Chapter 4:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writer
Mamy ce zaune gaban ayya tana mika gaisuwa, kawar da kai ayya tayi batareda ta amsa ba tafara masifa “oh ni y'asu adole dai ana so arabamin kan ahali, ai dole ma hakan takasance nayi nayi kar ya auro ki amma yanace, sai da ya auroki gashi ta sanadiyyarki kan ahalina duk ya tarwatse karasa ko dangin mayu ya aura oho”kasa da kai mamy tayi tareda da jin zafi da radadin maganganun ayya sai tace cikin sanyin murya “kiyi hakuri ayya insha Allah zasu dawo” “yo karma yadawo mana ai can tarege muku, nan da shi dawudan ya auri yar fulani ai da hakan bai faruba, yaro rabonshi dagida yau shekara goma kenan"mom hana dake zaune tana jinsu duk jikita yayi sanyi da maganganun ayyan sai ta amshi maganar da cewa “a'a ayya shekara hudu ne fa” “yo ko shekara dayane ai ya dade, da jinin mune na fulani ai da bazaiyi nisa da gida hakaba,kodayeke dole kisa baki saboda kema an janye miki d’a an tafi da shi can kamar kasar haihuwarsa”nanne suka jiyo muryar daddy bayan yayi sallama yana cewa “inban da abinki ayya ai jabir da Muhammad abu dayane, yaranda tunsuna kanana suka taso tare acan”. To ananne sai mamy ta dan ji relief dan koba komai zuwan daddy zai sa acanja topic din.
Fitowa yayi yana faman Kiran sunan Jay “Jay nifa yunwa nake ji”d’an wai wayowa Jay yayi ya kallesa sai kuma ya maida dubansa ga system din da yake dannawa yace “ai gaka ga kitchen sai ka shiga ka girka” “stop joking bro am starving fa and da kake cewa nayi girki u have already knew that I have never cooked, and in kamanta bari in tunatarma, game mukayi nayi daring dinka zaka mana girki for 1 week, that's why kaga na dakatarda cocos na gidannan, and sai ka wani ce nadafa abinci, ni malam yunwa nakeji” “alright toh zauna muyi maganar zuwa Nigeria 🇳🇬 in ba hakaba bakai bacin abinci” bayanda ya iya dan tsaf Jay zai iya aikatawa danma bayajin cin abincin waje ne da ai bazai tsaya yana mishi iskanciba, “ina jin ka” yafada cikin yanayinda ke nuni da bayanda ya iya “dude ka nutsu kayi tunani ni bazan takuraka ba amma idan kayi duba da halinda mamy ke shiga a dalilin rashin zuwanka da kuma takurawan ayya, wannan kadai ya is a yasa ka yarda mu kuma” kallon Jay kawai yake har yakai aya sai Jay din ya sake cewa “kace wani abu mana u just keep quiet and staring at me?” “to me zance, zan koma, but just because of mamy, and sometimes wannan ayya ko me ake cemata has problem wallahi”murmushi Jay yayi a zuciyarsa yace “badai ka aminceba”sai ya mike yace “toh your food is on dining” “what! u mean abincin yana dining shine kayi tabani wahala haka"shiko Jay tuni yayi gaba abin shi yana dariya sai azan ya girgiza kai ya mike Shima ya nufi kofar da zata sadashi da dinning room din.