Page 2
A daren nan Khairi ba ta bar zuciyata ta sarara ba,haka ta dinga azalzalata,ina jin kamar na tashi na tafi gidan su,na kalle ta ko zan ji sauk'i,tun kafin ta amince har na fara sako ta cikin tsare-tsaren rayuwar aurena. Washegari da yamma na je shagon Hafiz,yana gani na ya fara dariya ya ce"ai dama na sani zan ta samun ziyarar abokina,tun da an samu dalili".
Nayi murmushi na zauna,na ce"wallahi Hafiz kamar ba zan jure sati d'ayan da na ba ta ba". Na ja tsaki,ina sauke numfashi.
Hafiz ya ce"to ka koma mana,sai ka fad'a mata satin ya yi maka nisa".
Na ce"da dai tana da waya,sai na samu damar sake shigar da kaina,to ta ce ba ta da waya".
Hafiz ya yi tsaki ya ce"ta raina ka dai,amma ba za ta rasa waya,bari na tambayar maka Maryam".
Ya d'aga waya ya kira Maryam,suka gaisa,ya ce ta turo mana lambar Khairi,cikin mintuna ta turo. Na karb'a na kwafe ina murmushi, da kuma jinjina ajin yarinyar,kenan Ni ban kai ma na samu lambarta ba,sai da na koma gida na nutsu bayan sallar isha'i na kira ta. Ta d'auka da sallama,na gaisheta ta amsa sannan na fad'a mata Ni ne,muka gaisa sama-sama,har nayi mata wasu tambayoyin,nan nake jin a shekarar ta yi Candy,na kuma sake tabbatar wa ba ta da wani saurayi,sai Ni da nake fatan samun muhalli. Tun daga nan kullum sai mun yi waya,da yake ina da surutu sosai ba na rasa firar da zan ja ta da ita,ina yi tana waskewa haka dai ake wayar,kuma ban tambaye ta matsayar da ta yanke ba,na fi so sai ga Ni ga ta,duk da ma na saddakar tana so na,tun da har hotunanta ta ba Ni,suna rage min kewarta sosai.
Ranar da satin ya cika na koma gidan su,amma sai ta ce min ita fa har yanzu ba ta gama tantance Ni ba,kuma ba ta ce tana so na ba. A haka muka dinga tafiyar fa har wata biyu,duk sati ina zuwa sau biyu,muna yin fira amma ta k'i amsa tana so na,saboda tsantsar izzarta.
Watarana da rana ina d'akina,muna waya da ita cikin shauki,Nabila ta turo k'ofa ta shigo. Na katse wayar ina kallon yanayin yarinyar,kwana biyun na lura kamar damuwarta tana son dawowa.
Tana kallon gefe ta ce"Ummi ce ta ce na fad'a maka ba Ni da lafiya,ka ba Ni magani".
Na tashi zaune,na ce"mene ne ya sameki?"
"Ciwon kai,da jiri". Ta yi maganar tana shirin barin d'akin.
Na ce"to ina za ki je? Zo ki zauna".
Ta zauna a k'asan katifar,ta mai da kanta k'asa.
Na ce"me yake damun ki?"
"Ba komai!" Tayi maganar kamar za ta yi kuka.
Na matso kusa da ita ina jin damuwa,na ce"tunanin kika dawo da shi ko? Kina so ki mutu,ko ki haukace ko?"
Ta share hawaye ta ce"A'a".
Na ce"to ki cire tunanin komai daga zuciyarka,ko kin tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo? Allah bai yi mijinki ba ne,dan haka ki manta kun yi wata rayuwa,ki fuskanci sabuwar rayuwa,kin ji ko!?"
Ta gyad'a mini kai.
Na ce"je ki,bari nayi wanka na fita na kawo miki maganin".
Ta tashi ta fita,tana goge hawaye,Ni kuma na koma na kwanta,na sake kiran lambar Khairita.
Sai da na kira sau uku ta d'auka,nayi murmushi na ce"dan Allah ki rage jan ajin nan naki".
Ta ce"dan ma ka samu na d'aga ko?"
"To me nayi?" Na tambaya a shagwabe.
Ta ce"me ya sa ka katse ba muyi sallama ba?"
Na ce"sorry! K'anwata ce ta shigo d'akin".
Ta ce"ban hak'ura ba,kuma na ba ka hutun wata d'aya,kar ka kira Ni,kar ka zo gidanmu".
Na tashi zaune na ce"wasa kike yi!"
Ta ce"Allah da gaske,ko ka zo ba zan fita ba".
Na ce"nayi laifi,ayi hak'uri dan Allah, ba zan iya wata d'aya ban ki ba".
Ta ce"to idan kana so na janye sai ka yi aski yau".
Na zaro ido,ina shafa sumar kaina,wacce nake ji da ita,nayi murmushi na ce"sorry! Ban shirya aski ba,ba zan k'ara katse miki waya ba,kin hak'ura ko Khairin Saifu?"
Ta ce"wallahi ban hak'ura ba,sai ka yi aski,idan kuma ba za ka iya ba,kar ma ka zo mini".
Na ce"zan yi,amma sai kin ce min I love you".
Sai ta yi dariya ta katse kiran.
Na bi ta da sak'on I love you.
Na tashi nayi wanka,na fito ina jin zuciyata k'alau,kamar ba Ni da wata damuwa a duniya,dan har 'yar wak'a nake rairaiwa,a falo na tarar da duka k'annen nawa,kasancewar ranar Alhamis ne babu islamiyya,na kalle su duka na ce"ina Nabila?"
Suka had'a baki wurin fad'in"tana waje".
Ina fita na ganta zaune a corridor ta had'a kai da gwiwa. Nayi tafi,ta d'ago ta kalle Ni,sai na ga idanunta sun canza alamun ta yi kuka.
Na ce"me kike yi a nan?"
Ta ce"raka ka zan yi".
"Mu je" Na fad'a, ina yin inda motata take,muka shiga na ja muka bar gidan.
Mun fara tafiya na ce"Nabila ki dinga hak'uri da duk yanda k'addara ta zab'a miki,wani hanin ga Allah baiwa ne,sai ki ga kin samu wanda za ki so fiye da son da kike yi Abdul,ki dinga addu'a idan kika ji tunanin shi".
Kamar ba za ta ce komai ba,kusan minti biyu sannan ta ce"Ina jin zafi sosai a zuciyata,ban san ya zan yi ba Ni".
Na ce"na sani Nabila,amma idan kika rik'e addu'a za ki samu sassauci,babu abin da addu'a ta bari".
Ta ce"na rasa wanda nake so,kuma ba zan tab'a samun wani ba".
Na kalleta sai na ga ta kwantar da kanta a kujerar idonta a rufe.
Ina shirin yin magana,na ji ta ce"wacce kake so d'in sosai kake son ta ko? Idan ka rasa ta ya za ka ji?"
Nayi murmushi na girgiza kai na ce"daina yi min wannan fatan,ba zan ma rasa ta ba in sha Allah!"
Ta ce"Ni ma ban san zan rasa Abdul ba,na tab'a ce masa idan na mutu ya zai yi? Sai ya ce mini bakinsa ba zai iya furta yanayin da zai shiga ba,ashe ya san shi zai mutu ya bar Ni".
Daidai nan muka kawo inda za mu je,dan haka ban kula ta ba,na sauka na shiga wurin sai da magungunan,na siyo na dawo motar,muka juya,har kuma muka koma gida babu wanda ya sake magana a cikin mu,ban shiga gidan ba,na ba ta magungunan da bayanin yanda za ta sha,na d'auki hanyar shagon aski.
A ranar da daddare na je gidan su Khairi,sai ta dinga yi min dariya wai askin bai yi min kyau ba,irin dariyar da ban taba ganin tana yi ba,har na shagala da kallon ta,cike da burgewa.
Na ce"dan Allah kina so na?"
Sai ta saita kanta,tana had'e gira,ba ta ba Ni amsa ba".
Na kau da zancen muka ci gaba da fira. Muna zaune a k'ofar gidan mahaifinta ya zo zai shiga,na tashi na k'arasa na duk'a na gaishe shi,ya amsa babu yabo babu fallasa,ya ce"kai ne Saifullahi?"
Na ce"Ni ne Baba".
Ya ce"to idan aure ne ya kawo ka,kuma ka shirya ka turo manyanka,ba na son ayi ta shiririta".
Na ji gabana ya fad'i duk da ban san dalili ba. Na gyad'a kai na ce"zan yi magana da su in sha Allah! Na gode".
Ya shige,Ni kuma na koma inda muke,ina jin farin ciki da 'yar fargaba,dan ban yi zaton za a fara yi min maganar aure yanzu,na so mu k'ara samun shak'uwa da ita,saboda har lokacin ba ta tab'a furta tana so na ba.
Ina murmushi na zauna,ina kallon ta
Ta ce"na ga kamar kun yi magana".
Na ce"I! Baba ne ya ce ya ba Ni ke,sai d'aurin aure kawai".
"Ba wani,ban yarda ba". Ta fad'a tana hararata.
Na ce"wallahi ya ce na turo ayi maganar".
Ta ce"Ai ba shi yake nufin an ba ka ba dai,idan ka turo aka tambaye Ni na ce ba na so fa?"
Na ce"wai ke meye hakan? Sai ki yi ta wani waske min,kin san yanda mata suke bi na kuwa?"
Ta ce"to me ya hana ka auren su?"
Na ce"ke kad'ai nake so!".
"Kar ka sake yi min zancen su to". Ta fad'a tana tashi tsaye.
Na ce"to meye na ga kin tashi?"
Ta ce"sallayar nake jira,zan shiga ciki".
Nayi dariya na ce"Allah ya huci zuciyar saurauniyar kishi".
Tana hararata ta ce"Ni ba kishin ka nake ba".
Na tashi na ba ta sallayar,dan na san tun da ta tashi zai yi wuya ta zauna,muka yi sallama na tafi.
Kai tsaye d'akin Ummi na shiga,tana kallo na ta ce"kai kuma ka ga damar askin kenan".
Nayi murmushi ina shafa kan na ce"I,nayi d'azu".
Na zauna na kalmashe yatsuna,na sauke ajiyar zuciya.
Ta ce"lafiya?"
Na ce"k'alau Ummi! Dama yarinyar da nake so ce,a gidan su aka ce idan na shirya na turo".
Ummi ta ce"dama kana da wata da kake zuwa wurin ta ban sani ba?"
Na ce"I,mun d'an jima ma".
Ummi ta ce"wace ce? A ina take?"
Na ce"A Fage take,ta gama secondary".
Ummi tayi shiru,ba ta ce komai ba.
Na ce"dan Allah ki yi wa Abba magana,sai na kwatanta muku gidan,ba na so ya wuce cikin satin nan,saboda kar su ga kamar ba da gaske nake ba".
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Saifu ai Ni nayi zaton kun gama sasanta junanku da Nabila".
"Nabila!" Na fad'a ina zaro ido,duk da ban yi mamaki,dan duk 'yan'uwa na lura kallon masu son juna suke yi mana Ni da Nabila.
Na ce"Ni Ummi ai babu wani abu a tsakaninmu, ba son ta nake ba".
Ta ce"shisshige mata da kake yi,ku zauna kuyi ta fira,har ma ka d'auke ta ku fita yawon ku duka na meye?"
Na ce"Ummi Ni fa tausayin ta kawai nake yi,kuma na ga dai k'anwata ce,idan na fita da ita ko na zauna mun yi fira ba wani damuwa ba ne".
Ummi ta ce"Ai mu duka mun yi zaton soyayya kuke yi,kuma har mun yi magana da iyayenta,aka tambayi Nabila tana son ka,ta ce tana so,ka san abubuwan da suka faru da yarinyar,dan haka tun da tana son ka kawai ka aure ta, ka ajiye zancen wata a gefe".
Raina ya b'aci,na ce"Ummi Ni fa ba na son Nabila,daga taimako sai gada ta rufta da Ni? Sam ma Ni fa yarinyar ba kala ta ba ce,Ummul Khairi nake so,kuma ita d'aya zan aura,gaskiya ba na son wata Nabila".
Na tashi na fice daga d'akin cikin fushi.
A falo na ga yan gidan duka suna kallo,ban da Nabilar,na shiga d'akin su direct,na gan ta ta fito daga wanka kenan,na kauda kai,na ce"saka hijjabi Malama!"
Ta d'akko ta saka,ta zauna a bakin gado.
Ina had'e rai na ce"Nabila tun da muke da ke,na tab'a cewa ina son ki?"
Ta girgiza kai almar a'a.
Na ce"na tab'a nuna miki wata alama da za ki yi tunanin son ki nake".
Ta ce"I,kana nunawa".
Na k'ank'ance ido cike da b'acin rai na ce"me nake yi miki?"
Muryarta tana rawa,dan dama ba ta da hayaniya,ta ce"kulawa kake ba Ni,kuma kana tausayi na,duk abin da na ce ina so kana k'ok'arin sama min,kalaman kwantar da hankali kake yi min kullum,idan ba Ni da lafiya kana damuwa,kuma kana kula da Ni".
A tsawace na ce"wannan abun da nake yi miki duka ba na yi wa su Ramla? Matsayin ki d'aya da k'annena wanda muke uwa d'aya uba d'aya,ko su suka shiga halin da kika shiga irin wannan kulawar zan ba su,saboda haka ba son ki nake ba,ina da wacce nake so,yanzu ma zancen auren ta za a fara!".
Sai ta fara kuka har da shasshek'a.
Na danne tausayin ta dan kar ya yi tasiri a zuciyata Na ce"kin ji abin da ba fad'a miki? Ba na son ki!"
Ta gyad'a kai alamar ta ji.
Nayi tsaki,na bar d'akin ina jin raina a jagule.
Nabila sai ta fashe da kuka,ta kwanta tana ta yi babu k'akkautawa,har sai da suka gama kallon suka zo suka tarar da ita a wannan yanayin,suka sanarwa Ummi.
Ummi ta tambayi abin da yake damunta ta ce babu komai,ina tunanin ta zarge Ni ne,ta zo har d'akina ta ce"me ka yi wa Nabila?"
Na ce"me ta ce nayi mata?"
Ummi ta ce"me ka fad'a mata!? Ina tambayarka kana tambaya ta?"
Na ce"Ni fa kawai na fad'a mata ba na son ta ne".
Ummi ta ce"Saifullahi ka shiga hankali ka fa! Kana ganin yarinyar lallab'ata ake yi,shi ne za ka d'aga mata hankali? To sai ka aure ta,idan aka yi auren ka kashe ta ka ji!?"
Ta fice daga d'akin.
Ta koma wurin Nabila,ta janyo hannunta zuwa d'akinta,ta ce mata"Nabila Saifullahi kike so dai ke?"
Sai ta girgiza kai alamar a'a.
Ta ce"to me ya sa ki kuka?"
Nabila ta ce"babu komai Ummi,Yaya Saifu akwai wacce yake so,a k'yale shi kawai".
Ummi ta ce"kurari kawai ya yi miki,dole ya aure ki,gida bai k'oshi ba,ba za mu kai wa dawa ba!".
Washegari na tunkari Abba da zancen,sai ya ce na ba shi adireshin gidan su Khairi,zai sa ayi bincike, na ba shi,ina d'an jin sassauci tun da nayi tunanin shi zai goya mini baya,amma sai na ji shiru har sati d'aya bai sake yi min zancen ba,a lokacin kuma mahaifin Khairi ya ce min idan ban shirya ba,na daina zuwa,zai had'a ta da wanda zai aure ta.
*** [10/24, 3:47 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕