Page 10
Tun daga ranar na sake shigewa Ni'ima, sosai nake ji da yarinyar saboda girman kyautar da ta yi mini, ita kuma yadda na lura ta k'ara nutso cikin kogin so na, had'e da fargabar kar na rabu da ita, tana ta nan nan da ni.
Sai dai duk yadda na so mu sake had'uwa ta k'i yarda, ga shi cikin kwana biyun kamar wani ya zuga Nabila, na lura yarinyar ta rage shakkata, kuma yanayin shigarta kamar da gayya take yi, duk da na yi mata gargad'i, amma daga baya ta watsar ta dawo d'akina da kwana, ta wani saki jikinta a cikin gidan ta daina d'ari-d'ari, hakan ya sake tunzura gangar jikina ga buk'atuwar abokiyar tarayya, sai dai fa ko kusa ba na kawo wa raina na je ga Nabila wacce ta kasance halalina, sai dai begen Ni'ima ya lunku a zuciyata.
Watarana muna tare da Ni'ima, na k'ure ta da kallo kamar yadda na saba, sai ta kai hannu ta rufe mini ido tana dariya da tambaya ta dalilin kallon.
Na rik'e hannun nata da murya mai rauni na ce"Honey me ya sa kike yi mini rowa ne? Ko kin fi so na haukace?"
Sai ta juya mini baya, ta canja fuska.
Na janyo ta jikina na ce"ki yi hak'uri, ba zan d'auki fushin ki ba, me ya faru? Me na yi miki?"
Kamar za ta yi kuka ta ce"tsoro nake kar ka rabu da ni..."
"Wallahi ba zan bar ki ba!" Na tari numfashinta .
Ta ce"tun ranar da abun ya faru, zancen ka d'aya kawai na saki jiki da kai, na sake yarda da kai, ko zancen yadda za a yi auren mu ya yiwu ka daina, ta ya jikina ba zai yi sanyi ba?"
Na lumshe ido na bud'e, idan na ji ta yi zancen aure gabana fad'uwa yake, duk sai raina ya jagule.
Na ce"Ni'ima zan yi mamaki ace har yanzu kin kasa yarda da ni, kin k'i sakin jiki da ni, ta ya zan yarda son da kike yi mini na gaskiya ne, har na fara nema mana mafita? Gaskiya idan kina zargi na kawai ki sanar mini, na yi gaba!".
Sai ta kalle ni ta na hawaye, ta ce"Idan har kyautar mutuncina da na yi maka bai sa ka yarda da ni ba, to ci gaba da ba ka kaina ba zai zama silar yarda da ni ba Saifullahi!".
Na ce"kina nufin yanzu ni dai ban kai wanda zan iya tambayar alfarma a wurin ki duk lokacin da nake so na samu ba ko?"
Sai ta girgiza mini kai alamar ba haka ba ne, har lokacin tana hawaye.
Na kai hannu na share mata hawayen a hankali, sannan na ce"idan har ni ne silar kukan ki Ni'ima daga yau kin daina in sha Allah! Zan fita daga rayuwarki, mu daina ganin juna bare har na sake tambayar ki abin da za ki yi k'yashin ba ni, na gode da soyayyar da kika nuna mini, daga k'arshe ina yi miki fatan alkhairi, Allah ya dubi zuciyarki ya ba ki mijin da ya fi ni".
"Saifullahi!" Ta kira sunana a tsorace.
Sai na jinjina mata kai, alamar tabbatarwa, sannan na kai hannu na bud'e murfin motar alamar ta fita.
Sai ta rik'e hannuna da duka hannuwanta biyu ta fashe da kuka, tana ta girgiza mini kai ta kasa magana.
Na danne tausayin ta da yake neman sare mini gwiwa, na nuna mata k'ofar motar na ce"bismillah! Ni'ima ni ba macuci ba ne, tun da har ina cutar da ke a tarayyar mu to gaskiya akwai matsala, ba na son zama silar kukan wani a duniya, bare ke da kika nuna mini so, kuma kika yi min babbar kyautar da matata ta sunna ba ta yi mini ba, kina da k'ima a idona!".
Sai ta sake fashewa da kuka ta ce"yanzu ne kake shirin zama silar kukan nawa, Saif idan ka rabu da ni waye zai aure ni? Me zan fad'awa wani mijin da na aura sab'anin ka?"
Na d'aga mata kafad'a cikin rashin damuwa na ce"ki zo zan yi miki d'inki, idan kuma ya gane sai ki fad'a masa sharrin shaid'an ne, ya sa kika aikata, zai fahimta ai ana hakan!".
Ta tsagaita da kukan ta ce"ni ba zan yi hakan ba, kai nake so,kuma kai za ka aure ni, mu rufawa juna asiri".
Na ce"to idan kina so hakan ya tabbata, wajibi ki daina yi mini rowar kan ki, ki d'auka mun zama d'aya kawai".
"Na daina in sha Allah!" Ta fad'a a sanyaye.
Na ji dad'i har raina, na ce"yanzu gobe ina so mu had'u..."
"A ina?" Ta katse ni.
"Hotel" Na ba ta amsa.
Ta ce"wallahi tsoro nake".
Na ce"Ni'ima don Allah mu rabu! Na lura kamar tilas nake yi miki ba da son ranki ba, hakan kuma yana nufin fyad'e, ni kuwa Allah ya tsare ni da zalunci!".
Ta girgiza kai, ta ce"ba haka ba ne, amma ai gara cikin gidan".
Na ce"ba za mu dawwama muna zuwa gidana ba, idan kin amince kawai gobe zan zo na d'auke ki!".
Ta ce"Allah ya kai mu".
Washegari haka ta yarda mu ka had'u a hotel duk a tsorace take, kuma daga wannan ranar shi ke nan, muka dinga zuwa, ba ma rufe sati ba mu je ba, sautari ma uzuri nake dauka a wurin aiki, na je mu huta da Ni'ima, na mai da ita matata ta karfi, tun tana tsoro har ta saba, duk da ina sane har cikin zuciyarta ba ta so, tana yarda na kawai saboda fargabar kar na bar ta.
Watarana kwatsam ta kira ni a waya, tana kuka take sanar mini mahaifinta ya ce ta daina fita, saboda sakamakon jarabawarta da ya munana, abun ya b'ata masa rai, saboda ya san ta na da k'ok'ari sosai a baya, sai ya je makarantar domin ya ji dalilin faduwarta, nan ya samu labarin yadda take yi wa makaranta a sha ruwan tsuntunye, kuma ya tisa ta da tambaya ta ce masa hakane, ba ta b'oye masa komai na soyayyar mu a b'oye ba, don haka ya fusata ya ce ta daina fita gabad'aya. Sosai na yi mamaki, saboda duk haduwar mu da ita ban san makaranta ake tura ta ba, a zatona kawai dai gidan nasu babu dokar fita unguwa ne.
Ta dinga kuka, tana roko na kar na rabu da ita.
Na ce"to Ni'ima an hana ki fita, ina soyayya za ta yiwu?"
Ta ce"ga waya nan!".
"Ta waya za mu yi auren?" Na tambaye ta.
Ta ce"kafin zancen auren ya zo, ba zan iya jure kewarka ba, don Allah!".
Na ce"ina tare da ke Ni'ima! Zan kwanta na huta". Na katse wayar.
Tun daga ranar kuma sai na yi ta k'ok'arin ja baya da ita, saboda a gani na wannan wata damar da zan yakice ta ce ta zo mini, na yi ta k'ok'arin fakewa da k'udurin mahaifinta saboda mu rabu, amma sai ta k'i amincewa, idan na so na yi nan, sai ta taro ni ta can, saboda tana so na sosai, to ni d'in ma sosai na yi kewarta, kwana biyu da ban ji d'umin jikinta ba sai na dinga ji na incomplete, ga zuciya da ba ta da k'ashi sai k'awata mini Nabila take yi, sai ka ce ta manta kalar kayan takaicin da na kwasa ranar da na kasance da ita ba.
Haka dai na dinga daddafawa har zuwa ranar da na gaji da kewarta, buk'atar kasancewa da Ni'ima kawai nake, tunanin ta ya dinga azalzala ta, haka na zo mata da buk'atar ta zo mu had'u a hotel d'in da muka saba, amma sai ta tuna mini har lokacin ba a barin ta zuwa ko'ina, na dinga yi mata magiyar ko satar fitar ta yi, few minutes za mu yi, amma ta kafe akan ita tsoron Daddynta take, sai da na nuna mata fushi na sosai, da kalaman barazanar rabuwa da ita, wanda na lura sosai take shiga tashin hankali idan ta ji kalmar, sannan ta ce ta amince, amma na yi gaba za ta biyo ni daga baya.
Wajan k'arfe hud'u da rabi na yamma na shirya, na je na kama d'aki, muka yi waya ta ce ga ta nan zuwa, ina zaune ina jira har biyar da rabi ta yi shiru ba ta zo ba, na kira wayarta sai na ji a kashe, raina ya b'aci, na rasa mafita, ga shi na kai k'ololuwar buk'atuwa, saboda na saka rai sosai, wata zuciyar ta dinga fad'a mini na manta da komai, na je ga matata, wata zuciyar kuma ta na ce mini Ni'ima za ta zo, ta dai kashe wayar ne kawai, da wannan na fito harabar hotel d'in, ina d'an zagaye.
Tun da na fito na ga shigowar wata mota, sai dai na ciki bai fito ba, kuma ba na iya hango komai daga ciki, da na gaji da zagayen sai na nemi wurin zama ina ta sake gwada layin nata, amma shiru dai, har shida da rabi ta yi, ina ta shawarar na koma gida, kuma babu ni babu Ni'ima, sai na ga an bud'e wannan mota da ta tsaya tun d'azu, wata matashiya ta fito ta nufo ni tana rausaya, na kau da kai ina sake had'e fuskata, don raina a b'ace yake.
"Hi! Kai ne na kwanaki ko?" Ta fad'a bayan ta karaso.
Ni ma kallon farko na lura kamar na san ta, sai da ta yi magana kuma na gane ta, na d'ago na yi mata kallo daya na mai da kaina ga wayata.
Ta zauna dab da ni, ta ce"Siyama sunana, mun tab'a haduwa da kai a nan kwanaki, har na tambayi sunan ka ba ka ba ni amsa ba".
"Ok" Na fad'a kamar an yi mini dole.
Ta sake matsowa ta ce"wane taimako zan iya ba ka? Kamar wata kake jira ko?"
Kusancin mu, ya sake zabtare sauran jarumta ta, saboda masifaffen k'amshin da yake bankowa daga jikinta, sai na d'an matsa ina saita kaina, na ce"na gode".
Ta ce"idan ba ta zo ba, zan iya taimaka maka, ina nufin na rage maka zafi".
Sai na kalle ta daga sama har kasa, na girgiza mata kai alamar a'a.
Ta ce"ba zan takura ka ba, amma da ka cutar da kanka da dai ka gwada, duk da na san ban kai ba".
Zuciyata ta shiga taraddadi, ba zan ce ba na so ba, saboda sosai na kai bango, amma kuma ina kokonto a kanta, don daga ganin ta karuwa ce, ban san adadin mazan da ta sani ba, na kalle ta na ga sai murmushi take yi mini.
Kamar ta san tunanin da nake yi, sai ta zuge yar jakar hannunta, ta d'akko condom tana nuna mini ta ce"Idan ba ka yarda da ni ba".
"Ok, zan gwada". Na fad'a ban san ta inda maganar ta fito ba, sannan na tashi na yi gaba, ta biyo bayana, sai da muka shiga d'akin sannan na tuna wannan ba so ne farashin ta ba, kud'i take nema.
Na kalle ta na ce" farashin fa!?"
Sai ta yi dariya ta ce"ai ni na gayyace ka, na farko kyauta ne".
'Dama daga shi babu kari'
Na fad'a a zuciyata.
Haka na biye mata, muka aikata alfasha, ni ne har goma na dare a hotel, babu sallar magriba bare ta isha'i, hakan ma da k'yar na yak'i shaid'an, na yakice Siyama muka rabu, bayan na karb'i lambarta.
Ashe tsautsayi ya kai ni hotel din, a wannan ranar, don kuwa tun daga ranar muka yi very close da ita, ita ce ta mantar da ni Ni'ima, kuma ta sanadin ta na daina kyamar karuwai, na tsunduma a hanyar neman mata babu ji babu gani, wanda har sai da ya zama silar rasa aikina, da kuma targad'a rayuwata, sannan ya zama babban makamin da ya fille kan burina. [11/22, 9:16 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕