Page 5
Ummi ta ce"I! Yau muka yanke za a d'aura aurenku in sha Allah!".
Sai nayi murmushi kawai,na jinjina kai na fice daga gidan.
Ina hanya ta kira ni ta ce ta je shagon Hafiz a kulle, sai na kira shi na ce maza ya fito ya bud'e shago,kafin na je kuwa ya bud'e, na same ta zaune a cikin shagon,shi kuma yana k'ofa,na shiga na zauna,ina kallon yanda take goge hawaye, zuciyata na raya mini shi kenan na rasa kyakkyawar yarinyar nan, mai hankali da nutsuwa. Na sauke numfashi na matsa dab da ita na ce"Khairi ki daina kukan haka, addu'a ya kamata a ce kina yi a daidai wannan lokacin, kuma a tunani na idan kika bijere dole za su rabu da ke,ki ce ni kike so dan Allah! Ba zan jure rashin ki ba, na fi ki shiga matsala fa,ni zancen aurena suke yi da k'anwata Nabila wai a yau za a d'aura, to dame zan ji? Rashin ki ko auren wacce ba na so? Don Allah ki bar kuka,sai kin so za ki auri mahaukacin, wuk'a da nama ne a hannunki,ki bijire!".
Sai ta girgiza mini kai alamar ba ta yarda ba,ta ce"Saifullahi ban tab'a sab'awa iyayena ba, ba zan fara ta sanadinka ba,idan na yi hakan iyayena za su tsaneka ko ka aure ni,bare kuma ba ni da tabbacin za ka aure ni d'in,tun da za ka auri 'yar'uwarka,ina tsoron butulcin maza".
Na rik'o hannunta sai ta k'wace,na ce Khairi kar ki sake saka ni a jerin wancen mazan, ba na daga cikin su wallahi, ki saka a ranki ina tare da ke duk nisan zamani,zan jira har lokacin da iyayenmu za su amince da auren nan,matsalar tana wurin ki!".
Ta share hawaye ta ce"saura kwana hud'u komai ya shud'e,zai fi ni da kai mu d'auki k'addara,ka auri 'yar'uwarka,ni kuma ka dinga saka ni cikin addu'a Allah ya sa kar na cutu ta sanadin auren Hamza".
Ta tashi za ta fita,na tare hanyar ina kallon cikin idanunta,sai ta kau da kai, tana share hawaye.
Na ce"dama can ba so na kike yi ba Khairi,na san wannan,tun da ba ki tab'a furta kina so na ba,da akwai so ina da tabbacin za ki bijere!".
Ta kalle ni na 'yan sakanni,sai ta fad'a mini maganar da ta rage min rad'ad'in da nake ji a zuciyata,ta ce"Ina son ka tun ranar da na fara ganinka a shagon nan,ka burge ni tun kafin na san za ka so ni,kuma na furta maka kalmar ina son ka cikin zuciyata ya fi a k'irga".
Na yi wani murmushi na ce"na gode,mu je na ajiye ki a gida ".
Ta ce a'a za ta tafi ita kad'ai,haka ta tafi ta bar ni zaune kamar an d'aure ni,ban san hawaye nake yi ba sai da na ji hannun Hafiz a kan fuskata tare da furucin shi ya ce"Abokina ba girmanka ba ne yi wa soyayya kuka".
Na share hawayen na ce" Hafiz ba ka san yanda nake ji ba,shi ya sa ka yi zaton ana girma akan lamarin so,ashe mafarkina duka na k'arya ne,ashe burina akan Khairi matacce ne!".
Hafiz ya ce"Allah ya zab'a maka mafi alkhairi,kuma a shawarce kar ka kyamaci 'yar'uwarka in sha Allah haske ce a rayuwarka".
Na girgiza kai na ce"Hafiz babu son Nabila a zuciyata, kuma ba na jin zan iya koyawa kaina son wata bayan Khairi,saboda na lura ba a koyon so,so shi ne yake yin kan shi,kuma yana da tsawon rai,ba ya tab'a mutuwa duk runtsi,kayi min addu'a Allah ya ba ni ikon jurewa!".
Hafiz ya ce"haka ne! Allah ya muku zab'in alkhairi ku duka. K'arfe nawa ne d'aurin auren?"
Na yi wani tsaki mai aji,na ce"babu shi fa! Wallahi muddin aka yi auren nan yau sai an samu matsala,ji nake kamar zan iya shak'eta ta mutu".
Hafiz ya yi murmushi ya ce"ka bi komai a hankali dai,watak'il wacce kake k'i ita ce alkhairin ka".
A shagon na wuni,sallah ce take fitar da mu,ko ruwa na kasa sakawa cikina,kuma na kashe wayoyina saboda kar a neme ni,sai bayan magriba na koma gidan ina jin yanda zazzab'i ya fara shiga ta a nutse.
A falo na tarar da duka 'yan gidan har ma da wasu cikin 'yan'uwan mu,na gaishe su sama-sama na shige d'aki,babu jimawa Abba ya kira ni,na je na zauna ina jin kamar nayi ta masa kuka ko zai fahimci halin da nake ciki.
Ya ce"Saifullahi ina ka je tun safe,ka kashe wayarka kuma,bayan an sanar maka yau d'aurin auren ka? " Na ce"Abba ni na yarda zan auri Nabila,amma don Allah ku ajiye zancen a gefe har sai na dawo cikin hayyacina,yanzu idan na yi aure ai sai iyayen Khairi su ce dama can shi ne dalili na na fasa aurenta,ku yi min adalci!". Na k'arasa kamar zan yi kuka
Abba ya ce"babu aure a tsakanin ka da yarinyar da kake so tun asali,shi ya sa Allah ya canza lamarin da k'anwarka".
Na ce"ku dai kuka canza! Kuke son kashe mini buri"
Abba ya ce"Saifullahi gobe k'arfe tara na safe za a d'aura aurenka da Nabila in sha Allah! Don mun gama sanarwa kowa,saboda haka wajibi ka san abin da kake yi,goben ka halarci daurin auren ka!"
Na ce"Abba ko ba na nan za ku iya d'aurawa".
Na tashi cikin fushi,ina ji yana kira na ban ko juyo ba,bare na dawo d'in.
Kai tsaye d'akina na koma na d'auki mukullin babur na tafi gidan su Nabila,zuciyata sai zafi take yi.
A tsakar gidan na tsaya na kira ta a waya,na ce ta fito ina jiranta,babu jimawa ta fito sanye da hijjabin ta,kanta a k'asa ta gaishe ni,ba tare da na amsa ba,ina yi mata wani bahagon kallo mai cike da tsantsar k'iyayya na ce"Nabila kin san gobe za su daura auren mu?"
Ta gyad'a mini kai alamar ta sani.
Na ce"kina ta farin ciki ne ko akasin haka?"
Ta ce"ni ma ban sani ba".
Na ce"za ki sani daga baya! Na zo na tabbatar miki ne wannan auren ba na farin ciki da shi,ina bak'in cikin zamowar ki matata,saboda ba na son ki,ba kya cikin ra'ayina,Khairi ce yarinya d'aya da nake so duk duniya,kuma ta sanadin ki na rasa ta,saboda haka zan ta tsanar ki har abada!".
Ta fara kuka sosai wanda na lura ba ya yi mata wuya,ta ce"ka yi hak'uri Yaya,ni ban ce sai kai zan aura ba wallahi,na san ina son ka,amma zan iya d'aukar k'addarar rashin ka,tun da na rasa Abdul har abada,kai ne kacal namijin da na ji zan iya rayuwa da shi,amma tun ranar da ka fad'a min ba ka so na na hak'ura, ni ba zan yi musu k'aryar rashin lafiya ba,son ka ne yake kwantar da ni,amma ban ce sai dole ka aure ni zan rayu ba,suna jin tausayi na ne shi ya sa".
Na yi murmushi na ce "ai hakan ya yi daidai! Amma ki sanar musu su adana tausayin su,dan ba ki ga komai na k'uncin rayuwa ba,sai daga baya".
Na juya na yi tafiya ta,na bar ta tana ta kuka.
Ina komawa gida Ummi ta tare ni da fad'a,wai me na je na fad'awa Nabila? Na ce mata babu komai,ta buk'aci mukullan gidana,na d'akko na bata.
Na je na kwanta ina ta kiran Ummul-khairi ba ta d'agawa,k'arshe ma sai ta saka ni a blacklist, kuma daga ranar wayarta ba ta sake shiga ba har sai ranar da ta nemi wani taimako na...
Washegari ban fita ko'ina ba tun asuba,takwas Hafiz ya zo gidan mu, shi da wani abokin mu,ina kwance ina fama da zazzab'i, kuma na k'i cin komai bare na sha magani,suna ta kwantar mini da hankali da ba ni shawarar na karb'i Nabila hannu biyu-biyu,ni kuwa ina jin zancen su kamar wata wak'a,haka dai suka tisa ni gaba har na shirya,k'arfe tara muka tafi gidan su Nabila aka d'aura aurena da tsirarun mutane, don wanda suka zama dole kawai aka sanarwa,kuma a ranar suka ce an gama jera kayanta,kuma a ranar za ta tare. Sai na dinga jin abun kamar almara,wai ni ne na auri Nabila,kuma za mu kwana gida d'aya da ita,wannan abun takaici ne babba a wurina.
Da na canza layi na kira Khairi tana jin muryata ta katse,haka na bi ta da sak'on ina son ta har abada, na kasa sanar mata an d'aura aure na.
Tun bayan sallar la'asar na ji an ce an kai Nabila,bayan issha'i Ummi da Abba suka tisa ni a gaba da fad'a, da nasiha kan na yi wa k'anwata adalci,amma sam ban d'auki zancen su,na dai saurara ne kawai tun da ya zama dole, haka na tashi na had'a wasu daga cikin kayana a jaka na bar gidan ina tunanin ta inda zan fara nunawa Nabila kuskuren shiga rayuwata.
*** [11/1, 3:17 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕