Mataccen buri

Page 12

by @sadiyaabdulrazak954

Watarana ina tsaka da aikina, ka'in da na'in, sai na ji hayaniya ta wajan ofishina, babu jimawa kuma aka banko k'ofar, maza sun kusa su goma suka shigo, ga security biye da su, suna kokowar fitar da su, sai fizgewa suke suna fad'in "Ina yake? Wallahi yau sai mun dandatse shi!".

Na tashi tsaye a firgice ina rarraba ido, don dama can ni ba mai rigima ba ne, ban tab'a yin fad'a da wani ba, kafin bakina ya kai ga tambayar su wanda suke nema, tuni wani ya k'araso ya wanke ni da mahaukacin mari, don har gefen idona ya tab'a, ya fizgo ni ya watsar a wurin, yana fad'in"yau sai na ga k'arshen iskancin ka! Sai ka san ka tab'a mai gata, banza mazinaci!".

Daidai nan kuma abokan aikina suka shigo, suka nemi jin ba'asi, wanda na lura ya fi su nutsuwa shi ya ce"wata biyu da suka wuce mun yi jinyar mahaifiyar mu a asibitin nan, akwai yarinyar da take kula da ita, to wannan likitan da kake gani, ya yaudareta, ta hanyar biyan kud'in magani, ya yi mata ciki".

Zuciyata ta buga da k'arfi, lokaci daya na gane 'yan'uwan Aisha ne, da k'yar na bud'e baki na ce" ni fa ban yi wa Aisha tilas ba, ita ta ga za ta iya, kuma zancen ciki, ban san da shi ba, dama can ta saba yawon ta, don haka ku je ta nuna muku uban cikinta, ba dai ni ba!".

Hayaniya ta kaure, zage-zage ne kawai yake tashi, wasu har suna fizgewa za su dake ni, ana kare ni, daga k'arshe dai sai wurin manyan asibitin aka mik'a mu duka, tun da an kasa sasantawa. Bayan an zube zance a faifai, hukumar asibiti ta ba su hak'uri, da alk'awarin biyan su duk abin da suke buk'ata, sannan ku kawo Aisha a zubar da cikin, ni kuma za su hukunta ni, da k'yar suka amince aka tsaya akan hakan.

Na ji dad'i sosai, a zatona asirina zai rufu, ashe sun so rufe maganar ne saboda kar sunan asibitin ya b'aci, a ranar suka ba ni takardar sallama, ma'ana an kore ni daga aiki, kuma suka nuna mini wannan shi ne babban adalcin da suka yi mini, don zunubin da na aikata ba k'arami ba ne a wurin su.

Tashin hankalin da na shiga baki ba ya iya furta shi, ji na ina ma mafarki nake yi, ina matuk'ar son aikina, kuma ban yi mafarkin rasa shi a daidai wannan lokacin ba.

Haka na koma gida jiki a mace, ina jina kamar ba ni ba, da daddare na je gida, kaina a k'asa na mik'awa Abba takardar sallamar, bayan ya karanta ya kalle ni, mamaki shimfide a fuskar shi ya ce"Saifullahi! Akan wane dalili aka kore ka daga aiki?"

"Abba matsala aka samu, kuma don Allah kar a wani tsaya tone-tone, haka Allah ya k'addara". Na fad'a kamar zan yi kuka.

Abba ya ce"ka san ka yi laifi kenan! Idan ba ka sanar da ni komai ba, wa za ka sanarwa?"

Duk yadda ya so ji daga bakina, ban fad'a masa ba, karshe cikin fad'a ya ce na tashi na bar masa gida, babu musu na fice na bar shi da takardar. Washegari sai ya je asibitin da kan shi, ya ji komai, wayyo! Ranar na yi nadamar halina, ya dinga yi mini fad'a, ina jin k'una a zuciyata, Ummi ma ta d'ora da nata, har tana fad'in sai ta raba aurena da Nabila, kar na kwaso wata cutar na shafa mata, haka suka yi suka gama, sannan na tashi na tafi a sanyaye, kwana biyun ji na nake kamar ba ni ba, ga Siyama ta matsa min tana so mu had'u, ni kuma sam ba na cikin yanayin, don kulle d'akina ma nake, Nabila ta karaci nocking ta hak'ura. To da yake ya zamar mini jiki, jimamin na sati d'aya na yi, sai na ware na manta komai, na koma sharholiya ta, abun ma sai ya fi na da.

Wata d'aya na yi, ba ni da aikin yi, sai kud'in account d'ina nake ta facaka da shi, ina bautawa mata, na zama k'wararre ko yau na fara ganin mace zan tunkare ta, ba na wata fargaba, suka koya mini shiga clubs kala-kala, a nan kuma na samu wasu abokan da suka fi ni gogewa a harkar, na hau hanya d'od'ar!.

Daga baya sai Abba ya bud'e mini shago a kasuwar Sabon gari, wannan kuma shi ya sake tunzura ni, na zama d'an watangaririyar da gaske, to shagon nawa ba ya rabo da mata, daga wannan sun fita wasu za su shigo, duk wacce na ga ta yi mini sai na karb'i lambarta, idan na ji 'yar'uwa ce, mu had'u a hotel, idan na ji nutsattsiya ce na share ta.

Watarana, ina shagona, kamar a mafarki sai ga kiran Ummul-khairi, abun ya ba ni mamaki sosai, don ban yi zaton har lokacin tana da lambata ba, na katse na kira ta, ta d'aga ta yi shiru, na yi sallama tare da kiran sunan ta, ta amsa muka gaisa sama-sama, kafin na ce"Khairi kin manta ni ko?"

Muryarta tana rawa ta ce"ba haka ba ne".

Na ce"to ya ne?"

Ta ce"don Allah wani taimako nake nema a wurinka idan zan samu".

Na ce"Allah ya sa zan iya!".

Ta d'an yi jim, kafin ta ce"ciwo na ji, zan zo asibiti ka yi mini treatment".

Gabana ya fad'i na ce"wane irin ciwo? Kuma ina mijinki?"

Sai ta fara kukanta da yake azabtar da zuciyata ta ce"mijina ne ya dake ni".

Na tashi daga zaunen da nake, na ce"haukan na shi har ya kai nan! Kuma kike zaune da shi Khairi?"

Ta ce"ni dai zan zo".

Na ce"ina iyayen shi? Me ya sa ba za ki sanar musu, kuma ki nuna musu abin da ya yi miki ba?"

Sai ta fara kuka, ta ce"daga gidan nake ai, ba sa goyon bayana!".

Raina ya b'aci sosai, na yi wani huci, na ce"kina ina? Ina ne gidan naki?"

Ta kwatanta mini, na ce zan zo na d'auke ta, sai da na koma gida na ajiye babur dina, na d'akko mota, sannan bi kwatancen nata, na tsaya a bakin titi, ta fito ta shiga motar, na tsaya ina kallon yadda jini duk ya b'ata mata gaban hijjabi, sai ta kifa kai tana kuka.

Na yi k'wafa, zuciyata tana zafi, na ja motar muka fara tafiya, kai tsaye gidana na kai ta, sai da muka k'arasa ta ji na bud'e motar zan fita sannan ta d'ago ta kalle ni, idanunta sun yi jawur.

"Gidana ne, ina da kayan aikin" Na fad'a don na san tambayar da za ta yi mini kenan.

Sai ta girgiza mini kai, ta ce"asibiti ya kamata, ba gidanka ba".

Na ce"Ai ba mu keb'e ba, tun da ina da mata, sannan yanzu ba na aiki a asibiti, a kasuwa nake".

Ta ce"matar taka fa idan ta ce wace ce ni?"

"Sai na fad'a mata muradin raina ce ke, idan ta ja zancen kuma, na nuna mata kin fi kowace mace muhimmanci a wurina".

Ba ta ce komai ba, na je na bud'e gate din, na dawo na shigar da motar, muka shiga falon.

Babu kowa a ciki, watak'il tana bedroom ne, na shiga d'akin da kayan aikin suke, na d'akko na yi mata treatment cikin takatsantsan, kamar fatar jikina ce, sannan na tashi na shiga d'akin Nabila, sai na ganta kwance tana bacci, na bud'e sif d'inta na ciro hijjabi, ina juyowa muka yi ido hud'u da ita.

"Ina da bak'uwa ne!" Na fad'a, a dake ina tsare gida.

Sai ta tashi zaune, ta ce"wace ce?"

"Mai daraja ce, treatment na yi mata, idan ta huta za ta tafi, sannan ba zan jure ko kallon banza ki yi mata ba!".

Daga haka na fice daga d'akin, aikuwa ta mara mini baya, na mik'awa Khairi hijjabin na ce"ki cire wannan ya b'aci".

Ta karb'a ta ce"na gode".

Sai ta kalli Nabila ta gaishe ta.

Nabila ta ce"baiwar Allah daga ina?"

Sai Khairi ta kalle ni, ta mik'e tsaye za ta fita.

Na ce"dawo ki zauna Khairi, ki ci abinci, ki huta, akwai maganar da za mu yi ma".

Ta ce"haka ma na gode Saifu".

Ta fita, sai na bi ta a baya, muka shiga mota, maimakon na ja mu tafi, sai na saka key, na juyo ina fuskantar ta. [12/1, 10:22 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕