Mataccen buri

Page 3

by @sadiyaabdulrazak954

Jikina yayi sanyi,zuciyata kuma ta cika da tsoro,duk yanda na so na maze kar yanayina ya canza,sai na kasa,har Khairi ta fahimta,kuma ta tambaye Ni abin da Babanta ya ce mini,

Na sauke numfashi na ce"dama akwai wanda yake son ki bayan Ni?"

Ta ce"I! Akwai wani d'an'uwan mu,amma Ni ba zan aure shi ba wallahi!".

Na ce"ya ce idan ban shirya ba zai had'a ki da wani,nayi magana da Abbana,ba na son nayi ta maimaita masa ba,na san yana sane bai manta ba,amma dole yau zan sake tuna masa".

Sai ta fad'i maganar da ta sake tsorata Ni,tana kallon gefe ta ce"sun ce dole had'awa za a yi da na anti Maryam,nan da wata biyu kenan,dan Allah ka turo,zan iya auren kowa ban da wanda suke son had'a mu,saboda mahaukaci ne,mai magani ya ce sai ya auri buduruwa zai warke,shi ne kuma suke son na aure shi a hakan".

Gabana ya fad'i,na fara salati,a tsorace na ce"mahaukaci kuma! Wane irin hauka Khairi?"

Ta ce"I! Matsalar k'wak'walwa ce da shi,kana ganin shi ma za ka san ba shi da hankali,har juya kai yake fa yana zabura,ga shi ba shi da kirki,ko dariya ba ya yi".

"Na shiga uku! Daina fad'a min, ba zai faru ba,babu yanda za a yi na bari na rasa ki,gobe za a turo in sha Allah! Har rana za a tsayar,na shirya wata biyun in sha Allah!". Na fad'a ina jin wani yanayi a zuciyata

Ta ya ma za a d'auki yarinya kamar Khairi a magancewa wani k'aton namiji matsalar shi da ita? Idan ya kashe ta kafin ya samu lafiyar kuma fa,sai ma na fara zargin anya su suka haife ta kuwa? Haka dai na bar gidan jikina duka a sanyaye,zuciyata babu dad'i.

Kai tsaye b'angaren Abba na nufa,na samu Ummi a can,abinci yake ci dan haka na zauna bayan na gaishe su ina ta sauke numfashi.

Abba ya ce"Saifullahi lafiya kake kuwa?"

Dama jira nake,tun kafin ya rufe bakinsa na ce"A'a Abba! Ba na lafiya".

Ya ce"me yake damunka?"

Na ce"Abba akan maganar da muka yi,ka ce za ka yi bincike kuma na ji shiru,ga shi sun ce nan da wata biyu za su aurar da ita,kuma sun ce idan ban turo ba akwai wanda za su ba ta".

Abba ya ce"na saka an yi bincike,komai lafiya lau,amma sai Ummin ku ta yi min zancen Nabila,ashe da kuna soyayya,wai sai ka fasa ka ce ga wata,kuma ita Nabila ta ce kai take so,meye matsayin yaudarar da kake son yi mata?"

Na ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abba wallahi tallahi babu komai tsakanina da yarinyar nan,ban tab'a son ta ba!".

Ummi ta ce"ko hakan ne Saifullahi ka tausaya mata,ka aure ta,Ni dai a matsayina na mahaifiyarka ba na goyon bayan aurenka da wata a waje,Nabila na zab'a maka".

Abba ya d'aga mata hannu ya ce"A'a,ba a yin haka! Ko mace an daina yi mata haka,bare kuma namiji, idan mun tilasta ya aure ta,ita kanta ba za ta ji dad'in zama da shi ba,damuwar da ake son ta fita daga ciki, sai ta shiga wacce ta fi wacce take ciki".

Na jinjina kai ina jin sauk'i a zuciyata.

Ya kalle Ni ya ce"wata nawa suke so?"

Na ce"biyu ne,suna so a had'a da na yayarta ne".

Abba ya ce"kai d'in ka shirya dai ko?"

Da sauri na ce"I! A shirye nake".

Ya ce"ka sanar musu gobe da yamma in sha Allah za a tura,a saka rana".

Farin ciki ya rufe Ni,na ce"na gode Abba,Allah ya saka da alkairi,Allah ya k'ara girma!".

Abba ya yi murmushi ya amsa da amin,Ni kuma na tashi na fita ina kiran lambar Khairi,dan nayi mata albishir.

A inda ta saba zama na ganta,tana zaune akan d'aya daga cikin kujerun da suke barandar. Na katse kiran na mai da wayar aljihu,na ja kujera d'aya na zauna dab da ita ina fuskantar ta,sannan na kamo hannayenta duka biyun,ina kallon ta,sai ta sunkuyar da kai.

Na ce"Nabila!"

Ta ce"na'am!".

Na ce"wannan alfarma nake nema a wurin ki,dan girman Allah idan kin san kina so na,ki yi hak'uri ki cire,ki manta da Ni,saboda wallahi tallahi Ni Ummul khairi kad'ai nake so,kuma ko na aure ki ba za ki samu yanda kike so ba,Abba ya yarda gobe ma zai tura a saka ranar aurenmu wata biyu kacal! Ummi ce na lura ta dage ke ta fi so na aura,amma idan kika nuna ba kya so na,na san za ta sakko".

Sai ta fara hawaye,tana jinjina min kai.

Na share mata hawayen na ce"ko sosai kike so na?"

Ta girgiza min kai alamar a'a.

Sannan ta zare hannayenta,ta tashi ta shige ciki. Ni kuma na gyara zama na kira layin Khairi,na shaida mata gobe akwai bak'i,sai ta kasa b'oye farin cikinta,har ya bayyana k'arara a muryarta.

Nayi murmushin jin dad'i na ce"wallahi Saifullahi ya gama siye zuciyar wata yarinyar!".

Ta ce"babu wani! Ni ban ce ina son ka ba!".

Na ce"kuma kike murna dan kin ji zancen aurenmu?"

Ta ce"na ji zan aure ka,amma ban ce ina son ka ba".

Nayi dariya na ce"yarinya akwai ranar da za ki furta min ne".

Sai ta yi dariya ta katse kiran. Na kira Hafiz shi ma na fad'a masa,ya yi min murna,yana ta tsokanata da Angon Khairi,na tashi na shiga ciki ina jin zuciyata wasai,haka na kwana cike da farin ciki.

Washegari kuwa Abba ya cika mini alk'awari,aka kai kud'in aure gidan su Khairi,aka tsai da wata biyu,babu kwana hud'u ma a ciki,farin ciki ji nake kamar har an d'aura,tun a ranar na sa aka fara k'yalk'yale gidana,wanda na kwana biyu da ginawa,na so ganin fuskarta a ranar,amma sai ta dage wai kunya take ji,kar na so a ranar.

Washegari da yamma ina dawowa daga asibiti gidan su na wuce,muna tsaye a k'ofar gidan muna fira,ina ta tsokanarta da Amaryar Saifu,tana murmushi, wani ya tunkaro mu,sai na lura lokaci d'aya fara'ar fuskarta ta d'auke,kuma kamar ta cika da tsoro.

Kafin na tambaye ta,ta ce min"ka gan shi,shi ne fa wanda da suke son aura mini".

Na kalle shi,na ga fuskar shi babu alamun rahama,ya yi wani doro kana gani ka san na gadara ne da rashin mutunci,wallahi Ni kaina sai da zuciyata ta motsa.

Ya zo dab da mu ya tsaya,nayi ta maza na k'arasa na mik'a masa hannu da nufin muyi musabaha,sai yayi min wani mugun kallo,ya wani jujjuya kai,har na firgita,ya ja wani burki,ya shiga cikin gidan.

Na kalli Khairi,ina sai sauke numfashin tsoro take,duk da Ni ma fa na ji tsoron ganin yanayin ta bai hana Ni fara dariya ba. Sai idonta ya cika da k'walla,ta ce"wallahi tsoron Hamzan nan nake yi sosai!".

Na ce"wai da gaske da shi za a aura miki?"

Ta ce"Hmmm!"

Na ce"ya kuke da shi?"

Ta ce"d'an yayan Babana ne fa,wai sai ya auri buduruwa zai warke".

Na jinjina kai da mamaki na ce"wane kalar hauka ne yake damun shi da za ace aure ne magani? Wannan ai ganganci ne a d'auki yarinya k'amara mai hankali da nutsuwa irin ki a had'a da mahaukaci!".

Ta ce"to su dai sun ce ciwon shi ba na asibiti ba ne,kuma ya k'i kula kowace mace bare ya yi auren!".

Na ce"To Khairi wace za ta auri mahaukaci tana sane?"

Ta ce"amma da aka ce masa ga Ni,ai ya ce yana so na! Suka ce na aure shi,tun da korar samarina nake yi".

Nayi murmushi Na ce"ki bar tsoro,babu yanda za a yi ki auri mahaukaci,ke matata ce in sha Allah!".

Ta ce"Allah ya sa".

Na ce"ashe kina so na!"

Ta harare Ni ta ce"Ni fa ina nufin Allah ya sa ba shi zai aure Ni ba".

Na ce"to tun da ba kya so na,bari na janye kawai".

Sai ta juya za ta shige gida.

Na ce"Allah ya ba ki hak'uri!".

Dab da magriba na tafi,kuma har lokacin Hamza bai fito daga gidan ba.

A ranar na yi wa Ummi zancen had'a kayan lefe,sai ta yi kamar ma ba ta ji Ni ba,hakan ya tabbatar mini har lokacin ba ta karb'i aurenmu da Khairi ba,washegari na shirya na tafi gidan yayarta,na sanar mata halin da ake ciki,ta yankar min kud'in da za su isa ta had'a min lefe,nayi mata transfer nan take ina jin farin ciki,cikin sati biyu kuwa ta gama had'a lefe,ta kwaso akwatuna ta kawo gidanmu.

Hmmm! Shegiyar yarinyar nan Nabila ashe ba ta hak'ura da so na ba,wannan akwatuna da ta gani shi ya k'ara firgita ta,a ranar dinga kuka har zazzab'i ya rufeta,Ummi ta kira Ni nayi mata allura,na ba ta magani,ko sannu ban yi mata ba,kamar yanda na saba,saboda sosai nake son yarinyar ta gane ba na son ta,kuma ba zan so ta ba.

Kwana uku tana kwance,ranar na hud'un ina asibiti sai ga ta an kawo ta,wai jikinta ya matsala,babu wanda ya zauna a asibitin suka ce Ni zan kula da ita,fuskata babu walwala na jona mata ruwa,nayi mata allura,na koma office d'ina,ina ta waya da Khairi cikin farin ciki.

Da yamma da zan tashi daga aiki,na tarar tana bacci,na tashe ta fuska a had'e na ce"Malama tashi haka,mu tafi gida!".

Tana labgwab'ewa ta ce"jikina babu k'arfi,kuma yunwa nake ji".

Na ja tsaki ina danne tausayin ta,na ce"dalla tashi mu wuce! Wahala ce kika siya da kud'inki,dan haka ke kad'ai za ki cinyeta!".

Ban yi zaton za ta yi magana ba,sai na ji ta ce"Yaya Saifu,Ni ba dan kai nake rashin lafiya ba,tun da har ka nuna min k'yama ai ka san dole zan kama kaina!"

Nayi tsayi ban ce komai ba,ita kuma ta sakko tana dafa bango ta fito,na jima a mota sannan ta k'araso saboda na lura da gaske jikinta babu k'wari,ta shiga motar na ja muka kama hanyar gida.

Muna komawa Ummi ta rufe Ni da fad'a wai na d'akko ta ba ta warke ba.

Na ce"to Ummi wani me kuke nufi da Ni zan yi jinyarta!? Kalli fa layi take kamar 'yar maye Ni zan ta rik'eta ne? Ai bai kamata ba".

Ummi ta ce"lokacin da kake rik'e ta din ka manta bai kamata ba? Saifullahi wallahi idan nayi niyya sai ka auri yarinyar nan dole!".

Na zauna ina dafe kaina.

Ita kuma ta ja Nabila suka shiga d'akinta.

A ranar da za a kai kayan lefe,lokacin saura sati hud'u auren,sai jikin Nabila ya matsa sosai,Ni kaina sai da na tsorata,yarinya tana gadon asibiti an yi mata allurar bacci ta kasa baccin sai sauke ajiyar zuciya take yi,tana d'ago k'irji kamar za ta mutu,kuma tambayar duniya an yi mata ta k'i magana sai kuka take yi,an ce ko Ni take so,ta ce a'a.

Haka dai aka fasa kai kayan a ranar aka zauna jinyarta.

*** [10/26, 10:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕