Page 4
Sai da Nabila tayi sati a asibiti, lokacin bikinmu saura sati uku,dan haka na tunkari Ummi da zancen Ni dai gaskiya a je a kai kayan aurena,lokaci yana k'urewa,haka dai suka kai duk ransu ba son auren yake ba,Nabila kuma washegarin ranar jikinta yayi sauk'i,aka sallameta,sai ta ce ita gidansu za ta koma,hakan ya yi mini dad'i sosai,dan ba na son ganin yarinyar saboda kar na ji tausayinta.
Muka sake samun shak'uwa da Khairi,duk da har lokacin ita fa tana nan akan bakanta,wai ba so na take yi ba,duk wani shiri da ya kamata mun kammala shi,sai jiran ranar aure,wanda nake jin kamar ba za ta zo ba,ga shi a cikin satuttukan kamar an rib'anya min k'aunar Khairi,wallahi idan idan tunanin ta sai na ji kamar wuta aka kunna a zuciyata, dan idan a kwance nake sai na tashi zaune ina sauke numfashi,shi ya sa komai dare ba na jin shakkar kiranta,idan ta d'auka na ji muryarta sai na ji sassauci,idan na fad'a mata halin da nake ciki sai ta yi min dariyarta, wacce nake jin ta fi miliyan d'aya daraja a wurina.
Watarana kwatsam Nabila ta kira Ni a waya,na katse na kira ta,bayan ta gaishe Ni nayi mata ya jiki,ta amsa,sai muka yi shiru na 'yan sakanni,har ina shirin yanke wayar sai na ji shasshek'ar kukanta,ta ce"Brother!".
Idan muna yanayin shauki ne kawai take ce min brother,ta fi ce min yaya Saifu.
Na ce"Sister ya aka yi?"
Ta ce"saura sati nawa?"
Na san abin da take nufi,dan haka kai tsaye na ce"saura kwana tara".
Ta sauke numfashi ta ce"Allah ya sanya alkairi!".
Na ce"Amin! Yaushe za ki dawo gidanmu?"
Ta ce"sai satin bikin".
Na ce"Allah ya nuna mana". Na katse kiran
Washegari kuma Ummi ta ce min,na je na duba Nabila wai ba ta da lafiya, na ce to,ba dan ina da niyyar zuwan ba,sai da ta jera kwana uku tana maimaita min,amma ban je d'in ba.
Satin aurenmu ne ya zama satin canza komai na rayuwata ko na ce rayuwarmu Ni da Khairi,lokacin saura kwana biywr auren,kwatsam sai Khairi ta kira Ni tana kuka,hankalina ya tashi a firgice nake tambayarta
Sai ta ce"Saifullahi ka san ba ka shirya aurena me ya sa ka saka min rai?"
Na tashi tsaye da mugun mamaki na ce"me ya faru? Waye ya ce miki ban shirya aurenki ba!?"
Ta ajiye shasshek'ar kuka ta ce"ya za a yi ka ce a d'aga,bayan na fad'a maka sun ce dole had'awa za a yi?"
Na ce"Ni fa ban fahimci komai a maganganun ki ba! Ki yi min bayani".
Kawai sai ta katse kiran.
Na fito daga asibiti,ina shirin d'aukar hanyar gidan su,sai ga kiran Abba,na d'aga ya ce na zo gida yanzu yana son ganina,ya katse ba tare da ya jira cewata ba. Ba na jin zan iya juyawa na koma gidan,bayan na san Khairi tana can tana kuka,dan haka na k'arasa gidan,gabana sai fad'uwa yake yi,na kira wayarta ta k'i dagawa.
Nayi mata gajeren sak'o na ce ina k'ofar gidansu.
Sai Maryam ta fito,yanayinta ya nuna ita ma tana fushi da Ni,ta gaishe Ni sama-sama,sannan na ce"Ina take, me ya faru?"
Kafin ta ba Ni amsa,na ga Abba ya sake kira na,ban d'aga ba,dan na fi damuwa da jin halin da ake ciki.
Maryam ta ce"Saifullahi me ya sa ka yi hakan? Khairi ta ce a shirye kake,kuma yanzu 'yan gidanku sun zo sun karb'e kayan lefe,wai ba ka shirya ba,aure sai an sake saka sabuwar rana".
Tun da ta fara magana na daskare,sai da ta dire na d'auki furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Raina ya kai k'ololuwar b'aci,na ce"wallahi Maryam ban san komai game da wannan abun ba,meye shirin wallahi a shirye nake,amma na san inda matsalar take,bari na je gidan yanzu zan dawo,ki ba ta hak'uri dan Allah! Wallahi za a yi auren nan,ba za a d'aga ba!".
A sanyaye ta amsa min da to,sannan ta shige gida,Ni kuma na shiga mota na tafi gida a guje.
Da sassarfa na k'arasa sashen Abba,zuciyata tayi min tsaye a k'irji,na shiga da sallama muryata har rawa take na ce"Abba me ya sa za a yi min haka?"
Abba ya ce"zauna".
Na ce"A'a Abba ba sai na zauna ba!".
Ya ce"zauna Saifullahi!".
Na zauna ina shirin yin magana ya d'aga min hannu.
Nayi shiru ina ajiye numfashi.
Ya ce"na san zuciyarka ba ta yi maka dad'i,na san mun yi maka ba daidai ba,amma da farko ka yi hak'uri ka saka dangana a zuciyarka,Saifullahi ba hana ka auren wacce kake so za mu yi ba,mun dai yanke shawarar d'aga auren ne,ka hak'ura sai nan da wata uku masu zuwa,in sha Allah za ka aureta!"
Na kalle shi a razane na ce"haba Abba! Me ya sa?"
Ya ce"ka nutsu ka fahimce mu duka..."
Na girgiza masa kai alamar ba zan fahimta ba,na katse shi da fad'in "Abba ku je ku mai da kayan auren nan,ku sanar musu yana nan a yanda yake,sai na fahimci komai".
Ya ce"Saifullahi tun farko na ce ka yi hak'uri! Ban san abubuwan da suke faruwa ba,sai jiya Umminku take fad'a min,ita k'anwarka Nabila ta ce kai take so,kuma tana can kwance a wani hali saboda kai,idan ka fasa auren nan watak'il babu wani hali da yarinyar za ta shiga,amma ita kuma 'yar'uwarka ta zurfafa,kuma ka sani Allah ne ya d'ora mata lalurar son ka,za ta iya rasa ranta saboda kai,idan ta mutu da wane ido za ka kalli mahaifanta da kuma sauran dangi? Ka san Allah zai iya yi muku hisabi? Tun da tun farko kai ka nuna kana son ta,yanzu idan ka fasa ka cutar da ita".
Zuciyata ta dinga tafasa,na ce"amma Abba..."
Ya d'aga min hannu ya ce"kar ka ce komai! Mahaifiyarta ce ta zo ta duk'a ta rok'e Ni alfarma,kuma nayi mata,saboda haka Nabila za ka aura nan da kwana biyar in sha Allah! Ita kuma wacce kake so d'in ka yi hak'uri har sai Nabila ta samu lafiya".
Na tashi tsaye ina girgiza kai na ce"A'a! Wallahi a'a,ba zan iya ba,ba zan aureta ba! Tabb!".
Na fice daga d'akin cikin fushi sosai, ina ji yana kira na ban juyo ba,na shiga d'akin Ummi kai tsaye sai huci nake yi,sai na tarar ba ta nan,na shiga d'akin k'anne na,na tambaye su suka fad'a min tana asibiti wurin Nabila,na d'auki d'aya muka tafi asibitin tare,ina jin kamar nayi tsuntsuwa na gan Ni a gaban Nabila. Tana nuna min d'akin na shiga kai tsaye,ba tare da na bi ta kan su Ummi dake zaune a gefe suke yi min magana ba,na tura k'ofar na shiga,na sameta tana bacci,na shiga tashin ta,tare da kiran sunanta a mugun fusace. Ta bud'e idonta mai cike da bacci,na d'agata na zaunar,jire ya kwasheta za ta koma,na rik'e kafad'unta,ina yi mata mugun kallo na ce"Ni dai kike so ko!?"
Sai ta fashe da kuka tana girgiza min kai alamar a'a.
Na hankad'ata ta koma ta kwanta na ce"wallahi Nabila idan kika yarda aka fasa aurena saboda ke sai kin yi nadama..."
Ban kai k'arshe ba,Ummi da mahaifiyar Nabila suka shigo.
Da hargagai kamar zan fad'a kanta na ce"muddin kika aure Ni,sai kin tsane Ni! Saboda ni Ummul-khairi kad'ai nake so kuma ita ce matata,wallahi da ki yarda ki aure Ni gara ma ki mutu tun yanzu!".
Ummi ta k'araso ta wanke Ni da mari, ko zafin marin ma ban ji ba,saboda zafin da zuciyata take yi min ba zai bawa k'wakwalwata damar aiki ba,bare har ta fahimci an dake Ni.
Na ce"Ummi me ya sa za ku yi min haka? Idan tausayin wannan yarinyar kuke yi,Ni ma ai mutum ne sai ku duba halin da zan shiga,ku duba halin da Khairi za ta shiga,za ku mai da kanku k'ananun mutane fa!".
Ta ce"ba za mu duba ba! Kai wane irin mara kunya ne Saifullahi!? Ko mutuwa tana tsoron idon mahaifi,a gaban mahaifiyarta kake yin wannan furucin,saboda wata banzar 'yar talakawa wacce a 'yar aikin gidanmu ya dace ta zo,ba suruka ba!".
Na ce"Ummi ko gidan su sun fi kowa talauci a duniya ita na zab'a akan Nabila!".
Ummi za ta sake marina mahaifiyar Nabila ta tare,tana hawaye.
Ummi ta ce"da mun yi niyyar a d'aga auren ne,amma tun da kake iya kallona ina matsayin mahaifiyarka kake min wannan furucin wallahi an janye auren wannan yarinyar, har abada ba za ka aureta ba,kuma aure da Nabila a yau za a d'aura shi,yau din kuma sa ta tare,ba sai gobe ba!".
Ban san lokacin da murmushin takaici ya kufce min ba,na kalli Nabila da take ta rusar kuka daga kwance,na ce"congratulations!".
Har na juya zan fita na ji ta sake fashewa da kuka ta ce"Ummi na fasa,Ni ba na son shi,na fasa!".
Na jinjina kai na fice a fusace,ina jin wani kalar yanayi da ba zan iya misalta shi ba. Haka na koma gida ina tafe ina sauke numfashi, amma har lokacin ban yarda da gaske zan rasa Khairi ba,nayi wanka na kwanta ina ta huci har aka kira sallar magriba,na tashi nayi,sannan na fito na tafi gidab yayar Ummi,wacce nake zaton ita kad'ai ce za ta goya min baya. Amma da na je ita ma sai na samu tana bayan su,ta fara yi min kalaman kwantar da hankali wai na hak'ura da Khairi,ban ma gama sauraronta ba,na fice daga gidan na d'auki hanyar gidansu Kahiri,wai na ganta ko zan ji sassauci.
Na dinga kiranta ba ta d'agawa,na aika yaro ana sallama da ita,sai ta k'i fitowa. Na kai awa d'aya a k'ofar gidan,dan har sallar isha'i anan nayi,sai ga mahaifinta ya zo shiga gidan.
Na karasa da sauri na duka na gaishe shi.
Sai ya amsa min kamar ran shi a b'ace yake,ya ce"lafiya dai ko?"
Na ce"Baba dan Allah kuyi hak'uri da abin da ya faru,babu sani na suka yanke hukunci,ba za a d'aga ba in sha Allah!".
Baba ya ce"Saifullahi ai Ummulkhairi ba za ta rasa mijin aure ba,iyayenka sun ce 'yar'uwarka suka zab'a maka,dan haka mu ma za mu aura mata d'an'uwanta,dama can shi ne zab'inmu,Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi!".
Na ce"Baba ba haka ba ne wallahi! Ko ba za ku ba Ni ba dan Allah kar ku had'a ta da wanda bai dace da ita ba!".
Baba ya shige gida bai ce min komai ba. Sai na kasa tafiya,haka nayi zaune ina jin kamar za ta fito,har sha d'aya na dare ta yi ban ankara ba,na tashi na tafi ina jin sanyin zazzab'i yana shiga gab'ob'ina. Ranar ban yi bacci ba,na kirata ya fi sau talatin kafin ta kashe wayarta,ta bar Ni da zafin zuciya.
Sai da nayi sallar asuba sannan baccin ya d'auke Ni,k'arfe takwas na tashi,sai na ga ta kira Ni har sau uku,na kirata hannuna har karkarwa yake yi,ta d'aga muryarta na rawa ta ce"dan Allah kar ka fasa aure na! Mahaukaci ne fa,shi za su aura min!".
Na girgiza mata kai kamar tana gani na,na ce"A'a Khairi ke ba MATAR MAHAUKACI bace!"
(Littafin Mrs Sadauki)
Sai ta fara kuka sosai.
Na ce"ki kwantar da hankalinki,yanzu zan zo ki fito dan Allah!".
Ta ce"an hana Ni kula ka!"
Na ce"ki fito dan Allah! Sai mu yi magana a nutse,kuma ki daina kuka na fi ki jin ciwo".
Ta ce"to,zan jira ka a shagon Hafiz,kar ka zo gidanmu!".
Na katse wayar,nayi wanka a gurguje na fito zan tafi,na gaida Ummi ba ta kalle Ni ba ta ce"ka je ka duba matarka kuma ka ba wa mahaifiyar ta hak'uri!".
"Matata!?" Na tambaya da mamaki.
*** [10/30, 10:33 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕