Mataccen buri

Page 1

by @sadiyaabdulrazak954

Akwai banbanci a tsakanin kalmar lalatawa da kuma lalacewa. Idan mutum ya je wurin mata ma su zaman kansu,ma'ana karuwai suka aikata masha'a,wannan sunan shi lalacewa,ba za a ce ya lalata mace ba,sai dai ace sun lalace. Sab'anin wanda ya je gidan su yarinya ya yaudareta,da wayo da dubara,ko kuma ya rud'eta da kud'i,wannan ake cewa lalatawa.

Na lalace da matan da ba zan iya k'irga adadin su ba,wasu a gidana,wasu a hotel's,wasu a club,wasu a gidajensu. Kuma na lalata mata da adadin su ya kai bakwai,wanda nake da tabbacin Ni ne na fara sanin su,ma'ana Ni na saka su a harkar banza,amma kaf cikin su yara uku ne suka tsaya mini a rai,wanda ba na jin zan manta da kalar yaudarar da nayi musu,Ni da kaina ina Allah wadai da halina na yaudara. Amma hakan bai tab'a sa na ji zan daina ba,har sai ranar da na samu nasarar dawo da ran MATACCEN BURINA!

Ba zan daina kallon iyayena a matsayin wanda suka saka Ni a halin da nake ciki yanzu ba,duk da ina sane,babu iyayen da za su so su ga d'ansu ya lalace,amma wasu iyayen suna raina sanadiyya,na tabbatar da sun san zan shiga halin da nake ciki a yanzu da ba su bari burina ya mutu ba,su suka kashe mini buri,kuma daga k'arshe abun ya dame su,bayan sun yi gwagwarmayar dawo da ruhin burina sun kasa,abun takaici sai suka kalle Ni,ido cikin ido suke sanar da Ni,ba za su iya raya matacce ba, Allah ne kad'ai yake da ikon wannan,saboda haka kar nayi jayayya da hukuncin ubangiji,murmushin takaici kawai nayi,ina jinjina son zuciya irin na wasu mutanen,sun san Allah ne mai hukunci amma suka kasa yarda shi ya hukunta komai tsakani na da Ummul-khairi,suka tashi tsaye akan wasu raunanan hujjojin su,har sai da suka yi nasarar kashe mini burina na aurenta,sai daga baya su ce za su yi mini nasihar tawakkali,bayan a baya sun nuna min ba su san shi ba,ba zan iya hak'uri ba,zan iya rasa su na d'auki k'addara,amma ban da Ummul-khairi,wacce nake yi wa lak'abi da Khairin Saifu.

Sunana Saifullahi Usman. Ni ne d'a na uku a wurin iyayena,akwai mata guda biyar dake bin bayana,mu takwas ne kenan, maza uku,mata biyar,mahaifina yana da rufin asiri,dan duk eriyarmu idan za a yi lissafin ma su hali,shi ne na d'aya,kaf! Gidanmu kanmu a had'e yake, mun taso cikin k'aunar juna,iyayenmu suna son mu,kuma suna son duk abin da muke so,duk da ya kasance d'an kasuwa,amma ya fi burin muyi karatun boko mai zurfi,mu rik'e aikin gwamnati,shi ya zab'a wa kowa abin da zai karanta,ya ce babban yayanmu shi ne Soja,mai bi masa Lauya ne,Ni kuma likita ne,kowa ya amince,dan haka abin da na karanta kenan.

Shi farin jini,wata baiwa ce da Allah yake zab'ar wasu cikin bayin shi ya ba su,Allah ya ba Ni wannan baiwar,kuma Alhamdulillah a baya na sarrafata ta hanyar da ta dace,kafin lokacin da k'addarar Ummul-khairi ta canza Ni,daga Saifullahi ta mayar da Ni,d'an watangaririya. Ko a gidanmu Ni ne d'an So,kowa yana so na,haka ma a makaranta,cikin dangi,da unguwa,duk inda na shiga ina yin farin jini, ana nuna mini so,kodayake Ni ma mutum ne mai son mutane,kuma ina da fara'a da surutu sosai,ina da saurin sabo,uwa-uba ba na raina matsayin wani,ba na kallon wadatar mahaifina,ba na raina na k'asa da Ni,bare kuma wanda ya girme Ni,duk wanda ya nuna yana yi na,Ni ma ina yin shi,ba Ni da abokin fad'a ko d'aya,rayuwata nake yi lafiya lau,a wancen lokacin. Kodayake daga baya duka na canza halayena,ko kuma na ce So ya canza Ni,dan idan na ce ita ce ta canza Ni,ban yi mata adalci ba.

Ranar da na fara ganin Khairi,na kai wa wani abokina ziyara ne,da yamma na d'auki wanka,bisa al'adata,dan Ni d'in d'an gayu ne, ina son ado,na buga babur d'ina na d'auki hanyar Fage,ina jin shauk'i har cikin raina,to a lokacin fresh nake rayuwata,ba Ni da damuwar komai,a shagon da yake yin d'inki na same shi,na shiga na mik'a wa Hafiz hannu muka tafa,na zauna muka fara fira,yana d'inki ina kallo saboda abun yana burgeNi.

Ban jima a shagon ba,k'addarata ta bayyana. Kamar wanda aka fizgi idanuna na hangi yarinyar da take tunkaro shagon,cikin takun yauk'i,fuskarta babu alamar wasa,Ni kuwa na zuba mata ido ina k'are mata kallo,tana yin sallama nayi farat na amsa,murmushi shimfid'e a fuskata na ce"sannu da zuwa!" Ni dama can ina so na ga mace kyakkyawa,musamman mai nutsuwa kamar dai wannan d'in.

Ba ta amsa min ba,ta k'arasa shigowa,na gyara zama na ce"sannu da zuwa k'anwata,d'inki kika kawo?"

Ba ta kalle Ni ba,sai ma had'e rai da tayi ta cewa Hafiz"Maryam ce ta aikoNi".

Hafiz ya tashi ya d'akko leda mai d'auke da kayan d'inki ya mik'a mata.

Ta karb'a ta zuge jaka tana cewa"ta ce nawa za ta cika maka?"

"Dari tara". Ya ba ta amsa.

Ni da nake ta kallon yarinyar da burgewa,nayi farat na ce"ba matsala,zan cika mata!".

Sai a lokacin ta kalle Ni,na sakar mata murmushi ina gyad'a kai,alamar tabbatarwa.

"Ba na so!" Ta fad'a tana mik'a wa Hafiz dubu d'aya.

Ni ma na ciro dubun daga aljihuna na mik'a masa,na ce"ai ba d'inkin ki ba ne,na Maryam ne,kuma k'awata ce,ki ce mata Saifullahi ne ya biya mata".

Ko kallona ba ta yi ba,ta ajiye dubun akan keken Hafiz,ta ce"ba Ni canjin".

Na ce"haba dai k'anwar Maryam..."

Ban kai k'arshe ba,Hafiz ya kai min duka ya ce"kai dai ka shiga uku! Yarinyar ma sai ka tisa ta da zance? Tun da ta ce ba ta so ana dole?"

Ya ciro nera d'ari ya ba ta,ta juya ta tafi.

Na tashi da sauri zan bi bayanta,ya rik'o hannuna,sai na fizge ina hararar shi,har na kai k'ofa na ji ya ce"je ka! Amma ka sani matar aure ce".

Na ji kamar ya sare mini k'afafuwa,na dawo na zauna jikina yayi sanyi lokaci d'aya,shi kuma ya ci gaba da d'inkin shi yana murmushi.

"Amma tun farko ya kamata ka sanar mini" Na fad'a ina jin kamar na ci mutuncin aure.

Ya fara dariya,ya ce"k'arya nake wallahi,buduruwa ce".

Na ja tsaki mai tsayi na ce"amma ba ka da kirki!"

Hafiz ya ce"kai sai yaushe za ka fara saita kanka idan ka ga mata?"

Na ce"amma ka san kyawawa kawai nake so,kuma ma su nutsuwa,wannan yarinyar ta yi min sosai,sai dai tana da jan aji".

Hafiz ya ce"tana da wulak'anci za ka ce! Ba ka ga ko murmushi ban yi mata ba? Yarinyar nan jin kanta take kamar 'yar shugaban k'asa,kai ba ka ga yanda take taku ba,tana kallon mutane a d'age? Kar ma ka soma,dan ba ta kula kowa! To waye ma zai je wurin ta? Kana ta wani washe mata baki,ta d'auke ka banza,dan Allah ka dinga jan ajinka!".

Na jinjina kai na ce"ya sunanta? Ina ne gidan su?"

Ya ce"Ummul-khairi sunanta, gidan su babu nisa da shagon nan!".

Na jinjina kai na ce"ok! Gobe da daddare zan dawo ka raka Ni dan Allah! Ni fa tayi min,kuma tsarin nata da jan aji duk sun yi,irinta nake so".

Hafiz yayi murmushi ya ce"Allah ya kai mu".

Wannan ne ganinta na farko, kuma tun a lokacin tayi shara tayi shimfid'a ta kishingid'a a fadar zuciyata. A ranar komai nake yi fuskarta tana dawo mini,har na ji na k'agauta goben ta yi.

Kamar yanda na shirya washegari a unguwar su nayi sallar isha'i,na buga wankan shaddata har da hula,wacce ba kodayaushe nake saka wa ba,wani shauki ne yake tasowa tun daga cikin zuciyata,yana bayyana kan shi a fuskata. Muna fitowa daga masallaci yayi mini jagora zuwa gidan,a hanya yana ta yi mini dariya,wai Allah yasa ma ta kalle Ni,Ni kuwa murmushi kawai nake,ina ayyana har ma ta karb'e Ni,saboda na saba da yanda mata da yawa suke turo min sak'on so,ina ba su amsa da ina da matar da zan aura,duk da ba Ni da kowa,hasalima wannan ne karon farko da zan fara zuwa gidan su wata yarinya da sunan so,duk da dai ba ita ce macen farko da na ji ta burge Ni ba.

Hafiz ne ya ciro waya ya kira Maryam,wacce ya ce yayarta ce,ya ce mata ta ce ana kiran Ummul-khairi a k'ofar gida. Tare suka fito da Maryam d'in,sai dai ita Sarauniyar ba ta k'araso inda muke ba,muka gaisa da Maryam,ta koma cikin gida,shi ma Hafiz yayi gefe yana danna waya.

Sai na k'arasa inda ta coge,fuskata d'auke da murmushi nayi mata sallama.

Ta ce"kai ne kake kira na? Ga Ni,me ya faru?"

Sai nayi murmushina ce"Ummul-khairi,babu abin da ya faru,sai alkhairi in sha Allah! Da farko dai mu gaisa ko,kina lafiya?"

"Lafiya lau!" Ta amsa min a tak'aice.

Ni ma sai na saita kaina daga yanayina na barkwanci,na kalleta na ce"suna na Saifullahi,Ni abokin Hafiz ne,gidanmu a Zoo road yake,amm...ki yi hak'uri Ni ban saba soyayya ba,wannan shi ne karon farko da na je wurin yarinya,to ko zan fad'i abin da ba haka ake fad'a ba,sai ki yi mini uzuri".

Na kai k'arshe da murmushi.

Sannan na d'ora"jiya na fara ganin ki,na san dai kin gane Ni ko? Yanayin ki ya burgeni sosai, kuma na ji kina da halaye ma su kyau daga bakin abokina,a tak'aice dai idan wani bai riga Ni ba,ina son ki,kuma da niyyar aure har zuciyata".

Tayi shiru kamar ba ta ji maganganu na ba.

Sai na ji kamar zan karaya,a sanyaye na ce"wani ya riga Ni,ko kuma ban yi miki ba? Gaskiya d'aya ce,wannan ne zuwana na farko,zan so ki sanar da Ni gaskiya,idan ban yi miki ba na janye, tun kafin nayi nisa cikin soyayyarki".

Kamar ba za ta yi magana,har na fitar da rai,sai na ji muryarta mai sanyi ta ce"ba Ni da wanda nake so,kuma kai ma ba ka yi mini ba!".

Nayi murmushi na ce"da wuri haka? Ba za ki d'an samu lokaci ki yi tunani akai ba? Zan ba ki sati d'aya,zan dawo, idan har lokacin kin ji ban yi miki ba,zan hak'ura,na gode da ba Ni lokacinki!".

Na mik'a mata wayata,na ce"saka min lambarki,sai mu dinga gaisawa".

Ta girgiza kai ta ce"ba Ni da ita".

Na ce"sorry! Gobe zan kawo miki waya".

"Ba na so!". Ta fad'a tana shirin juyawa cikin gidan su.

"'Dan tsaya mana,ko sallama ba mu yi ba".

Na fad'a ina ciro dubu biyar d'in da na saka a aljihu tun daga gida,saboda nayi mata ihsani,na mik'a mata na ce" ga wannan".

Sai ta girgiza kai ta ce"na gode".

Ba ta sake sakan d'aya ba,ta shiga gida,ta bar Ni tsaye,da begenta.

Na ja k'afa na koma inda Hafiz yake zaune, ya tashi muka tafi muna tattaunawa.

Kun san wani abun mamaki? Ashe a wannan daren Ummul-khairi ta karb'i tayin soyayyata,amma sai ta dinga ja mini rai,saboda jan aji a jinin yarinyar yake. Kodayake ita ma daga baya rayuwa ta canza ta.

Haka na koma gida,ina taraddadi a zuciyata,saboda sosai son yarinyar yayi min kamun kazar kuku,gefe guda kuma ina tabbatar wa kaina za ta karb'e Ni kafin sati d'ayan.

Ina shigowa gida,na tarar da Nabila zaune a corridor ita kad'ai, babu abin da take yi. Na k'araso inda take ina canza fuska na ce"Nabila ba na hana ki zaman kad'aici ba?"

Ta tashi tana murmushi ta ce"sorry Brother ai kai nake jira".

Na ce"Nabila ki taya Ni addu'a,na zab'o wacce nake so,Allah ya sa ta karb'e Ni ".

Ta zaro ido ta ce" da gaske Brother? Wace ce,a ina take?"

Nayi murmushi na zauna na zayyane mata komai,amma sai na lura ba tayi farin ciki ba,kuma dama na san hakan zai iya faruwa,dan na jima da gane yarinyar ta kamu da so na,sai dai ban taba nuna mata na gane ba,saboda kar na ba ta k'ofar da za ta furta mini.

Ita Nabila 'yar'uwata ce,ita ce babbar 'ya a wurin k'anwar Babata,an yi baikon ta da wani da take yi wa mugun So,auren ya rage sati hud'u yayi hatsari ya rasu. Tun daga lokacin take cikin damuwa mai tsanani,hakan ya sa aka ce ta dawo gidan mu,cikin 'yan'uwa tun da ga sa'anninta nan za ta fi warwarewa.

Sosai na ji tausayin yarinyar,kuma dama Ni mutum ne mai son mutane, ina damuwa da damuwar wani a wancen lokacin, hakan tasa na ja ta a jiki sosai nake yin iya k'ok'arina na faranta mata,mun samu shak'uwa sosai,har ta kai ta fara nuna min alamomin So,Ni kuma har zuciyata ba na son ta,sai dai soyayya ta jini,da kuma tausayi.

Hmm! Nabila ma ta shiga kundin k'addarata! Daga baya duka za ku ji.

Na ce"me zan yi miki kike jira na?"

Cikin shagwabar da ta saba yi mini ta ce"dama fura nake so,kuma babu a gidan,amma na fasa sha ma kawai".

Na ce"bari na samo miki".

"Ka bar shi,sai da safe" Ta fad'a tana shige wa ciki.

Ni kuma na bi ta da ido,ina tab'e baki.

*** [10/23, 11:15 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕