Page 11
Siyama ta shiga cikin rayuwata, ta dinga juya ta yadda take so, sai na ji ashe duk nutsuwar da nake samu a wurin Ni'ima, ta k'arya ce, don haka na banzatar da ita, ta dinga bi na da rokon kar na barta, na riga na shiga rayuwarta na yi ta'adi, na ce mata ta zo na yi mata d'inki mu wuce wurin, ta k'i yarda, k'arshe sai ta fara bi na asibiti, ta zo ta yi ta mini magiya, to a ranar da ta zo gidana ne, na rufe ido na yi mata tijara, da cin mutunci na ajin k'arshe, daga ranar ta shafa mini lafiya, bayan ta ce da yardar Allah sai na yi nadama, kuma duhu zan ta gani a cikin rayuwata har abada, ta ce za ta dawwama ta na yi mini addu'ar shiga bala'i, sosai na yi mamakin yadda son da take yi mini ya zama k'iyayya a ranar, ban damu ba, don haka na shafe nata tarihirin, na sake k'ank'ame Siyama gam!.
Zuwa lokacin har Khairi ta rage tasiri a zuciyata, don nakan yi kwana d'aya cir ban yi tunanin ta ba, sab'anin da, da take ziyartar zuciyata duk bayan awa d'aya, ko ma mintuna.
Watarana, ina bakin aikina, aka kawo mara lafiya, babbar mace ce, mai yara da yawa duk maza, na karb'eta a gaggauce saboda yanayin jikinta ya tsananta, ciwon zuciya ne take fama da shi, tana buk'atar kulawa sosai, sannan gwaje-gwajen da za a yi mata ma su tsada ne, kafin ma a kai kan magunguna, kuma yaran nata duk ba ma su k'arfi ba ne, don haka take kwance a asibitin suna neman kud'ad'en.
Kwanaki biyu da kawo ta, na shiga duba ta, sai na tarar da wata yarinya zaune a gefen ta, ta na sharar k'walla, ita kuma matar ta na yi wa yarinyar maganar da suka katse, saboda shigowa ta, sai ta gaishe ni, ta matsa gefe.
"Lafiya lau, ya mai jiki?" Na amsa idanuna yana yawo a duka surarta, kyakkyawa ce, komai ya ji, ni kuma dama kun san ni da kyakkyawa, bare kuma yanzu da na gama sanin muhimmancin mace
"Da sauk'i" Ta fad'a ta na goge hawayen har lokacin.
Na ce"ki daina damuwa, za ta samu lafiya in sha Allah!"
Ta gyad'a mini kai.
"To ki bar kukan haka, ya sunan ki?" Na tambaye ta.
"Aisha!" Ta ba ni amsa.
"Nice!" Na fad'a ina kashe mata ido, sannan na gai da mahaifiyar tata, na fara aikina.
Wunin ranar sai Aisha ta tsaya mini a rai, yarinyar ta yi mini, na dinga ayyana yadda komai nata zai kasance da ace zan yi nasarar cim ma gaci, bayan na koma gida kawai sai na yi tunanin mai zai hana na biya musu kud'in da suke buk'ata, domin na samu nasarar shigar da kaina wurin ta, ko Allah zai ba ni nasara na shigar da ita kwana ta, na saka a raina zan gwada, amma gaskiya ni yanzu soyayya b'ata lokaci ce a tsari na, don ina ji a jikina ba zan tab'a son wata bayan Khairi, to na yi k'aryar soyayya mu rabu kamar yadda muka yi da Ni'ima, ai gara kawai kai tsaye na dinga bayyana abin da ya kai ni, idan yarinya tana iyawa a yi, idan ba ta yi, na k'arawa motata mai.
Washegari da kuzarina na je asibiti, na yi sa'ar ganin Aisha zaune a inda majinyata suka saba zama, da hannu na kira ta, sannan na wuce office dina, ta biyo bayana.
Ina tsaye ina saita takardun tuburin ta shigo da sallama, na amsa, na zauna, sannan na nuna mata kujera, ta gaishe ni, ban amsa ba ina bin ta da kallo, sai ta sunkuyar da kai.
Na ce"wacce kike jinya mahaifiyarki ce ko?"
Ta ce"Kakata ce".
Na jinjina kai, na ce"rayuwarta ta na cikin had'ari fa, kun k'i yin abin da ya dace, ko kuna son ku rasa ta ne?"
Idonta ya ciko da k'walla, ta ce"ba haka ba ne, kud'in suke had'awa".
Na ce"to Allah ya rufa asiri. Amma ya za ki ji idan na d'auki nauyin jinyarta gabad'aya?"
Sai ta kalle ni, ta ce"Zan ji dad'i sosai, kuma ba za mu manta da kai ba, za mu yi maka addu'a".
"Kawai!?" Na fad'a ina narkar da idanuna a kanta.
Sai ta sunkuyar da kai.
Na ce"da ace za ki iya ba ni tukuici da na biya muku kud'in komai a yau!".
"Ban san wane tukuici kake so ba" Ta fad'a muryarta da sanyi.
Ina karkada biron hannunna, idanuna a jikinta, na ce"za ki iya bari na shiga cikin rayuwarki ko da na awanni biyu ne?"
"Kamar ya?" Ta tambaye ni.
"Ta hanyar amincewa da buk'ata ta, mu samu kusanci mafi kusa ni da ke" Na fad'a murmushi a kan fuskata.
Sai ta girgiza mini kai, ta ce"a'a likita, ni ba haka nake ba!"
Ta tashi ta fice, ina kiranta ko juyowa ba ta yi ba, na kifa kaina a teburin na sakanni, ina tunanin yadda nake k'ok'arin zama mara kunya, sannan na d'ago, na fara aikina tuk'uru, kamar babu tabon komai a zuciyata.
A ranar na sake tsorata su da cewar muddin ba a yi gwaje-gwajen, an sayi magunguna tsakanin kwana biyu ba, za ta iya rasa rayuwarta, duka na ga damuwa a fuskokin su, musamman Aisha da ta fara kuka sosai, bayan na lura duk mazan sun tafi, sai na koma d'akin, na tarar kakar tata tana bacci, na kira Aisha.
Ta jima, har na fara tunanin ba za ta zo ba, sai ga ta ta shigo jiki a mace, na yi mata kyakkyawan murmushi, ta maze kamar ba ta gani ba, ta zauna.
Na ce"Aisha da alama ba ki damu da kakarki ba".
Ta ce"likita fad'a mini bukatarka kai tsaye".
Na ce"za ki iya bi na mu tsallaka hotel mafi kusa? Awa biyu kacal!".
Ta ce"yaushe za ka biya kud'in?"
Na ce"idan kika amince".
"Ka fara biya, zan amince!" Ta fad'a.
Na jinjina mata kai, ta fita na bi ta da kallo.
A ranar na biya kud'in duka gwaje-gwajen, da za a yi mata, ina ta zumud'i, su kuma suna ta yi mini godiya, kamar za su durk'usa, ita ma mara lafiyar sosai ta yi mini addu'ar gamawa lafiya, har da kukanta, ban da Aisha da take wani d'auke mini kai.
Washegari muka tsara yadda za mu had'u, sai na yi wa mara lafiyar allurar bacci dab da zan tashi daga aiki, na fita na jira Aisha a waje, ta fito ta shiga motata, muka d'auki hanya, ina cike da shauk'i.
Sosai na yi mamaki lokacin da na gano wani ya riga ni, shiga hurumin Aisha, amma har gara ita akan Nabila, da na tambaye ta, ta na kukan da tun da muka shiga hotel din take yi, ta ce"An tab'a yi mini fyad'e! Shi yasa ma na koma gidan Kakata da zama".
"Na ce"shi ne kika yaudare ni, na yi shirin tunkarar sabuwa?"
Ta yi shiru.
Na ce"to na biya kud'in gwaji, ba zan biya na maganin ba".
Tana kuka ta ce"don Allah ka yi hak'uri ka biya duka, kamar yadda ka yi alk'awari, ka karashe ladanka".
Na ce"idan ke ma za ki karashe naki ladan, ina nufin gobe da jibi".
Ta ce"na amince".
Haka muka jera kwanaki uku muna fita, kuma babu wanda ya gane, na biya musu duka kud'in da suke buk'ata, daga nan na nemi yardarta, idan tana so za mu ci gaba da had'uwa, ina biyanta, sai ta ce a'a, wannan ma dole ce ta kai ta.
Haka suka gama suka bar asibitin, nayi kewarta na kwanaki na watsar, tun da ko lambarta ban karb'a ba. Na yi zaton na gama da tarihinta, ashe akwai sauran rina a kaba, a kanta na gane ba ko'ina mutum yake shiga ya fito lafiya ba.
Rana d'aya Nabila ta rikid'e mini, ta daina shakkata, har ta kai tana iya tunkara ta, ta ce na ba ta hakkinta ko ta had'a ni da iyayena, tsanarta ta k'aru a zuciyata, to ni ba zan iya dukan mace ba, bare na saka bulala na zane ta, duk wulak'ancin duniyar nan, da maganganu marasa dad'i na yi mata, amma ko a jikinta, k'arshe sai ta hada ni da mahaifiyata, ta ce ba na cin abinci, ba na kula ta, kuma ina cin mutuncin ta da zagi kala-kala.
Ranar dai dukana ne kawai Ummi ba ta yi ba, ta dinga yi mini fad'a, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, raina ya b'aci sosai, kuma na sa a raina zan ba wa Nabila hakkinta, amma Ummi ba za ta sa na so wata bayan Khairi ba.
Bayan kwana biyu da na kusanci Nabila sai na ga bambanci sosai da wancen daren, har susuta ni ta so yi, haka na raba dare tare da ida, kuma daga ranar na sakko, na dawo ziyarta ta, amma hakan bai sa na daina yi mata kallon shara ba, bare na rabu da Siyama wacce ta kara zage damtse wurin faranta mini, don har ta had'a ni da kawayenta biyu, suka had'u su uku suka mai da ni sususu, saura kad'an su mai da ni d'an taure. [11/28, 11:28 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕