Mataccen buri

Page 7

by @sadiyaabdulrazak954

Sunan ta Ni'ima, farkon ganin ta na yi zaton na samu Khairi ta biyu ne,amma tun fara mu'amula da ita na lura ta fuska ne kawai suka yi kamanceceniya, ita halin ta da ban yake, ba ta da aji kamar Khairita, hasalima ta fi zurfafa wa a kan so na. Ranar da tunani biyu na wuni; Halin da Khairi take ciki, da kuma had'uwata da k'anwarta Ni'ima, idan na tuna mahaukaci ta aura, kuma zai yi amfani da ita wurin warakar shi, sai na ji duka zuciyata ta jagule, na ji ina ma ina da yanda zan yi, na haramta masa ita, sanin ba ni da mafita ya sa na bar wa Allah komai, ina yi mata addu'ar dangana.

Tara na dare na koma gida, Nabila har ta kwanta, sai da na gama duk uzururruka na, sannan na janyo wayata na kira lambar da na karb'a, muka gaisa, na sanar mata ni ne na d'azu, ta ce ta gane muryata, muka yi fira sama-sama, kafin na shaida mata na gani, ina so, abun mamaki babu ko musu ta ce mini ta karb'i tayi, kai! Wasu matan ba su da aji, don kafin mu yi sallama sai da ta furta mini Kalmar I love you, wacce na d'auki lokaci da Khairi ba ta furta mini ba, har muka yi sallama ban sanar mata na san Khairi, don ko zan fad'a mata ba da wuri ba, musamman da na ji tsakanin gidan su da na Khairin akwai tazara, na san zai yi wuya ta san ni, sai dai ta ji suna na.

Duk wayar da nake yi, ina lura da Nabila ba bacci take ba, tana ta mutsu-mutsu alamar tana ji na, da na gama na lumshe ido ina ta tuna Khairi.

Washegari tun sassafe Ni'ima ta kira ni a waya, abun ya ba ni mamaki, na d'aga sai ta ce wai ta kira ne ta gaishe ni, na yi murmushi mu ka gaisa, sannan ta ce ta tura mini hotunanta ta WhatsApp, na yi mata godiya ina jinjina rashin aji irin na yaran yanzu, ko kuma dan ta fi Khairi k'uruciya ne oho!

Ban koma baccin ba, sai da na kunna data na duba hotunan. A kwance nake amma sai da na tashi zaune, na dinga kallon hotunan da suka k'ara fito da tsantsar kamannin su da Khairi, sai dai ita fa ko a hoton za ka karanci kanta ya na rawa, dan kaf cikin su babu mai mayafi, wani ma ko d'ankwali babu, wani kuma shigar kai tsaye za a ce bai dace a bawa saurayi hotunan ba, kuma sun fi kala goma, na zauna na more kallo daidai gwargwado, sai nake ganin kamar Khairi ce nake gani babu hijjabi, don kaf hotunnta na wayata babu wanda babu mayafi, ko da kuwa rolling ne.

Haka na yi wunin ranar ina kallon hotunan Ni'ima, mun yi waya da ita a ranar ya kai biyar, bini-bini sai ta kira ni, wai za ta ji lafiyata ne, yarinyar tana da iyayi sosai, ko dan na lura na yi mata ne, ita da kanta ta tambaye ni yaushe zan zo gidan su, na ce mata gobe, sai ta marairaice mini wai tana son gani na da wuri, ta turo min adireshin gidan su da ke Janbulo, haka dai na buga wanka da daddare na yi mata tsaraba na tafi.

Tsaf! Na bi kwatancen da ta yi mini, ya kai ni har k'aton gidan su, wanda ina gani na san akwai rufin asiri, ta fito ta tare ni tana ta fara'a, dama ni gwanin fara'a ne, haka aka yi mini masauki har cikin d'aki, bayan mun gaisa na ce"da alama dai ni mai sa'a ne, don na lura tun jiya na gama da zuciyarki!".

Ta yi wani fari da ido ta ce"Ai dai ni na fara gamawa da taka zuciyar".

Na ce"gaskiya ne, kin caka mini mashi, kuma ya shiga babu k'arya na kamu, da ba ki amsa ba, ban san halin da zan shiga ba!".

Tana ta dariya, ina kallon ta sak Khairi nake gani a gabana, amma wannan komai nata ba irin na waccen ba ne, ta saki jiki da ni sosai kamar mun yi shekara.

Ta harare ni ta ce"sai kallo na kake yi".

Na sauke numfashi na ce"na ga har kin saki jiki da ni".

Ta d'age kafad'a ta ce"mutane su na cewa ba ni da wuyar sabo".

Na ce"na ga alama ai! Amma kin yi soyayya da wasu mazan kafin ni ko?"

Ta girgiza kai ta ce"mutum d'aya ne, amma mun rabu da shi".

Na ce"meye dalili? Fad'a mini don na kiyaye, saboda ni zai yi wuya na jure rabuwa da ke".

Ta ce"kawai, ba auren ne ya kawo shi ba, kuma yana da wata matar, ni kuma ba na son kishiya, sam ba zan iya ba!".

Na ji damm! Don sai yanzu na tuna ni ma ina da matar, sai na godewa Allah da ban sanar mata ba tun da wuri.

Na ce"ashe ba kya son kishiya, ni ma ina da matar to, ya za a yi kenan?"

Sai ta fara dariya ta ce"ba ka yi kama da mai mata ba".

Na ce"au! Har kama ne da namiji mai mata?"

Ta ce"I mana! Ina ganewa ni dai".

Na ce"ta yaya pls?"

Ta ce"tun da kai dai babu mu bar zancen kawai!".

Na yi dariya na ce"an bar shi!".

Muka sha fira sosai, don har ji na yi kamar kar na tafi wallahi, saboda d'auka nake kawai da Khairi nake tare ba Ni'ima ba, muka yi sallama na ce mata gobe ma ina hanya.

Haka na koma gida ina jin nauyin zuciyata ya ragu sosai, yarinayar ta rage mini kashi saba'in cikin d'ari na kewar Khairi.

Haka na samu wurin zuwa, ko ban je ba kullum muna manne a waya, duk da har lokacin ina ji a zuciyata ba ta kama k'afar Khairi ba, don haka ba za ta iya mantar da ni ita ba, babu wasu awanni da za su shud'e ban yi tunanin halin da take ciki ba, na daina gwada lambarta tun da na san yanzu matar wani ce, amma fa babu abin da ya rage son ta a zuciyata.

Soyayyata nake ci da tsinke, na mai da Nabila kamar hoto, don da ita da babu duk d'aya a wurina, ban san yanda take gudanar da rayuwarta cikin gidan ba, tun da ko tana falo idan na dawo za ta koma d'akinta, sai dare ta shiga d'akina ta kwanta a carpet, idan tana buk'atar wani abun kuma ta yi mini tex massage kamar yanda na umarce ta.

Wata d'aya kenan da had'uwar mu, amma mun saba da Ni'ima sosai, mun samu shak'uwa, duk da har lokacin har zuciyata ban ji zan aure ta ba, ina kula ta ne kawai saboda tana da kyau, tana kama da wacce nake so, kuma tana nuna mini so da kulawa sosai, a yanzu hotunan ta a wayata ba zan k'irga adadin su ba, hoto har wanda ta saka kayan bacci turo mini take, tun da na saba ganin ta a hakan, don duk daren duniya kafin mu yi bacci sai mun yi video call, kuma Nabila tana kwance a k'asa ta na ji na, amma ba ta tab'a yi mini magana ba.

Idan na ce ba na shiga wani yanayi a kan Ni'ima na yi k'arya, lokuta da dama idan muna zaune ina jin da ma ita ce a matsayin Nabila, da zan yi manage, yanayin shigar da take yi, da kuma sakin jiki da take yi da ni, sai na yi ta zargin kamar ta san maza, ina jin kamar na gwada rik'e ko hannunta ne na gano dalilin ta na saurin sakewa da ni, sai na kasa, na ga kamar Khairi ce, ita kuma Khairi ba ta cancanci haka a wuri na ba, kawai sai na basar. Sai na dawo gida na saci kallon Nabila, wacce nake jin ba zan iya d'aukar ta a matsayin matata ba, bare na je mata da wannan buk'atar, haka dai na dinga mazewa, amma sosai gangar jikina take sanar mini na kai namiji, sai na tauye ta, na yi mata musu.

Ban shirya ba, saboda ban yi zato ba, kwatsam iyayen Ni'ima suka nemi gani na, na dinga jin fad'uwar gaba, yayin da ita kuma take farin ciki da sanar mini ita ta ce musu ni take so, yanda na lura da yarinyar gabad'aya soyayyata ta tafi da imanin ta, a tunanin ta auren ta zan yi babu wata gargada.

Haka dai na amsa kira, jikina duka a sanyaye.

Kaina a k'asa na gaida mahaifinta, ya amsa, sai na yi mamakin jin ya san gidan mu, ya ce"a cikin 'yan gidan ku waye ya nemi Ummul-Khairi da aure a ka fasa?"

Nan take k'irjina ya fara dukan tara-tara, ban tsammaci tambayar ba, don haka na d'an yi jinkirin ba da amsa, na 'yan sakanni, kafin na ce"ni ne!".

Ya jinjina kai ya ce"yaushe ka yi aure da har za ka k'ara wani?"

Gabana ya na ta fad'uwa na ce"I, zan k'ara nan ba da jimawa ba".

"To ban amince d'an gidan ku ya auri 'yata ba, bare kuma kai!". Ya fad'a kai tsaye.

Na d'ago na kalle shi, na mai da kaina k'asa ina jin ya wulak'anta ni.

Ya ce"tun farkon zuwan ka, na bincika na gano kai ne, kuma na sani ba aure ne ta kawo ka ba, ka yaudari 'yar'uwarta shi ne za ka dawo kan ta kenan? To na raba ka da ita, kar na sake ganin k'afar ka a gidan nan! Namijin k'warai kawai zan aura wa 'yata, na tabbatar ba ka sanar mata ka so 'yar'uwarta ba, tun da ka ma yi mata k'aryar ba ka da aure, hakan ya sake tabbatar mini dama ka saba yawon yaudarar yaran mutane, to muddin na sake jin ka kula Ni'ima, sai na je har gida na kai k'arar ka, idan ba su d'auki mataki ba ni na d'auka!".

Duk maganganun da yake yi kaina yana k'asa, ina jin zafi a zuciyata sosai, ba wai zafin rabuwa da 'yar shi ba, kawai Na ji haushin yanda ya titsiye ni yake fad'a min son ran shi, kodayake ni na shiga gonar shi, tun a tsugunne a wurin na saka a raina na bar Ni'ima har abada!.

Sai dai kash! K'addara ta riga fata, ashe ma a wannan lokacin had'uwar ta da Ni'ima za ta fara, had'uwa mai muni wanda ni kaina ban so komai ya kasance ba, had'uwata da Ni'ima ita ta mayar da ni d'an watangariri!

Gaba duk za ku ji yanda aka haihu a ragaya.

*** [11/6, 8:54 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕