Page 9
Bacci rabi da rabi na yi a ranar, sosai na yi nadamar kula Nabila, nutsuwar da na yi fata ban samu ba, sai tarin bak'in ciki, na dinga kallon hotunan Ni'ima, ina ayyana watak'il ita ma hakan take.
Washegari da safe na fito zan tafi aiki na ga Nabila zaune a k'asan kujera, ta lullub'a da bargo, ta takure wuri d'aya, na yi mata kallo d'aya zan wuce, cikin muryar da ke nuni da ta na dab da sakin kuka ta ce"Yaya ba ni da lafiya".
Na juyo na yi mata wani mugun kallo, sannan na yi k'wafa na fice, gabad'aya yarinyar ta gama sire mini, sam babu tausayin ta a zuciyata, a da na yi zaton ta gari ce, shi ya sa har nake rarrashin ta bayan ta rasa jigon rayuwarta, amma yanzu da na gane ainahin kalar ta sai na yi nadamar b'ata lokacin da na yi a baya, wurin faranta mata.
Ina tsaka da aiki babu zato sai ga ta, har cikin office d'ina, na d'ago na kalle ta da mugun mamaki, ta na shirin zama a kujera na daka mata tsawa da fad'in"idan ki ka zauna sai na wanke ki da mari, me ya kawo ki wurina?"
Ta fara kukan da a yanzu haushi yake ba ni, ba tausayi ba, ta zube a k'asa ta ce"wallahi ba ni da lafiya, tun jiya!".
Na taso a fusace na doddoke kanta, cikin fad'a na ce"ni na d'ora miki cutar da zan yi miki magani?"
Cikin matsanancin kuka ta ce"Amma ka san abin da ya faru daren jiya, sai ka kore ni, kuma ba ka bi ta kaina ba..."
Kafin ta k'arasa na nad'a mata k'afa, sai da ta hantsila, na d'ago ta na wanke fuskarta da mari, na watsar da shegiya, na koma na zauna ina huci, cikin haka abokin aikina ya shigo, ya kalli Nabila ya kalle ni, a rude ya ce"Doctor wannan fa? Me yake damun ta?"
Na ce"don Allah watsa ta waje, don idan na tashi ba ta fita ba sai na lahanta ta!".
Nabila ta tashi ta na kuka, ta fita, shi kuma ya kalle ni ya ce"wace wannan? Kar dai ka ce mara lafiya ce, ta zo ganin ka?"
Na girgiza kai, na ce"k'anwata ce".
Sai ya fita, bai ce mini komai ba, can kuma ya dawo ya ce"na mayar da ita gida, amma kuma na ga ba gidan ku da na sani ba ne".
"Ba uban mu d'aya ba! Kuma kar ka dame ni don Allah!" Na fad'a cikin k'osawa
"To Allah ya rufa asiri" Ya fad'a sannan ya fice.
Bayan la'asar ina shirin tashi daga aiki, Ummi ta kira ni, na d'aga na gaishe ta, ta ce"ka san matarka ba ta da lafiya?"
"Gaskiya ban sani ba" Na fad'a kai tsaye.
Ta ce"to ba ta da lafiya, ka je ka gani".
Na ce "in sha Allah!".
Sai da lokacin tashi na ya yi, sannan na koma gidan, na tafar mata da magunguna, a falo na same ta, na jefa mata na wuce d'aki, na fito daga wanka sai na ga tex d'inta, ta na fada mini wai ba ta ci komai ba, na yi tsaki ban bi ta kanta ba, na buga wanka na, na zo na wuce ta ina kiran layin Ni'ima, muka had'u a inda muka saba had'uwa, muna yin fira sama-sama, Ni'ima ta kalle ni ta ce" Love kamar kana da damuwa ko? Menene?"
Na kalle ta na girgiza mata kai alamar a'a.
Ta shagwab'e fuska ta ce"ban yarda ba! Ba za dai ka fad'a mini ba".
Haka kawai zuciya ta ingiza ni, kan na gwada Ni'ima kamar yadda na jima ina so, amma wani abu mai kama da tsoro ko shakka yana hana ni, na ruk'o hannunta ina matsawa idona cikin nata, ita ma ni d'in take kallo babu yabo babu fallasa.
"Kina son jin damuwata?" Na tambaye ta.
Sai ta gyad'a mini kai alamar ta na son ji. Kafin kiftawar ido na had'e bakina da nata, na shiga sumbatar ta kamar wanda na saba, ta tsaya cak ba ta hana ni ba, har na yi mai isa ta, na matsa baya, sai na ga hawaye a idanunta, na goge mata ina d'an jin fargaba, na ce"ki yi hak'uri! Na kasa saita kaina ne, ba hali na ba ne".
Ta k'arasa goge hawayen ta ta ce"Kiss ba komai ba ne Saif! Kawai dai yadda na lura duk wani saurayin da mace ta yarda suke romantic bai fiya auren ta ba, abin da ya raba mu da saurayi na ke nan, ya tab'a ni sosai, kuma ba na damuwa saboda ina tunanin aure na zai yi, don a yadda nake son shi tsaf zan iya ba shi kaina a lokacin, amma da ya nemi ya kai har k'arshen sai na so na gwada yadda yake so na, na nuna masa ba zan yarda ba..."
Sai hawaye ya zubo mata, ta kwantar da kanta a k'irjina tana kuka ta ce"sai ya nuna mini dama inda yake so ya kai kenan, tun da ba zai samu ba ya bar ni har abada, ya kira ni da banza, mara kamun kai, ya ce shi ba zai auri sauran titi ba, alhalin shi ne farkon wanda ya yi kissing d'ina!"
Ta k'ank'ame ni, tana jan hanci, na so na janyeta daga jikina sai ta k'i, ta ce"don Allah kar mu yi haka da kai, na ji tsoro da ka fara kissing d'ina, kar kai ma ka guje ni!".
Na girgiza kai, na ce"ni ba irin sauran mazan ba ne, Ni'ima indai kin yarda da ni, to ki bar saka kokonto a kaina, ina tare da ke har zuwa lokacin da za ki daina so na!"
Sai ta d'ago ta kalle ni tana murmushi ta ce"har abada ke nan!".
Na jinjina mata kai, alamar tabbatarwa, sannan na sake had'e bakin mu, tun da na d'azun bai ishe ni ba.
Wannan shi ya zama mafarin lalacewa ta, tun daga ranar muddin za mu had'u da Ni'ima sai mun yi romance sosai, abun ya dinga tafiya gaba-gaba, tun ina d'ari-d'ari har na ware na zama k'wararre ta wannan fannin, na yi mugun sabo da jikinta kamar matata, domin ita na lura ta saba tun tuni, tun da ba kaina farau ba, sai dai tana yawan maimaita mini don Allah kar na guje ta.
Na share Nabila na manta da ita mace ce, zan iya samun nutsuwa daga gare ta, kuma daga ranar da wannan abun ya faru na kore ta, ba ta sake kwana a d'akina ba, shi ya sa nake sakewa mu yi dirty tallk da Ni'ima duk daren duniya, mu yi video call har sai na gaji da ganin jikinta.
Sannu a hankali kuma na fara k'osawa da romance d'in da muke yi, to na yi ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba, kullum abu d'aya ne, jikina ya fara neman k'arin wani abun, ko kuma canji, ba na son barin ta a wannan lokacin, don haka kai tsaye na je mata da babbar buk'ata ta, don burina kawai na je can d'in, saboda jikina yana ba ni babu yadda za a yi buduruwa cikakkiya ta saki jiki ina yin yadda na so, ba tare da ta tab'a sanin namiji ba.
Amma da na fito na sanar mata muradina, sai ta nuna ba ta yarda ba, ta kalle ni kamar za ta yi kuka ta ce"don Allah kar mu yi haka, mu bari har sai mun yi aure, tsoro nake ji kar kai ma ka guje ni ".
Na girgiza mata kai, na ce"don Allah Ni'ima ki cire zargin ni Saifullahi zan bar ki, ki gwada yarda da ni, sau d'aya kawai fa".
"Ina matarka?" Ta yi mini tambayar da ban yi zato ba.
Na had'e rai na ce"babu ruwan ki da ita, kin fi ta daraja a wurina, idan kin ga ba zan samu ba shi ke nan, ni ba zan takura ki ba".
"Zan yi tunani!" Ta fad'a da murya mai sanyi kamar ba ita ba.
Na d'aga kafad'a alamun ko a jikina.
Haka muka rabu dai a ranar duk jikinta a sanyaye, ina ta jira ta yi tunanin har kwana uku shiru, kuma ko zancen ba ta sake yi mini ba, sosai sha'awar yarinyar take neman zautar da ni, don haka na sake tuntub'ar ta da zancen, sai ta ce mini ita fa tsoro take ji, raina ya b'aci na ce mata shikenan na gode.
A ranar na yi blocking d'inta, ba dan ina jin zan iya barin ta ba, sai don na gwada ta na ga da gaske take nuna mini so, ko iya baki ne, aikuwa na samu tabbaci, don ta yi ta kira na da wasu lambobin idan na d'aga na ji ita ce sai na katse, sati d'aya muna a haka, duk da ina azabtuwa da kewarta, amma na fi so ta horu, ta yadda ba za ta sake yi mini gardama ba.
Watarana Ni'ima ta biyo ni har asibiti, tana shigowa na d'ago na kalle ta, sai na mai da kaina ga abin da nake yi, ta ja kujera ta zauna damuwa k'arara a fuskarta.
Na ce"idan kin san ba ganin likita kika zo ba, tashi ki fita".
Ta ce"ina so mu yi maganar..."
"Nan wurin aiki ne, ko matata ba zan saurara ba!". Na katse ta.
Ta ce"to a ina za mu had'u? Ka yi blocking d'ina!".
"Ki je, zan neme ki!" Na fad'a ba tare da na kalle ta ba.
Sai da ta fita na sauke ajiyar zuciya, tare da lumshe ido, ina ji a jikina kamar idan ban nemi mace ba yau ba zan kwana a duniya ba.
Sai da na tashi daga aiki sannan na yi unblock na kira ta, ta d'aga ta gaishe ni, na amsa na ce"maganar me kike so mu yi?"
Ta ce"ka na ta son ka rabu da ni, ka san kuma ina son ka sosai".
Na ji dad'i har zuciyata, na ce"a'a ban sani ba! Tun da ban ga alama ba, Ni'ima wanda kake so burin ka kullum ya kasance cikin farinciki, za ka iya sadaukarwa wanda kake so rayuwarka gabad'aya, amma ke wannan k'ank'anin abu da na tambaye ki, shi ne kika nuna mini ban isa ba?"
Sai ta yi shiru har na yi zaton ba ta tare da ni.
Sannan ta ce"ba haka ba ne, kuma wannan ba k'aramin abu ba ne..."
"Ok babba ne, kuma ban cancance shi ba, na gode!" Na fad'a, na katse kiran, na kama hanyar gida.
Ina hanya ta kira ni ya fi sau goma, ban kula ta ba, Allah sarki yarinyar tana so na sosai.
Da na shiga gida ban tarar da kowa a falo ba, na dai jiyo motsin ta a kitchen, don haka na zauna har ta gama ta fito, sai ta kalle ni, ta wuce za ta shiga d'aki, tun da dama ba mu saba shan inuwa d'aya ba.
"Ke zo nan!" Na kira ta.
Ta dawo ta zauna a k'asa nesa da ni.
Ina harararta na ce"don uban ki wasu 'yan iskan kika rabawa kanki?"
Kamar na kunna ta, sai ta fara kuka.
A fusace na ce"ba tambayar ki nake ba? Ki ba ni amsa ko yanzu na kora ki gida, na sanar musu a yanayin da na same ki! Munafukar banza".
Ba ta daina kukan ba, ta ce"Abdul ne kawai, kuma tsautsayi ne".
Na ce"ko baban tsautsayi ba! Ke nan don kin ga da gaske auren ki zai yi, sai kika saki jiki har kika yarda kuke shek'e ayarki ko?"
Ta girgiza mini kai alamar a'a, tana kuka.
Na ce"yanzu da ya mutu ga shi abin da kuka b'oye ya fito, Allah tona asirin ki, me za ki ce mini da kika zo min babu daraja?"
"Ka yi hak'uri!" Ta fad'a tana kuka sosai.
Na ce"shi ne kawai abin da za ki ce?"
Ta ce"kai d'an'uwana ne, ko wani namijin na aura ba kai ba Yaya za ka iya ba shi hak'uri! Na yi nadama".
Na jinjina kai, na tashi na shiga d'akina.
Duk kiran da ta dinga jero min ban d'aga ba, sai da daddare, ta dinga ba ni hak'uri, kuma ta ce ta amince da buk'ata ta, sai dai tana jin tsoron zuwa hotel kar wani ya ganta, sai na yanke ta zo mu had'u a gidana, zan san yadda zan yi da Nabila.
Washegari ta kama Asabar ne dama babu aiki, tun safe na ce wa Nabila ta je gidan su ko gidan mu, kar zaman kadaici ya ishe ta, ni na kai ta har gidan su, na dawo, k'arfe biyu na rana na je na taro Ni'ima a bakin titi, tana ta d'ari-d'ari, duk jikinta a sanyaye, har ta ba ni tausayi, na nuna mata d'akina alamar ta shiga sai ta kalli sauran d'akunan ta ce"kar fa matarka ta dawo!"
Na yi murmushi na ce"ba za ta dawo ba, sai dare zan d'akko ta".
"Tsoro nake ji!" Ta fad'a kamar za ta fita a guje.
Raina ya b'aci saboda na fara gajiya da rarrashin ta, don haka kawai na ce"ok ki koma!" Na shige d'akin na bar ta a nan.
Sai ta biyo ni, tana taku kamar wahainiya.
A wannan ranar dai na san Ni'ima, kuma na same ta daidai ba kamar matata ba, duk tantirancin nata ashe tana rik'e da mutuncin ta, ta yi mini kyutar shi saboda So, amma daga baya ni sai na butulce mata!. [11/14, 9:39 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕