Page 8
A sanyaye na fito daga d'akin, sai na hango Ni'ima a can nesa tana jira na, murmushi shimfid'e a fuskarta, sai ta ba ni tausayi, don na san duk a zaton ta na amsawa mahaifinta zan aure ta ne. Na k'irk'iri murmushi bayan na k'arasa inda take, na ce"Ni'ima! Ki yi hak'uri, ban cancanci ki d'auke ni matsayin masoyi ba, ina nufin ban kai matsayin wanda zai aure ki ba, mahaifin ki ya yi mini katangar k'arfe da ke, saboda haka mu bi umarnin shi, shi ne daidai".
Tun da na fara magana kallo na kawai take yi, kamar mai mamaki, ko k'ifta ido ba ta yi, na fara tafiya don barin gidan, sai ta yi saurin shan gaba na, ta rik'e hannuna idanunta har sun canza launi da alama hawaye suna dab da zubowa, ta ce"ban gane ba Saif! Ka na nufin ba za ka aure ni ba? Me na yi maka?"
Na kalli hannuna da yake cikin nata, na janye na girgiza mata kai, sai na kasa cewa komai kawai na ci gaba da tafiya, har k'ofar gidan ta biyo ni, zuwa lokacin tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta ce"don Allah me ya faru?"
Na ce"ki je Daddy zai yi miki bayani".
Ta girgiza mini kai ta ce"daga bakin ka..."
Ba ta k'arasa ba, na ce"na ji za mu yi waya!".
Na wuce da sauri na shiga motata na bar layin a slow ina jin zuciyata babu dad'i, ko babu So akwai shak'uwa a tsakaninmu, lokacin da na rabu da Khairi na fi tausaya wa kaina, amma yanzu na fi tausaya wa Ni'ima, saboda dama can ban saka ran zan same ta ba, ita kuwa ta yi amanna d'ari bisa d'ari.
A falo na zauna ina ta sauke numfashi, da kuma harhad'a maganganun da zan yi amfani da su wurin kwantar mata da hankali, yanda za ta manta da ni cikin sauk'i. Ina cikin wannan tunanin wayata ta yi ringing, sai da na zabura don na yi zaton ita ce, sai da na d'auka na ga Ummi ce take kira na.
Na d'aga da murya mai sanyi.
Ko amsa gaisuwa ta ba ta yi ba ta ce"Ya yi maka kyau! Saifullahi ka kyauta, idan wulak'anta d'an'adam abun yi ne kar ka fasa har abada!".
Na tashi tsaye gaba na ya na d'an faduwa na ce"subhanallah! Ummi me ya faru?"
Ta ce"ban sani ba! Ka ba wa matarka maganin ciwon jiki, kuma wallahi idan ta sake kwana a k'asa sai ranka ya b'aci, duk wani nau'i na cutar wa idan ka yi mata komai k'ank'antar shi ban yafe maka ba!".
Ba ta ma jira cewa ta ba, ta katse kiran.
Na furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ina jin wani sabon takaicin ya rufe ni, ni ina son kashe case din Ni'ima ita kuma wannan banzar mara amfani ta na son bud'e mini wani.
"Aikin banza!" Na furta ina shiga d'akin.
Kwance na same ta a gefen gado, ta duk'unk'une wuri d'aya, kana gani ka san a tsorace take.
"Kee!" Na daka tsawa.
Sai ta tashi zaune ta na sunkuyar da kai.
Na ce"to uban me ya hau da ke kan gado?"
Ta ce"Ummi ce ta ce na daina kwana a k'asa".
Ina harararta na ce"kenan fitar da sirrin aure kike yi?"
Sai ta girgiza mini kai da sauri ta ce"a'a! Ciwon jiki nake shi ne na fad'a mata".
Na ce"idan ba gulma ba ita d'in magani za ta rubuta miki?"
Ta girgiza mini kai alamar a'a.
Na ce"to ba za a ba ki maganin ba! Ko rub'ewar jiki kike ba ciwo ba, kalle ta don Allah! Yanzu meye ribar da kika ci a gidan aure? Ko kin yi zaton MATAR SHIGE ta na daraja?"
Ta girgiza mini kai alamar a'a, har ta fara hawaye.
Na ce"dalla cen kwanta, kika mini kuka a nan zane ki zan yi wallahi!".
Sai ta kwanta, tana share hawaye daga kwancen.
Na yi wani murmushi, ina jin dad'in yanda yarinyar take tsoro na, hmm! Kafin ta falle ta fara yi mini bore kenan!.
Sai da duk na gama abin da zan yi na nutsu sannan na kira wayar Ni'ima, bugun farko ta d'auka, kamar dama jira na take, na sauke numfashi na ce"Ni'ima ki yi hak'uri!".
Ta ce"Saif! Me ya sa tun farko ba ka fad'a min kai ne wanda aka fasa auren ku da Ummul-Khairi ba?"
Na ce"saboda ina tsoron kar ki ji, ki k'i kula ni".
Ta ce"babu ruwa na da tsohon baikon ku, ko auren ta ka yi, ka sake ta wallahi ni zan aure ka, ina son ka!".
Na girgiza kai kamar tana gani na, na ce"ni ma ina son ki, amma wajibi mu hak'ura, tun da mahaifin ki ba ya so".
Ta ce"A'a don Allah, ba dole sai mun rabu ba, za mu iya soyayyar mu ba tare da ya sani ba, sai...".
Na katse ta da fad'in "Ni'ima meye amfanin soyayyar da babu aure? Ko mun yi soyayya a b'oye ai ta banza ce, tun da watarana dole mu rabu, to a gani na kawai mu hak'ura da juna!".
Sai ta fashe da kukan da ya k'arasa kashe mini jiki, tausayin yarinyar ya kama ni, na ce"ki yi hak'uri, ki daina kuka, ba na jin dad'in kukan ki!".
Ta ce"ba zan daina ba, me ya sa za ka bar ni? Tun farko me ya kawo ka wuri na?"
Na ce"ki yi hak'uri! Ni ma ba a son raina ba".
Ta ce"ina son ganin ka gobe!"
Na girgiza kai, na ce"Alk'awari na yi, ba zan sake zuwa gidan ku ba".
"Ba sai a gida ba!" Ta fad'a da sauri.
Na ce"Allah ya kai mu". Na katse wayar, sannan na rage dare da kallon hotunan ta kafin bacci ya d'auke ni.
Washegari sai na tashi daga asibiti sannan na kira ta, ta fad'a min za ta jira ni a nesa da layin su, da na je na faka inda na ganta a tsaye, sai ta shigo motar, ta juya mini baya.
Na ce"ki yi hak'uri Ni'ima!".
Ba ta juyo ba, kuma ba ta yi magana ba.
Na lek'a fuskarta sai na ga hawaye take yi sosai, na zari tissue na mik'a mata, sai ta harare ni, ta ce"ai ka na son kukan nawa".
Na kai hannu a karo na farko da na tab'a jikinta, na share mata hawayen, na ce"ba haka ba ne, kawai ina son ki yi wa iyayen ki biyayya ne".
Ta ce"za mu yi soyayya ko babu aure".
Sai na jinjina mata kai alamar gamsuwa, saboda ba na son kukan nata, sosai ta ba ni tausayi don haka na dinga rarrashin ta, da kalaman yaudara, ban bar ta ba har sai da ta yi mini murmushi.
Kuma tun daga wannan ranar ba ma cika kwana uku ba mu had'u mun yi zance a mota ba, wannan kusancin zaman motar da kuma kad'aicin da muke samu, shi ya haddasa komai da ya faru a tsakaninmu, tsakanin hotuna da videon Ni'ima da nake yawan gani cikin shigar da ba ta cancanta saurayi ya gani ba. Da kuma kusancin da na samu da matata Nabila na kwana a shimfid'a d'aya, cikin shiga ta d'aukar hankali, ba zan ce ga abin da ya yi rinjaye a kaina ba, na dai wayi gari ne kawai da samun canjin bazata a jikina, a lokacin na dinga ji a jikina ni ma cikakken namiji, kuma akwai buk'atar na ba wa gangar jikina hakkin ta, tun ina daurewa har abu ya ci tura, na cutar da gangar jikina ba kad'an ba, har zuwa lokacin da ta gaji ta yi mini bore, da nuna muddin ban bi ra'ayinta ba, za a samu matsala.
Hmm! Wallahi a lokacin na fi sha'awar na rab'i Ni'ima fiye da matata, amma sanin hakan haramun ne a gare ni, kuma abin da ba ka tab'a aikatawa ba dole ka ji shakkar sa, ya sa na sakko na yanke shawarar nema daga wurin halali na, amma sai Nabila ta yi mini bazata, ta karantar da ni halin da duniyar mafiya yawan samari da 'yan'mata take ciki a yanzu.
Ranar mun had'u da Na'ima, surarta ta gama kunna ni, na dawo gida a jigace, tun yamma na kasa tab'uka komai, ina kwance ina sauraron yanda ake zabga gumurzun yak'i tsakanin zuciya da gangar jikina, kai! Wani lokacin zuciya ba ta da adalci, musamman idan mutum ya bari ta fi k'arfin shi, zuciya tana ta fad'a mini kar na kusanci wacce ba na so, na k'ara hak'uri, yin hakan kamar na manta da Khairi ne, yayin da gangar jikina take tunzura ni, kan na daina cutar kaina, na je ga halalina na samu nutsuwa, tun da ina buk'ata, to k'arshe dai gangar jikin ce ta yi galaba a kan zuciyar, don haka na tashi na nufi d'akina wanda Nabila ta jima da shi.
Ba k'aramin yak'ar kunya na yi ba, kafin na iya nuna mata ainahin muradina na ranar a kanta, duk da na san za ta iya jin tsoro, amma sam ban yi zaton za ta yi mini gardama, sai da na nuna mata fin k'arfi kafin na kai inda nake muradi, sai dai ban tarar da Nabila a yanda na yi zato ba, duk da ba ni da tabbaci, tun da ita ce macen da na fara sani, amma ina da ilimi ta wannan fannin saboda haka ko wani mai auren zan iya ba shi labari.
Ta kifa kanta tana ta kuka da iya k'arfin ta, na ce"Nabila tun yaushe kike rabon mutuncin ki?"
Kukanta ya tsananta, kuma ba ta ba ni amsa ba.
Maganar duniyar nan yarinyar ba ta tanka ni ba, raina ya b'aci ba kad'an ba, cikin tsawa na ce"tashi ki bar d'akin nan kafin na karya ki!"
Babu musu ta tashi ta fita a guje, na shiga band'aki na sakarwa kaina ruwa, ina cike da bak'inciki mara misali, zafin biyu ya had'e mini, ba son ta nake ba dama, ga shi kuma na gano ba 'yar kirki ba ce, duk wani sauran tausayin ta a ranar ya sulale daga zuciyata, k'aunar jinin ma na neme ta na rasa, kuma na yi alk'awarin ba zan sake had'a d'aki da ita ba, na gama da babin ta har abada, za ta yi ta zaman amsa sunan matata, ni kuma wajibi na yak'i gangar jikina har ta yi saranda ta amince na fi k'arfinta, na tilasta ta ta daina yi mini kallon lafiyayyen namiji, bare har ta k'awata mini wata macen.
Sai dai duk iya k'ok'arina na gaza, gangar jikina ta fi karfi na, don haka kawai na zabawa kaina rayuwar da na yi tunanin za ta fisshe ni, ba tare da na yi dogon nazari ba. [11/8, 10:50 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕