Page 15
Ina katsewa aka sake kira, har ta gama ringing ban d'auka ba, sai da ya sake kira sannan na d'aga, ina saita kaina.
"Waye kai!?" Na ji muryar wanda make kyautata zaton mijinta ne.
Na ce"wrong number na yi".
Ban ma jira cewar shi ba, na katse kiran, na kashe wayar duka, na rik'e hab'a cike da fargabar Allah ya sa bai gane ba.
Hankalina bai kwanta ba, sai washegari da ta kira ni, ta fad'a mini bai gane ba, saboda Khairin da na ambata, ni kad'ai ne nake fad'a mata sunan, ta sanar mini cikin ya zube, na yi farin ciki sosai, sai na ji kamar kaso talatin cikin d'ari na k'alubalen da nake shirin fuskanta ya ragu, yanzu sai dai na daura damarar k'watar matata. Daga ranar kullum sai mun yi waya, tun tana d'ari-d'ari har ta saki jiki, sai dai idan ina zuga ta akan zancen mijinta ba ta cewa komai, yadda na lura dai tana jin tsoron shi, ko kuma tana shakkar abin da nake ba ta umarni, a haka har muka yi wata d'aya tare.
Watan da ya zame mini watan kunya, da tonon asirina, don a watan ciki ya bayyana a jikin Mariya, wanda suka yi ik'irarin cikina ne, kuma ba ni da bakin musawa, tun da na san na shiga ban d'auka ba, ba ta fitar da b'arawo, sannan tsakani da Allah na sani, ni ne na fara sanin Mariya, kuma ba na zargin tana bin wasu mazan.
Ranar na yi nadamar halina, na ji kunyar Hafiz ba kad'an ba, musamman da ya manta da amintar mu ya kalli idona ya ce 'abin da ka yi wa Mariya, in sha Allah sai an yi wa yaranka, sannan hannunka ba ya rubewa ka yanke ka yar, saboda haka sam ba za mu cuci Mariya mu had'a ku aure ba, da niyyar ka k'arashe b'arnarka! Kai ba ka cancanci a d'auki 'ya a ba ka ba, kuma idan akuyanci sana'ar yi ce, Allah ya kawo kasuwa!'.
Maganganun Hafiz sun yi mini ciwo, amma kuma na ji dad'i da suka k'i amsar tayin Abba na aura mini Mariya, don kuwa Nabila ma ta zamar mini karfen k'afa, bare wata Mariya, ni fa duk duniya da Khairi kad'ai nake hango rayuwar aurena ta nan gaba, ba zan sake auren wata mace ba, Nabila ma so nake su gaji, su nemi saki, na huta, sannan ni cikakken namiji ne, ba zan tauye kaina ba, na ce har sai lokacin da na auri Khairi ba, don haka neman mata yanzu ma na fara, rigima uban wa ta kashe!?
Bayan komai ya lafa, sai Ummi ta kira ni, ta ce na zo na d'auki matata, na ji kamar na yi mata k'aryar ba na garin, saboda sam ban shirya dawowar ta ba, na saba kawo mata cikin gidan, don ya fi mini kwanciyar hankali, haka na d'akko ta, ina jin takaici kamar na bige ta, da daddare ina d'akina ta shigo cikin shirin bacci, na yi mata kallo d'aya na watsar.
Ta zo ta zauna gefen gadon da nake kwance ta ce"Yaya".
Na yi kamar ban ji ba, don har ga Allah na so Ummi ta bari sai nan da kwana uku, saboda akwai wacce na shirya kwana ukun da ita a cikin gidan, kuma har na biya kud'in.
Sai ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba, ina zabga mata harara na ce"meye kika zo kika saka ni a gaba?"
Sai ta share hawaye ta ce"na ji abin da ka aikata!"
Na ce"uwar me na aikata?"
Ta ce"ka yi wa k'anwar abokinka ciki!".
A hasale na ce"na yi d'in! Ko za ki rama mata ne? Ke saboda kin raina ni har ni kike zuwar wa da wannan maganar?"
Ta girgiza kai, hawaye ya wanke fuskar ta ce"ba haka ba ne, amma a matsayina na matarka ya kamata na san halin da kake ciki, ban san dalilin da ya sa kake neman mata ba, zan so na san abin da ya sa, kake fita kana neman abin da nake da shi a waje, abin da ya faru ban ji dad'i ba, duk da na yafe maka".
Ina yi mata wani banzan kallo na ce "ni na ce miki ina neman yafiyarki? Ke uwata ce da idan kika yafe mini, wani abu zai canzu a k'addarata?"
Sai ta girgiza kai alamar a'a.
Na ce"kuma dalilin nan ai ke ya dace ki ba wa wani labari, idan kin manta to bari na tuna miki, na farko ke ce silar rabuwata da Khairi, don ba zan ce rasa ta ba, saboda in sha Allah! Ita din matata ce gaba kad'an, na biyu kin zo mini gida fanko, kin kawo mini sauran wani k'azamin, wa ma zai yarda mutum d'aya ne? Ai wallahi Nabila kin ba ni mamaki, kuma da na san haka kike da wallahi ko mutuwa kike ba suma ba, ba zan yarda da aurenki ba, gara na bar garin a neme ni a rasa, idan ya so ki mutu ko ki haukace!".
Har na gama fad'a mata abin da raina yake so, kuka take yi, sai da ta ji na yi shiru sannan ta tashi, na yi zaton ma fita za ta yi daga d'akin, sai gani nayi ta kashe hasken d'akin, ta dawo gadon za ta kwanta.
Na daka mata tsawa da fad'in"ke! Meye hakan?"
"I need you!" Ta fad'a kai tsaye, tana matsowa kusa da ni.
Da sauri na kunna fitilar wayata, na ce"kutt! Lallai yarinyar nan na ba ki dama da yawa, to zo na kashe ki!".
Ina shirin janyo ta, ta tashi ta fita daga d'akin da gudu, na yi k'wafa na kwanta ina jin mugun haushin ta.
Haka muka ci gaba da zaman, idan na kula Nabila to kud'in lalitata ne ya yi k'asa, saboda kaf ribar da nake samu a kasuwar a harkar banza take tafiya, idan ka cire nauyin gidana, to babu wani abu da na tsinana tun bud'e shagon. Ina ji a zuciyata ba na kyautawa rayuwata, wani lokacin sai na ji kamar na daina neman mata, na tsaya akan Nabila, sai kuma wata zuciyar ta ce mini idan na yi hakan, Nabila za ta rinjaye ni, ta mallake ni, har na manta da dabarun dawo da ran mataccen burin nawa, Khairi ita ce burina, kuma na yarda burin ya mutu, tun da ga ta can tana auren wani, amma ina ji a jikina ruhin burin zai iya dawowa gangar jikinsa, ya yi rayuwa mai tsayi fiye da ta da.
Wannan dalilin na rik'e, na dinga sab'on Allah, na mayar da kaina d'an watangaririya, ba tare da tunanin akwai ranar nadama ba.
Wani lokacin idan ina zaune ni kad'ai, ina hasashen kalar rayuwar auren da za mu yi da Khairi, sai na yi ta murmushi ni kad'ai, idan na yi sallah na yi ta rok'on Allah ya cika mini burina, duk kuma lokacin da wata zuciyar ta fad'a mini Khairi ta yi mini nisa, ban san lokacin da hawaye suke rinjayar k'wayar idanuna ba, Allah ya sani ina son Khairi so ba na wasa ba.
Na lalata rayuwata, kullum kamar wanda ake saukewa wahayin dabarun yaudara, haka na dinga lalata yaran mutane, sai da na lalata yara bakwai tun daga kan Ni'ima, har zuwa kan Fa'iza, wacce ta zama ta k'arshe cikin yaran da na lalata, don daga kanta na daddara, na daina bin yaran da ba su saba ba, sai dai wad'anda na san don kud'i suke yi, kuma ba ni ne na farko ba.
A kasuwa muka had'u da Fa'iza, kyakkyawar yarinyar da ba ta kai shekara ashirin ba, nan take na shigar da kaina, kuma na samu karb'uwa, don farinjiki halittata ce, muka shafe satuttuka muna soyayya da ita, amma ta k'i yarda na je gidan su, sai daga baya da na matsa, har na nuna zan iya rabuwa da ita, sannan ta sanar mini, an kusa aurenta da wani yayanta, kuma ba son shi take ba, idan na zo gidan su ya gan ni, za a samu matsala.
Ai ni hakan sai ya yi mini dad'i, na dinga zuga ta da nuna mata, kar ta yi auren da ba ta so, don ba za ta tab'a sanin ainahin gard'in rayuwar aure ba, na baje basirata, wurin sake cusa mata kaina, ta hanyar da ta kai ba ta iya musu da ni, saboda gudun fushi na.
Ta haka na rinjaye ta, muka fara musayar kalaman banza ta waya, hotuna, har ma da video, kafin na yi nasarar kiran ta gidana bisa sharad'in a iya romance za mu tsaya, duk da ni na k'udure komai zai faru a ranar, tun da tana so na, na san zai yi wuya ta musa mini, na yi sa'a ta amince.
Ranar da za ta zo har sakarwa Nabila fuska na yi, da kaina na kai ta gidan su da sunan ta je ta wuni ta huta, sannan na wuce na d'akko Fa'iza a inda muka yi da ita, za ta tsaya.
Sai dai duk yadda na yi tunanin abun zai zo da sauki', bai samu ba, Fa'iza ta k'i amincewa da ni, k'arshe ma sai ta nemi yi mini ihu, ni kuma na riga na je ajin k'arshe wurin buk'atuwa, don har wasu k'ayoyi na kora, saboda haka na kasa jurewa, na yi mata mummunan fyad'e.
Na firgita sosai, na ce mata ta zauna, na fita na siyo kayan aikin da zan yi mata d'inki, sai ta k'i yarda, ta ce ni ba likita ba ne, kawai na kai ta asibiti, muka dinga ja-in-ja, har kayan treatment na nuna mata, amma ta k'i nayi mata d'inki fir, sai da na yi mata jan ido, sannan ta ce ta yarda, na tafi siyowa, ina dawowa na na tarar babu kowa a gidan, hankalina ya tashi, na dinga kiran wayarta ba ta d'agawa, har hanya na bi, amma ban ga ko mai kama da ita ba, haka na dawo falo na zauna ina ta fargaba, sam babu wata nutsuwa da na samu ma.
Ashe dai na yi kuskuren kawo ta, ta ga gidana.
Har zuwa dare ina kiran ta, ba ta d'auka, washegari da misalin bakwai na safe, ina bacci, aka fara buga gidana da mugun k'arfi kamar za a b'alle k'ofar, Nabila ta shigo d'akina a firgice, ni ma tuni na tashi zaune ina mamaki, ta ce"ka je ka duba".
Na tashi babu ko riga a jikina, na tafi.
Ina bud'e k'ofar tun kafin na tantance wanda na gani, aka mayar da ni cikin gidan, da wani mugun naushi a k'irjina, irin wanda ban tab'a ji ba, don da farko ma na yi zaton da dutse aka mayar da ni, sai da na kai k'asa, bayan na rayuwata ta gama juyin waina, na d'an dawo hayyacina, sannan na lura da sojojin da suke tsaye a kaina.
Da k'yar na bud'e baki na karanto salati, ina shirin tambayar abin da ya faru, wani cikin sojojin ya warto ni daga k'asa, kamar ya damk'o kaza, ya shiga naushi na, na dai ji ihun Nabila, daga nan kuma ban sake sanin abin da yake faruwa ba, sai da na farka na ganni kwance, a wani wuri, jikina jagab da ruwa, na tashi da k'yar, na zauna, ina sauke numfashi, sanyin jik'akkun kayan jikina ya saka ni karkarwa, sai da na lura sosai sannan na gane a bariki nake, cikin tsakiyar sojoji. [12/11, 5:21 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕