyne bazaka biba ko me kake nufi “ “kai ma kasan wannan ba maganar mamy bane, mamy bata taba insisting sai nadawo ba, wannan rigimemmiyar tsohowar ce take so nakoma” juyawa Jay yayi tareda cewa “nidai yanzu bara naje na chanja kayannan daka gama jikamin shi, in yaso mazauna muyi magana cikin nutsuwa dan kaima kasan in kaki xuwa mami zakasaka cikin matsala” sai ya fita batareda ya jira amsar azan ba, shikuma azan juya grey eyes dinsa yayi tareda juyawa yacire lounge wear dindake jikinsa ya nufi bathroom.
Hangosu tayi cikin wani mota suna jiranta, sai takaraso suka gaisa tace su karasa ciki. Bude shop din tayi suka shuge.
Bayan tabasu wajen zama suka zauna sai suka fara fadamata kayayyakin da suke bukata “toh abayas din gasunan a rataye sai kuduba kuzaba wanda sukayi muku"nanne matan suka fara zaba suna yaba kyau da kuma tsaruwan kayayyakin nata yayinda ita kuma tawuce hada musu sauran atampopi, laces, jalbabs din da suka bukata.