Page 13
"Ki canza hijjabin". Na ba ta umarni.
Sai na kau da idona daga kallon ta, har ta canza, sannan na juyo ina k'are mata kallo na ce"Khairi kin rame sosai! Kenan dai da gaske mijinki mahaukaci ne, har dukan ki yake yi, amma kike zaune da shi, ba kya tsoron wani abu ya faru?"
Ta ce"yanzu da hankalin shi ya warke, tun wata d'aya da auren".
Na ce"ina wata waraka ga wanda zai daki mace kamar ki, kuma ma kina cikin inuwar auren shi?"
Sai ta share hawaye ta ce"da gaske ya warke, amma na sha wuya kafin ya warke, da haukan suka aura masa ni suna sane, duk dare kamar zai kashe ni, wai ta hakan ne zai warke, wata d'aya da auren ya yi rashin lafiya sosai, daga nan ya samu lafiya..."
"Sorry!" Na katse ta, ina jin mugun tausayin ta.
Sai ta share hawaye, ta ce"Saifullahi, da ya samu lafiya sai na zama shara a wurin shi, ni yake wulak'antawa, wulak'ancin da ko da yana mahaukaci bai yi mini irin shi ba, idan na kai k'arar shi sai dai ace na yi hak'uri, yanzu ma sun daina ba ni gaskiya, babu dama na yi magana sai su ce kishi nake yi, aure zai k'ara, har an saka rana, shi ne yake ta yi min wulak'anci, idan na rama ya dake ni".
Da ace Khairi ta san yadda labarin nan zai bak'anta zuciyata na san da ba ta ba ni ba, na ji kamar na sa a d'aure mijin nata har k'arshen rayuwar shi, idona ya ciko da k'wallar tausayin ta, na kalle ta na ce"Khairi! Kina cikin damuwa, me ya sa ba za ki sawwakewa kan ki ba?"
Sai ta kalle ni, tana goge hawaye ta ce"ban gane ba".
Na ce"jikina ya jima yana ba ni duk duniya babu wata mace da zan so bayan ke, don haka don kin auri wani kafin ni ba zai rage komai daga son da nake yi miki ba, wannan rayuwar da kike yi yanzu an daina yin irin ta, ki samawa kan ki 'yanci, ki san abin da ya fi dacewa da ruyuwarki, ba sai wani ya fad'a miki ba, ina nufin kawai ki kashe wannan wahalallen auren, ki zo mu gina rayuwa mai haske, ki mori soyayya, kuma na karantar da ke gard'in zamantakewar aure".
Sai ta girgiza mini kai, ta ce"wannan kuma Allah yana sane da ni, ina neman zab'i a wurin shi, sannan yanzu haka ina da ciki, ka ga Allah ya k'addara akwai rabo a tsakanin mu".
Wani sabon kishin ya rufe ni, wanda har na kasa dannewa, sai da ya bayyana a fuskata, na ce"Khairi! Da irin wannan mijin za ki had'a zuri'a?"
"Haka Allah ya tsara mini" Ta fad'a a sanyaye.
Na girgiza kai, na ce"kar ki kashe rayuwarki akan wanda bai san halacci ba, ina rok'on alfarma d'aya a wurin ki, don Allah ki zubar da cikin jikinki, sannan kar ki sake yarda ki samu wani, ki jira har ya k'aro auren ki ga kamun ludayin shi tukunna".
"Amma Saif..."
Sai na katse ta da fad'in"ki yi mini wannan alfarmar don girman Allah! Daga jin irin wannan rashin mutuncin ko ba yau ba zai sake ki, to idan haka ne meye amfanin fara haihuwa da shi? Kar ki raba mini kan 'ya'ya don Allah!".
Sai ta yi mini kallon mamaki. Ni ma kuma sai daga baya na gane na yi sub'ul da baka, amma abin da yake zuciyata ne na furta, saboda jin kalar zaman su ya sa na fara hasashen cikar burina, na janye idona daga kallon ta, na yi shiru.
"Ka bud'e mini zan koma gida". Ta fad'a ta na linke hijjabin hannunta.
Na ce"mu je na sauke ki".
"A'a".
"Me ya sa?" Na tambaya,ina kallon ta, son ta yana fizga ta, ina jin kamar na shigar da ita jikina ko zan samu sassaucin azalzalar da zuciyata take yi mini.
"Kawai zan koma ni kad'ai" Ta fad'a.
Sai na ja motar, muka yi tafiya mai nisa kafin na ce"duk taimakon da kike buk'ata ki tuntub'e ni, zan yi miki wanda ba zai gagara ba in sha Allah! Yanzu ki ba ni account details din ki" Na k'arasa maganar ina ajiye mata wayata akan cinyarta.
"A'a! Na gode". Ta fad'a muryarta na rawa.
Na girgiza kai na ce"Khairi! Ni da ke mun zama d'aya, bai kamata ki dinga b'oye mini wani abu na rayuwarki ba, kamar yadda ni ma ba zan iya b'oye miki ba, zan iya sanar da ke duk kalar rayuwar da nake yi, da yak'inini idan kin jin za ki tausaya mini, ki ba ni mafita, ba za ki guje ni ba".
Ba ta ce komai ba, ta dai d'auki wayar tana wasa da ita.
Na sauke numfashi na ce"daga yau duk lokacin da na ji ana lissafin dolayen maza, marasa sa'ar rayuwa, dole zan saka da mijinki, ina ma a ce ni ne na same ki, da ba ma zan bari kina fita ke d'aya ba, bare wani ya kalle ki a bayan idona, ba zan bari ki ci gaba da bayyana kyakkyawar fuskarki ga kowa ba, sai dai ki dinga rufe ta, adonki ya zama nawa ne ni d'aya, Allah bai tattabar mini ba Khairi!".
"Ka sauke ni a nan!" Ta fad'a, ba tare da ta bi ta kan sauran maganganuna ba.
Sai na tsaya, ina kallon ta na ce"me kike buk'ata? Kuma na ce ki saka mini account number".
Ta ce"ba na buk'atar komai ba, na san ina da gata a wurin ka, shi ya sa na nemi taimakon ka, na gode hakan ma, Allah ya saka".
Sai na cire key d'in motar, na yi mata murmushi na ce"babu godiya, wannan dole na ne".
Ita ma ta yi guntun murmushi, ta fita, ni ma na fito, na tsayar mata adaidaita, na biya kud'in, ta shiga suka tafi, zuciyata kamar za ta yi magana.
Ban iya komawa kasuwa ba, sai gida na yi, na tarar da Nabila zaune a falo, ta ci kwalliya ta kashe d'aurin da yake burge ni, na ture ka ga tsiya, amma duk da hakan kallo d'aya na yi mata ina shirin shiga d'akina, ta taso a tsiwace ta ce"Yaya Saifu, wai wace ce wannan d'in!?"
"Mantuwa kika fara kenan! Na ga dai tun shigowar mu na sanar miki, to bari na maimaita miki, ita ce wacce nake so, ita ce wacce ta kere duka matan duniya a idona, mai k'ima da mutunci, wacce nake da tabbacin ta kai mutuncinta gidan aurenta, duk da dai ba ta yi dace ba!".
Nabila ta ce"me kake son fad'a mini ne?"
"Ai ke dak'ik'iya ce, ba lallai ki fahimta ba! To macen da ta iya bawa wani banza d'an iskan gari kanta a titi, ta lullub'e ta zo wa mijinta a salon saliha, kuma a dak'ik'in tunanin ta wai ba zai gane ba, ai wannan ta cancanci matsayin sarauniyar dak'ik'an duniya!".
Muryarta tana rawa ta ce"dak'ik'an suna da yawa! Muddin da aurenta, ta biyo ka har gida wai da k'aryar ta ji ciwo, to ita ce babbar dak'ikiya, sannan kai ma da ka..."
Ba ta k'arasa ba na d'auke ta da wani zazzafan mari, don ni kaina sai da na ji zafin a hannuna, ta saka ni na yi abin da ban tab'a yi ba, dukan mace, da ta san matsayin Khairi a zuciyata da ba ta yi kuskuren yi mata kallon banza ba ko da a bayan idona, bare kuma ga ni ga ta, ta kalle ni ta danganta ta da kalmar dak'ik'anci.
Nabila ta dafe kuncinta, tana hawaye ta ce"ni ka mara saboda wata banza? Banzar ma matar wani?"
Da k'yar na danne zuciyata ban k'ara mata marin ba, da dukan mace halina ne, da yau duk wayoyin gidan nan sai sun tsinke a jikinta.
Na jinjina kai, zuciyata na k'una, na ce"idan kika sake furta wata kalma makamanciyar wannan akan Khairi, to sunanki sakakkiya, ina nufin na sake ki! Idan kina son zama da ni, dole ki kau da kai a duk lamurana, kuma ki sa wa ranki, idan za ki yi kishi da Khairi, to za ki yi da uwarki!".
Daga haka na shige d'akin, na yi wanka, na fice daga gidan zuciyata na yi mini zafi har lokacin. A hankali nake tafiya cikin unguwar tamu, ba ni da tak'amaiman wurin zuwa, shi ya sa ma ban d'auki abun hawa ba, suffofin Khairi kawai nake hangowa, wacce ba ta canza komai ba, sai ramar da ta yi, muryarta tana nan da sanyi, kamar yadda na san ta, da alama sanyin halinta da rashin kwad'ayin ta ma duk suna nan, ba su canza ba, zuciyata ta yi mini nauyi, har numfashina ya fara gargada, daidai lokacin da na k'araso dandamalin k'ofar wani gida, sai na zauna, ina sauke numfashi, hoton ta na dubo a wayata, na yi zooming ina kallo, na furta "Allah ne shaidata, Khairi ina son ki, har abada!".
Na yi nisa sosai a tunanin ta, don na manta ma inda nake, kwatsam na ji muryar mace kusa da ni, ta ce"Malam zan yi aiki a wurin".
Na d'ago idona mai cike da ruwan hawaye, na zube a kanta, sai na sakar mata murmushin da ban shirya ba, yarinyar ce da kallo d'aya na yi mata na san ba ta kai shekaru ashirin ba, black beauty, ta ci kwalliya, sai na kalli murhun da ta ajiye nesa da ni, ban ce komai ba, kallon ta kawai nake yi, har ta juya ta koma cikin gidan, ta sake fitowa ban motsa ba.
"Nan wurin sana'ata ne fa!" Ta sake yi mini magana.
Sai na yi murmushi na ce"na sani, ai siya na zo na yi, tun d'azu nake jiran ki!" Na k'arashe maganar ina d'age mata gira, sannan na tashi, ta saita komai ta hura wuta, na koma na zauna, ina cewa"ya ma sunanki?"
"Ummi!" Ta fad'a, hankalin ta yana kan aikinta.
Na ce"Ai Ummi ba sunan gaskiya ba ne, ko dai sunan mai tsada ne, sai na siya? To dubu nawa ne yanzu na nemi ATM mafi kusa?"
Sai ta yi dariya ta ce"sunana Sa'adatu".
Na ce"ma sha Allah! Tun kafin ki fad'a ai na ga alama, don sunan ya dace da ke. Ni kuma Sunana Saifullahi, awara kike siyarwa ko?"
Ta ce"ita ce, ta dubu nawa za ka siya?"
Na yi dariya ina mai da wayata aljihu, don an zo gab'ar da nake so a kai, na ce"haba dai! Ina za a samu mazubin zuba awarar dubu a cikina? Gwauro nake fa, aminin filo, sai dai idan har mai awarar zan siya, to wannan na ji ko ta dubu hamsin zan iya!".
Sai ta yi mini wani kallo, ta ce"haba dai! Ai ni na wuce a siye ni".
"Gangar jikin ko kuma zuciyar?" Na tambaye ta, ina fatan 'yar hannu ce, kawai mu daidaita, don har ga Allah ta yi mini.
"Wai me kake nufi ne?" Ta tambaye ni.
Na ce"abin da kika yi zato shi nake nufi".
Ta ce"zuciyata mai tsada ce, ba kowa ne zai iya siya ba".
Na yi dariya na ce"to ki ba ni dama na taya mana, kika sani ko ina da kud'in siyan?"
Sai ta yi dariya, ba ta ce komai ba.
Ni na yi ta mata surutu, har ta juye kaskon farko, na siye na linka mata kud'in, sannan na yi nasarar samun lambarta. [12/4, 9:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕