Page 16
Da k'yar na tashi zaune ina rarraba ido, zuciyata kamar zata fad'o saboda bugun da take yi mini, biyu daga cikin sojojin suka k'araso, d'ayan ya wanke ni da mari, ya yi ball da ni har na bugu da wannan durom d'in da suke zuba k'asa a ciki, kafin ya biyo ni, ya fara tattaka ni, babu imani.
Sai da ya gaji don kan shi ya bari, zuwa lokacin tuni na fid da rai da duniya, na saddak'ar yau ce ranar mutuwa ta, cikin mawuyacin hali na fara yi masa magana, muryata a shak'e, na ce"don Allah ku fad'a mini laifin da na yi muku, a sani na ban yi rigima da kowa ba, me na yi muku, ko dai ba wuri na aka aiko ku ba?"
Ina rufe baki, ya yi mini wani wawan naushi, da idona a rufe yake ko kuma cikin duhu ne, sai na rantse dutse ne, ba hannun mutum ba. Sai kuma ya dinga yi mini kallon tsana, yana huci, ya jinjina kai ya bar wurin.
Na kalli d'ayan ina kuka na ce"Oga don Allah, idan ka san abin da na yi masa ka taimake ni ka sanar mini!".
Kamar jira yake,sai kuwa ya wanke ni da mari, ya fizgo ni, ya fara jana a k'asa cikin rana, jikina duk ya kurkurje, don singileti da gajeren wando ne kawai a jikina, ya kai ni wuri mai nisa, sannan ya ba ni abun shara, ya ce na share duka birikin kafin awa d'aya. Da k'yar nake iya tsayuwa, amma ba ni da bakin musa musu, haka na fara yadda ya ce, duk bayan mintuna sai ya zo ya zane ni, wai ba na sauri, sai bayan azhar na gama, sannan ya ba ni d'ibar ruwa, to a nan ne kuma, duk dauriyata na kasa, don tun kafin na kai bokitin farko, k'afafuwana suka yi mini tawaye, muka zube ni da bokitin, a wurin, da ya zo ya same ni, sai ya dinga ja na har sai da ya kai ni wurin wannan mai k'irar samudawan, wanda yake naushi na, ya wancakalar da ni, tsoro duk ya dagargaza zuciyata, burina ya sanar da ni laifin da na yi masa kafin ya kashe ni, saboda na kiyaye, ko a lahira kar na yi gangancin sake aikatawa.
"Kai!" Ya daka mini tsawa.
"Na'am!". Na fad'a a firgice, don ko had'a ido da shi ba na so, saboda tsoro.
Ya ce"meye had'in ka da wannan?"
Na d'ago idona, na zube akan wayar da yake nuna mini, sai na ga hoton Fa'iza akan screen d'in, cikina ya d'uri ruwa, kamar na yi k'aryar ban santa ba, sai dai kuma ina tsoron kar ya zuciya ya kashe ni. Cikin rawan murya na ce"Fa'iza ce...I buduruwata ce, amma muj rabu".
Ya kife ni da mari har sai da na fad'i, ya ce"kun rabu, shi ya sa ka yi mata fyad'e? Ka san tun tana yarinya na mayar da ita gidanmu, nake tsaron mutuncinta, nake tarbiyantar da ita, nake raba ta da duk wani saurayi? Sai yanzu da auren ya rage sati biyu za ka shiga hurumina?"
Na dinga girgiza kai alamar a'a.
"Ka yi magana! A ina kuka had'u, kuma wasu kalaman yaudara ka yi mata, har ta je gidanka!?"
Na fara kuka, ina nadamar sanin Fa'iza, na ce"kasuwa! A kasuwa muka had'u, kuma ba ta fad'a mini kai ne za ka aure ta ba, don Allah ka yi hak'uri, ka yafe mini".
Sai ya tashi ya damk'i hannuna, har na yi zaton karya shi zai yi, ya je ya wurga ni cikin wasu tarin bulo, ya ce"ka duba cikin bulon nan, ka zab'i guda goma, kowanne ka yi masa irin yadda ka yi wa Fa'iza, idan ba ka yi ba, to sai na dandatse ka, tun da kai k'aramin d'an iska ne!".
Ya juya ya tafi, ya bar sojoji biyu kowanne rik'e da bulala suna gadi na, na fashe da kukan tausayin kaina, kamar jira suke a tare suka fara zuba mini mahaukaciyar bulalar, na hau ba su hak'uri, ina ce musu zan yi, da sauri na fara, ina kuka ina fatan Nabila ta je ta sanarwa Abba halin da nake ciki.
Ba k'aramin tashi hankalin Nabila ya yi ba, bayan sun tafi da shi ta durk'ushe a wurin tana kuka, kafin ta saka hijjabinta ta tafi gidan su Saifu, tana kuka ta sanarwa Ummi abin da ya faru, jikin Ummi ya yi sanyi, ta zaunar da ita ta sa aka ba ta abun kari, Nabila tana kuka ta kalli Ummi ta ce"Ummi ta ya zan iya cin abinci, ban san halin da yake ciki ba".
Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce"tuni na sallama wa Saifullahi! Duk wanda bai ji bari ba dole zai ji woho! Na tabbatar akwai abin da ya aikata, haka kawai sojoji ba za su zo su tafi da shi ba, Saifullahi ya wuce zaton mu, Allah ya fito da shi lafiya kawai zan ce".
Daga haka Ummi ba ta sake bi ta kan zancen ba, duk da abun yana damunta, suna ta zuba idon dawowar shi, tun bai tafi da mukulli ba, idan ya dawo dole zai nema, amma suka ji shiru, har washegari, bai dawo ba.
Nabila abinci ma yafita kawai take yi, damuwar duniya ta ishe ta, kuma ta ga Ummi ba ta da niyyar d'aukar mataki, sai ta sanarwa mahaifiyarta halin da ake ciki, ta zo gidan kuwa ita ma hankali a tashe, nan ta yi ta tausar Ummi, da ba ta hak'uri, tana nuna mata hannunka ba zai rub'e ka yanke ka yar ba, har dai ta hak'ura, ta kira Abba ta sanar masa, da yake ba ya garin a lokacin, shi ma fad'a ya dinga yi, me ya sa ba a sanar da shi tun jiyan ba, watak'il ma zuwa yanzu sun kashe shi, a gaggauce ya hau mota, ya taho gidan.
Shi ya kira yayan Saifu, wanda ya kasance babban soja, ya sanar masa halin da ake ciki, shi kuma ya sa aka yi bincike aka gano inda Saifu yake, lokacin har tara na dare ta yi, haka suka tafi shi da Ibrahim.
Kalmar na jigata, ta yi k'ank'anta, ta bayyana halin da nake ciki, wahalar da na sha baki ba zai iya furtawa ba, cikin kwana d'aya da wuni, na rame na fita daga hayyaci na, duk wata gab'a dake jikina ta san ina cikin wani hali, tun ina kuka da hawaye, har suka yi mini ta waye, don sun ga ba ni da niyyar barin su su huta, jikina duka shatin bulala ne, don kuwa bayan na kasa gwadawa akan bulo, duka suka yi mini ba na wasa ba, sai bayan magriba na rok'e su zan yi sallah, suka ba ni ruwa, na d'aga da niyyar yin kurb'a d'aya don na jik'a makoshina da yake shirin daskarewa saboda tsananin k'ishi, ai sai da na shanye ruwan sannan na ajiye butar, sai taimama na yi, don kar na tambayi wani ruwan na yi laifi, a zaune nayi sallah, shi ma don kar na kwanta ne su yi zaton hutawa nake ba sallar ba, sai wani daga cikin su ya mik'o mini burodi da ruwa, na karb'a ina godiya, na cuccusa na kora da ruwa, sannan suka watsa ni a wani k'aramin d'aki, na kwana cikin sauro, idan na gaji da tsinewa Fa'iza, sai na fara istigfari, ina yi ina hawayen da ban damu da share su ba, ko kad'an ban samu baccin ba, saboda tsananin azabar ciwon da jikina yake yi.
Washegari da suka ga ba zan iya aiki ba, sai suka zane ni, suka juye mini ruwa bokiti guda a kaina, haka na dinga rawar sanyi, jikina ya damalmale da jik'akkiyar k'asa, kallo d'aya dai za ka yi mini ka ce daga bakin kura na k'wato.
Bayan sallar isha'i, ina kwance wani soja ya zo ya bud'e ni, na bi bayan shi ina tangad'i kamar makakke, don sai da na fad'i sau uku kafin mu k'arasa, tun daga nesa na shaida babban yayanmu Captain Ibrahim Usman, farin ciki ya rufe ni, ai kawai sai na zube kafin mu k'arasa inda suke, to dama k'arfin halin takawar kawai nake, don kar su k'ara min dukan, yanzu kuma na ga gatana, na san k'arshen wahala ta ya zo, musamman da na ji muryar Abba yana salati, yayana kuma yana ta surfa masifa, Abba har da cewa sai ya yi shari'a da su.
Na sani dama ba su san inda nake ba, shi ya sa aka bari har na kwana, don Abba yana son 'ya'yan shi, musamman ni, ko me na aikata zai yi wuya ya bar ni cikin mawuyacin hali.
Haka aka kwashe ni ranga-ranga, sanyin da na ji ne ya tabbatar mini cikin mota aka saka ni.
"A kashe Ac, zazzab'i nake". Na fad'a da k'yar, ina jin yadda sanyin yake mugun fama mini ciwukan jikina.
"Sannu Saifullahi!" Abba ya fad'a yana shafa kaina, da yake kan cinyarsa.
Kai tsaye asibiti aka kai ni, Ummi da Nabila suka zo da ruwan zafi, na wanke jikina, aka shafe mini jiki da magani, sannan na ji abinci, na sha magani, aka jona mini karin ruwa, aka lullub'e ni da bargo, sai bacci. [12/11, 8:14 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕