Mataccen buri

Page 14

by @sadiyaabdulrazak954

Da na koma gida ban tarar da Nabila ba, kuma ban neme ta ba, ban runtsa ba, sai da na tabbatar Sa'adatu ta zo kusa da tarkona, k'iris ya rage na cim ma gaci, nan kuma tunanin Khairi ya dawo mini sabo, na dinga tuna duk abubuwan da suka faru a baya, kamar yau ne suka faru, son ta ya dinga ragargazar zuciyata, na ji kamar na kira ta, sai kuma zuciya ta hane ni, haka na yi bacci cike da kewar ta.

Washegari na je gaishe da Ummi kafin na tafi kasuwa, sai na ga Nabila zaune a falo cikin k'annaina, na yi mata kallo d'aya na wuce, bayan mun gaisa da Ummi a nutse ta ce"Saifulllahi ashe mata ka fara kawowa gidanka?"

Na juya na harari k'ofa, kamar an ce min Nabila tana tsaye, na ce"haba Ummi, wasu mata kuma?"

Ta ce"to wace ce yarinyar da ka kawo jiya, wai har ka yi mata treatment a cikin gidanka, ka ba ta hijjabin matarka, kuma kuka shiga mota kuka fita?"

"Ba fa wata ba ce, Khairi ce". Na fad'a kai tsaye, don ban ga amfanin k'aryar ba.

"Khairi!" Ta fad'a da k'arfi.

Na sunkuyar da kai.

Ta ce"ba ka ce ta yi aure ba? Ko auren mutuwa ya yi, har ka fara zawarcin ta?"

"I, ya mutu!" Na fad'a, ina tashi zan tafi.

Ta ce"Allah ya kyauta to! Nabila kuma za ta zauna a nan, har sai ranar da ka san muhimmancin ta!".

"To Ummi" Na fad'a ina ficewa.

Ai ba k'aramin dad'in hukuncin Ummi na ji ba, sai na huta da yawon kama hotels, nake gayyato matan har cikin gidana, mu kwana hankali kwance. Cikin sati biyu na jirkita tunanin wannan mai awarar ita ma, ta zo gidana mu ga k'are zance, mace ta biyu da ni ne na fara shiga huruminta, daga nan kuma ban sake bi ta kanta ba, don kud'i mai nauyi na biya ta.

Bayan wasu kwanaki, na je duba abokina Hafiz bisa rashin lafiyar da yake yi, karaf na ci karo da k'anwar shi, na san yana da k'annai mata, amma ban san su a ido ba, duk yadda na so na fi k'arfin zuciyata akan Mariya abu ya ci tura, na riga na mai da kaina wani d'an taure, ba fa na iya gani na bari, ko da a wurin kunya ne, nan na karb'i lambarta ba tare da sanin Hafiz ba, babu wani musu ta amince da k'aryar soyayyata, na kwantar da kai kamar gaske kullum ina yi mata kalamai a waya, ina yi ina shigar da manufata a hankali, da farko ta so turjewa, amma da na nuna mata abun iya waya zai tsaya, sai ta saki jiki, haka zan ta yi mata zancen banza, ina saka ta mayar mini da martani, tun tana rab'e-rab'e har ta ware.

Cikin haka ne kuma Hafiz ya ankara, don ko da wasa ban nuna masa ba, ranar har gidana ya zo, bayan mun gaisa, na fahimci akwai matsala, na ce"Hafiz ya aka yi?"

Ya ce"Saifullahi, meye dalilin b'oye min alak'arku da Mariya in dai har soyayyar gaskiya kake yi mata?"

Na d'an ji damm! Amma na dake na yi murmushi na ce"me kake tunani? Tun bayan rasa Khairi na ba ka labarin wata da nake so, nare har abun ya kai ga yaudara?"

Hafiz ya ce"Saif! Na san ka da son mata, duk da dai ba sosai kake kula su ba, kuma kai da bakinka ka ce, duk wani so da ba na Khairi ba, k'arya ne har zuciyarka, matarka ma duk da ta kasance jininka, kuma wacce kake tausayi a baya, ba ka so ta ba, duk da kana da tabbacin ka rasa Khairin, to ina ga Mariya wacce ka gani rana tsaka?"

Sai na yi shiru, ina jin idan na yaudari Mariya kamar na ci amanar amintarmu da Hafiz, yanzu kuma idan na sare da wuri zai gane dama can ba da gaske nake son ta ba.

Ya ce"idan ka san ba aurenta za ka yi ba, Saif don Allah ka fita daga rayuwarta, don tana da wanda aka yi wa alk'awari, tana son shi, amma yanzu saboda kai duk ta canza masa, na zaunar da ita na tambaye ta, sai ta ce mini kai take so, ta fasa wancen d'in, to idan da gaske kake mun baka, sannan sati d'aya muka ba ka, ka turo a yi zancen aure!".

Sai na yi dariya ina kai masa duka na ce"sati ai da yawa Baba, da ka sani ka ce awa daya".

Hafiz ya ce"ba fa wasa nake yi ba, na ba ka umarni ne a matsayin yayan Mariya, ba abokinka ba!".

Na ce"ba mu gama fahimtar juna ba, ku ba ni sati uku in sha Allah!".

Ya ce"Allah ya yarda".

Muka d'an tab'a fira, ya tafi.

Ina kasuwa ina ta nazari, shin na yi sauri na aiwatar da k'udurina akan Mariya kafin cikar sati ukun, idan lokacin ya yi sai na ce su k'ara min, na yi ta raina musu wayo, har su gane ba da gaske ba ne, ko kuma dai kawai na hak'ura, mu rabu salun-alun? Zuciyata ta fi nutsuwa da mu rabun, saboda ina kunyar Hafiz, kuma idan da kara k'anwar shi k'anwata ce, mun jima da shi, kuma ya yarda da ni, bai cancanci haka daga gare ni ba, da wannan tunanin na yanke shawarar rabuwa da ita, amma inaa! K'addara ta riga fata.

Da na je mata da zancen rabuwa, sai ta tashi hankalin ta, har tana ba ni hak'uri, duk da babu laifin da ta yi mini, sai na gane ita ma irin Ni'ima ce, ma su zurfafawa akan so, don haka ban wani sha wuya ba, a lokacin da na ce mata ta zo gidana sai mu yi maganar a nutse, na ba ta address ta zo, duk yadda na so fahimtar da ita mu hak'ura ba yanzu zan k'ara aure ba, sai ta kasa fahimta, ta dinga rok'ona, har da kukan ta, ta ce za ta jira ni, duk lokacin da zan k'ara auren, nan shaid'an tare da taimakon rafkananniyar zuciyata suka yi nasarar canza tunanina, na ce mata abu d'aya za ta yi na yarda za ta jira ni, ta ba ni kanta sau d'aya kacal! Shi ne zan san da gaske take so na, kuma na yarda za ta jira ni, tun da ba za ta je wa wani ba, bayan ta san ta ba ni kyautar, da farko ba ta yarda ba, amma da na dage da kalaman yaudara, da kuma taimakon son da take yi mini, sai ta amince, a wannan ranar Mariya ta zama mace ta uku da na lalata, wanda na jima ina nadamar aikata hakan. Haka muka ci gaba da waya da ita, amma na ja baya sosai, don sai ta neme ni, nake neman ta.

Watarana bayan sallar isha'i Khairi ta kira ni, tana kuka take fad'a min, mijinta ya watso mata duka kayan d'akinta waje, saboda wacce zai aura ta ce d'akunan da take ciki su take so, ita kuma Khairin ta kafe akan ba za ta bar d'akunanta ba.

Zuciyata ta fara zafi, na ce"Khairi wannan wace kalar rayuwa kike yi ne? A hakan kike cewa ya warke? Don Allah ki tafi gidanku haka!".

Ta ce"ai daga gidan nake, na je kai musu k'ara sai na tarar da kayan duka a tsakar gida, kuma ya kulle d'akin, kuma dama sun ce na yi hak'uri na zauna a inda ya ce d'in!". Ta k'arashe maganar da shasshek'ar kuka.

Na sauke numfashi na ce"to ki yi hak'urin Khairi, ki koma inda ya ce d'in".

"Daki d'aya ne fa! Ta ya zai cinye kayana?" Ta tambaye ni.

Na ce"to idan ban ce miki hakan ba, me zan ce? Ke dai ban kai wanda zai ba ki shawara ki bi ba, da za ki d'auki shawarwari na, da rayuwarki ta gyaru, kin zauna cikin 'yanci da soyayya!".

Sai ta yi shiru, kamar ba ta ji na.

Na ce"da farko dai shi wannan mijin naki, mahaukaci ne na gaske, kuma babu alamun zai warke, don duk mahaukacin da ya aure ki, ya samu kulawa daga gare ki, har tsawon watanni bai warke ba, to ba zai warke ba! Yanzu idan kin haihu da mahaukaci, kina tunanin zai iya kula da d'anki? Ko kina ganin yana da nutsuwar da zai ba shi tarbiyya?"

"Ko bai yi ba, ni zan yi daidai gwargwado!" Ta fad'a da k'warin gwiwarta.

Na yi murmushin takaici, zuciyata cike da ciwon rashin ta, na ce"Khairi nutsuwa ce kad'ai take ba da nutsuwa, farin ciki shi yake ba da farin ciki, sai kin samu ingantacciyar rayuwa da kwanciyar hankali, kafin wanda suke k'ark'ashin kulawar ki su samu, idan zan fad'a miki ki ji, to ki zubar da cikin jikinki, matuk'ar bai yi k'warin da zubarwar zai zama baraza ga rayuwarki ba!".

Ta ce"ni kaina ina fargabar fara had'a zuri'a da shi, saboda rashin mutuncin shi kullum k'ara gaba yake, amma kuma babu kyau zubar da ciki, sannan ina jin tsoro!".

"Wata nawa ne cikin?" Na tambaye ta.

Ta ce"biyu ne!"

Na ce"idan kin amince, zan kawo miki magani ki sha ya zube".

Sai ta yi shiru, ba ta amsa mini ba.

Na ce"Khairi! Wallahi ba na ji a jikina zan so wata bayan ke, ina miki son da ko kaina ba na yiwa, wallahi da matata ce mai ciki, kika ce ba kya son cikin, ko ina so sai na yi mata tilas ta zubar, da ace zaman lafiya kuke yi da shi, da zan kwantar miki da hankali ne ki ci gaba da rayuwar aurenki fresh! Ni kuma na ci gaba da jinyar rashin ki, amma wannan rayuwar da kike ciki, ba k'aramin azabtar da zuciyata take yi ba, wannan bai cancanci zama uban 'ya'yanki ba, idan kin amince gobe na kawo miki maganin!".

"Na amince!" Na ji furucin ta a bazata.

"Wow! Alhamdulillah!" Na furta a fili, ina jin kasu hamsin cikin d'ari na kishin ya ragu a zuciyata.

Na ce"na gode Khairi, Allah ya kawo miki mafita cikin rayuwarki, Allah ya sa hasashena ya zama gaskiya, Khairi ina saka rai da ke, ban sare ba, kuma babu ranar sarewa har sai na daina numfashi! K'arfe nawa zan kawo miki goben?"

Ta ce"k'arfe takwas yake fita, ka zo karfe goma, amma kar ka k'araso kofar gidan".

Na ce"Allah ya kai mu, I love you!".

Ta ce"ina tsakar gida fa, ya zan yi da kayan?"

Na ce"na zo na shigar miki da su?"

Ta ce"rufa min asiri!".

Na yi murmushi ta ce"ki yi k'ok'ari, ki shiga da katifar, ki kwanta ki huta, daga baya zan nemo miki mafitar rayuwa in sha Allah! Muddin za ki ba ni had'in kai ta hanyar bin umarni na, in sha Allah kina dab da barin wannan k'azamar rayuwar, ki shiga sabuwar rayuwa mai 'yanci".

"Allah ya amince!" Ta fad'a.

Na ce"Amin! Don Allah ki furta min kina so na, sau d'aya kika tab'a fad'a, kuma lokacin ba na cikin nutsuwata".

Sai ta katse kiran.

Na kwanta ina jin kewarta kamar za ta kashe ni, aikuwa ban iya bacci ba sai da na gayyato 'yar tayin kwana.

Washegari na sayi k'wayar zubar da ciki, na kai mata, har na saka mata dubu ashirin a cikin ledar, wunin ranar sai na yi shi suk'uk'u, ina tunanin halin da take ciki, don na kira ta har sau biyar ba ta d'aga ba.

Tara na dare, na sake gwada kiran, sai na ji an d'auka an yi shiru, na tausasa murya na ce"Khairi! Sorry, kina jin ciwo ko? Khairi ki yi min magana pls, ya fita ko har yanzu? Ki na jin zazzab'i ne..."

Magana ta katse sakamakon jin muryara namiji yana fad'in"waye kai d'in? Kuma me kake nufi, a ina ka san ba ta da lafiya?"

Gabana ya fad'i, na yo saurin katse kiran, ina zare ido, kamar an kama kwarto. [12/9, 10:53 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*

BY *SADIYA ABDULRAZAK*

*FIRST CLASS WRITER'S*

MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru

*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕