Mataccen buri

Page 6

by @sadiyaabdulrazak954

A slow na dinga jan motar kamar ba ni da wurin zuwa,da na k'arasa sai na tsinci kaina da kasa shiga cikin gidan, na dinga fitar da numfashin bak'in ciki, ina jin ina ma a ce Khairi zan shiga na tarar a matsayin amaryata ba Nabila ba, amma komai ya riga ya faru, na fi minti talatin a cikin mota kafin zuciyata ta ba ni shawarar kar na shiga gidan, gara na kwana a waje, na d'auki shawarar zuciyata, na ja motar a slow na je na kama hotel karo na farko a rayuwata, ashe na je gida kenan, zan ta zuwa ne har sau babu adadi. A can na sha ruwan shayi, na ci abinci mara nauyi, na sha maganin da yake cikin motata, na kwanta ba dan ina saka ran baccin zai ba ni had'in kai ba, haka na raba dare ina kiran Khairi wayarta ba ta shiga, zuciyata kamar za ta k'one saboda bak'in ciki, sai dab da asuba na samu bacci hakan ya tilasta mini makara,k'arfe bakwai na tashi nayi sallah, sai kuma na ga me ma nake yi a wurin? Ai gara na je tun yau na fara nuna wa Nabila kuskurenta.

Na tashi na fito,ina tsaye a wurin ajiye motoci ina amsar wayar Ummi, da take tambaya ta ya Nabila ta kwana,na ga wata matashiya ta zo ta zo ta tsaya a gefena, sai kallo take, nayi mata kallo d'aya na d'auke kai, dan ni mace idan ba mai kyau ba ce ko burge ni ba ta yi. Har na gama wayar na fara neman layin Hafiz still tana tsaye tana kallo na, sai na kalle ta ina had'e gira na ce"ya dai!?"

Ta yi wani farr da ido kamar 'yar tsana kafin ta fara magana da wata siririyar murya kamar ta jarirai ta ce"jira nake ka matsa,motata tana bayan taka".

"Ok!" Kawai na ce, na shiga motar da niyyar na ja na tafi, sai ta zo ta k'wank'wasa mini glass d'in, na zuge na ce"lafiya?"

Ta yi murmushi ta ce"k'alau! Sunana Siyama kai kuma fa?"

Na ja tsaki kawai, na ja motata na tafi.

Wannan karon sauri na dinga yi,saboda Ummi ta sanar mini za ta aiko a kawo mana abinci, na shiga gidan babu shakkar komai sai damuwar da ta kasa b'oyuwa a kan fuskata. Zaune a falo na tarar da ita, tana danne-danne a waya, ta ci kwalliya kamar ba ita a ka ce tana jinya ba,ta kalle ni tana daburcewa ta ce"Yaya ina kwana!".

Na nayi mata wani mugun kallo,mai cike da gargad'i,sannan na jinjina kai,nayi k'wafa,na bud'e d'akin da na sanar musu shi ne nawa, na shiga,ina kallon yanda suka k'awata shi, baki na tab'e na zauna a bakin gadon na dafe kaina da hannaye biyu ina tunanin kalar zaman da za mu yi da yarinyar, ina jin lokacin da aka yi nocking alamar mai kawo abincin ya k'araso,amma ban motsa ba, sai ta turo k'ofar ta shigo, cikin yanayin ta na sanyi ta ce"Yaya ana nocking!".

Nayi kamar ban ji ta ba. Sai ta koma ta bud'e, babu jimawa ta dawo tana sosa kai ta ce"ga abinci can, ko a kawo maka nan?"

Na d'ago daga kallon wayata da nake, na ce"Nabila! Zan yi miki gargad'i, idan har kina so ki tsira da mutuncin ki a idona ki fita daga harka ta, ni ba sa'an auren ki ba ne kin sani, bare ki yi zaton zaman aure za mu yi, ki kama kan ki da shiga harkata, kina da lambata duk wani abu da kike buk'ata wanda yake hakkina ne, ki yi min tex massage, dan ko muryar ki b'ata min take".

Tana tsaye tana kallo na har na kai k'arshe ba ta motsa ba,sai hawayen da suka fara zubar mata.

Na ce"idan kin fahimta ba ni wuri, kin tare mini iska!"

Ta juya ta fita, ni kuma na yi tsaki na tashi na yi wanka na tafi wurin aiki.

A waje na ci abincin rana har na dare, sai k'arfe goma na koma gidan, na tarar da ita zaune a falo cikin shirin kayan bacci, tana kallon TV, na had'iyi yawu ina had'e rai na ce"ke! Idan kin ji alamun dawowa ta ki dinga shigewa d'aki!".

A sanyaye ta ce"to!".

Na shige d'akina,ina fitowa daga wanka sai na ga yarinya zauna a cikin d'akin, a fusace na ce"me kuma kike nema?"

Tana kallon gefe ta ce"Ummi ce ta ce na dinga kwana a nan".

Na ja tsaki ban tanka ta ba,har na gama shirina na kwanta tana wurin a zaune, na kira wayar Khairi ba ta shiga still, sai na nemo hutunan ta na tisa su a gaba,har na fara jin bacci, na sakko daga gadon, na kashe hasken d'akin na kwanta.

Sai tsakar dare na farka na danna wayata,sai na gan ta kwance a k'asan carpet tana bacci, sai dai ta d'auki filon kusa da nawa ta yi matashi, na ci gaba da bacci na. Washegari kuwa da na tafi masallaci da asuba ban dawo na tarar da ita a d'akin ba.

Da alama ba ta da taurin kai, za ta ji magana, don ko gaishe ni ba ta yi ba da safe, bare ta yi mini tayin abinci, ranar ma sai dare na dawo, kuma na tarar da ita a d'akina kwance a kan carpet, amma yau ta shimfid'a bargo, idonta a rufe, na yi zaton bacci take, sai na tsaya ina ta kallon ta, ido ba a yi masa shamaki, zuciyata ce take k'in ta, ita gangar jiki babu ruwan ta da k'iyayya, dan haka idan na ce ban ji sauyin yanayi ba na yi k'arya, ban ankara ba ta bud'e ido, mu ka yi four eyes, sai ta juya min baya, ni kuma na yi tsaki na shiga wanka.

Ina sane da ranar auren Khairi, kuma na ci burin zuwa, idan Allah ya sa ina da rabo na samu nasarar yi mata kallon k'arshe, don haka tun safe na shirya, na je gidan su Hafiz don ya yi mini rakiya, haka ya dinga nuna mini wannan ba komai ba ne, na d'auki k'addara kawai, na ce masa na d'auka, a kan idona aka d'aura auren Khairi da wanda ba ta so, na dinga kallon shi, duk a hargitse babu wani annuri a fuskar shi kamar ba ango ba, mun jima a layin, ban ga Khairi ta fito ba.

Ashe dai tsautsayi ne ya zaunar da ni.

Muna zaune da Hafiz, yana ta yi min surutu ni kuwa hankali na ya na kan matan da suke ta kai kawo a layin, wasu kyawawa wasu akasin haka, kwatsam na hango wata yarinya mai kama da Khairi ta zo za ta wuce ta kusa da mu, sai da ma na kalle ta sosai sannan na tabbatar ba Khairin ba ce, dan Khari ta girme ta, na tab'a Hafiz ina nuna masa ita.

Ya ce"ai wannan 'yar'uwar su ce,tana yawan zuwa gidan".

"Su na kama sosai!" Na fad'a hankali na yana kanta.

Tana zuwa dab da mu,na mik'e tsaye, sai Hafiz ya zaunar da ni ya ce"don Allah Saifullahi ka dinga kama kanka!".

Na ja tsaki, na fizge na bi bayanta.

"Hi!" Na fad'a bayan na kai dab da ita.

Ta juyo ta kalle ni,ta ce"sannu".

Na yi murmushi na ce"yawwa".

Ta ci gaba da tafiya, ni ma na mara mata baya,don na rasa me zan ce mata kuma.

Ta tsaya ta ce"lafiya kuwa?"

Na yi murmushi ina nuna mata wayata na ce"lambar ki!"

Babu jan aji ta karb'a ta saka mini, na yi mata godiya ina fad'a mata zan kira ta, sannan na koma wurin Hafiz.

Had'uwa ta da yarinyar nan ita ce nadamata ta farko, da na sani ban gan ta ba!. [11/2, 1:11 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕