Page 17
Sai bakwai na safe na farka, na ga Nabila zaune a d'akin da nake, babu laifi jikin nawa ya rage ciwo, na tashi a hankali ina cije baki, ta taso da sauri ta ce"sannu Yaya".
"Yawwa" Na fad'a ina sakkowa daga kan gadon.
Sai ta zo za ta rik'e ni, na yi mata mugun kallo na ce"ke dalla matsa!"
Ta koma ta zauna, har hawayen da ba sa yi mata wuya sun zubo.
Cikin zuciyata na ce 'ai duk ke kika ja mini komai, 'yar wahala'.
Don ni dai a gani na, tun farko da na samu Nabila a cikakkiyar buduruwa, zan iya hak'uri na yi maleji da ita, kafin zuwan lokacin da zan yi yak'in k'watar Khairi.
Na shiga band'aki, na yi alwala, kafin na fito ta shimfid'a mini sallaya, ina idarwa ta mik'o mini brush da Maclean, bayan na yi, na dawo na zauna, ta zuba mini abun kari, ta kawo gabana, tana sake yi mini sannu.
Da na gama, ta d'akko maganin da aka shafa mini jiya, muryarta tana rawa ta ce"likitan ya ce idan ka tashi, na shafa maka".
Na harare ta, sannan na rage kayan, ban ce komai ba, hakan ya ba ta damar shafa mini, da ta gama, ta mik'o mini magani na sha, sannan ta mik'o mini wayata.
"Su waye suka kira ni?" Na tambaya tun kafin na karb'a.
Ta ce"tun ranar a kashe take".
Na karb'a, na kunna, na bi duka na goge duk hotunan Fa'iza, da duk wani abu da ya dangance ta, sannan na kira layin Khairi, don na ji lafiyarta.
Babu jimawa ta d'aga, muka gaisa kafin na ce"Khairi ba kya nema na ko?"
Kamar tana jira sai ta fashe da kuka, hankalina ya tashi, na ce"subhanallah! Mene ne? Ko wani abun ya yi miki?"
Kamar na zuga ta, sai ta k'ara k'arfin kukan, na lumshe ido, ina jin ni ma na shiga damuwar, tun kafin na ji damuwarta, na harari Nabila da ta kafe ni da ido, sai ta kau da kai, tana sana'arta, ta share hawaye.
Na ce"ki yi hak'uri Khairi! Komai ya yi zafi maganin shi Allah! Allah yana sane da halin da muke ciki, in sha Allah komai zai zama tarihi, ba kuka ake ba addu'a ake yi".
Ta tsagaita da kukan, ta ce"Saifullahi! Hamza ya sake ni..."
Wallahi sai na ji kamar ban ji daidai ba, ko kuma mafarki nake yi, na katse ta da fad'in"me kika ce? Hamza ya yi me?"
"Ya sake ni!" Ta maimata.
Wani sanyi ya shiga ketowa daga cikin zuciyata, na ji farin cikin da ba zan iya fasalta shi ba, na sauke ajiyar zuciya, kafin na kai ga magana, ta ci ga ba da cewa"ba rabuwar mu nake yi wa kuka ba, don dama na san dole zai rabu da ni, saboda tun da ya tashi k'ara auren nan yake mini wulak'anci, a gida an kasa yi mini adalci, sun hau kan k'aryar da ya yi sun zauna, sun ce laifina ne, ni ce na dame shi da haukan kishi saboda zai yi aure, tun shekaran jiya da abun ya faru, ko na gaida Baba ba ya amsawa, kowa ya k'i fahimta ta, ina cikin k'unci!".
Na ce"ki yi hak'uri, ki daina damuwa, khairan in sha Allah! Komai ya zo k'arshe, dama ba kowane iyaye ba ne suke yi wa 'ya'yansu adalci a komai, kin ga dai rashin adalcin ne ya sa aka raba mu, to ki godewa Allah, yanzu ki bar yi mini asarar hawayen ki, don suna da matuk'ar tsada a wurina, ba ni da lafiya, muna kan wani case ne komai, zan kira ki daga baya".
Ta ce"to, Allah ya sawak'e".
Na katse kiran, ina murmushi, sai na mance gumurzun da yake gabana, tun da ga shi zan samu Burina ai komai mai sauk'i ne, matuk'ar za a bar ni da rai.
Kamar daga sama na ji muryar Nabila, tana cewa "Yaya! Me ya sa ba ka yi mini adalci? Me ya sa ba ka da uzuri, ba ka da mantuwa? Hujjarka ta cewa ba ka same ni a yadda ya kamata ba, mai rauni ce! Dama can ba ka so na, don da a ce wannan Khairin ka aura ka same ta, a yadda ka same ni, da tuni ka manta, kun zauna lafiya".
Na yi tsaki, na kwanta, don ba ni da lokacin ta, farin cikin mutuwar auren Khairi kawai nake, na fara hango rayuwar Mataccen burina nan ba da jimawa, idan na samu Khairi, ai na warke, komai daidai , babu wata mace kuma da za ta sake ja na, na aikata zina ko da bokayen duniya za ta bi, kai Nabila muddin Khairi ta nuna alamar ba ta son kishiya wallahi, sakin ta zan yi salun-alun, don Khairi ta sha wuyar rayuwa da mahaukaci, yanzu farin ciki take buk'ata, don haka wajibi na zage damtse na faranta mata da iya k'arfi na, kuma a wannan karon duk wanda ya so kawo mini cikas akan auren Khairi, ban k'i na yi shari'a da shi ba.
Da wannan farin cikin na koma bacci, sai azhar Ummi ta tashe ni, na yi sallah, Yaya Ibrahim ya shigo, yana yi mini sannu da alama ran shi a b'ace yake, na sha jinin jikina, na sunkuyar da kai ina amsawa.
Ya ce"kai! Da gaske ka yi wa 'yar mutane fyad'e?"
Kunyar duniya ta rufe ni, Nabila kuma sai ta fara hawaye, ta tashi ta fice. Na ce"I, amma ni ban yi mata fyad'e ba, da yardar ta".
Ummi ta wanke ni da mari, kafin ta fara fad'a, sai kuka ya k'wace mata, ita ma ta bar d'akin, shi ma ya yi mini mai isar sa, wanda sam bai dame ni ba, don mutuwar auren Khairi ta gama wanke zuciyata, duka ina sauraron fad'an shi, sai da ya zo gab'ar k'arshe sannan na kalle shi, inda yake cewa"yanzu dai sun shigar da k'ara kotu, kuma har an kawo maka sammaci, sannan sun d'auki lauya, jibi za ku fara shari'a!".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Na furta a hankali.
Ya ce"mun yi magana da Kamal, ya ce yana da shari'a jibin, amma zai had'a mu da wani lauya a cikin kotun da suka kai k'aran, in sha Allah za a yi nasara, amma ka sani wannan shi ne na k'arshe, daga nan duk abin da ka sake kwasowa, ko kashe ka za a yi, ba zan shiga ba!".
Da sauri na ce"to na gode sosai Yaya, Allah ya saka muku da alkairi!".
Ya fice, na fara fargaba, duk da na san zai yi wuya Abba ya bari a kulle ni. Sai na ji dad'in zab'in da Abba ya yi mana, tun ba mu gama sanin ciwon kanmu ba, babban yayanmu Ibrahim ya ce shi soja ne, kuma ya yi biyayya, ga shi yau yana matsayin Captain, kuma matsayin na shi ne ta k'wace ni daga hannun sojoji, mai bi masa Kamal, ya ce shi kuma lauya ne, shi ma ya yi biyayya, a yanzu yana matsayin k'wararren lauya, ga shi zai cece ni a wata shari'a, ni ne kawai na watsar da burin mahaifinmu, ban yi biyayya ba, ga shi yanzu ina da matsayin tantiti a idon mutane da yawa.
A ranar aka sallame ni daga asibitin, na ci gaba da shan magani, jikina ya yi kyau kafin ranar da muka shiga kotu, ni ko kallon shari'a ban tab'a zuwa ba, to ga wannan gabad'aya ma a kaina za a yi ta, gabana yana ta fad'uwa, ina fargabar abin da zai je ya zo, kar a tura ni gidan maza, kafin na fito Khairi ta yi aure ta bar ni.
Shari'a aka ce sab'anin hankali, lauyan da ya tsaya mini k'wararre ne, sosai ya san aikinsa, ya hak'ik'ance akan ba ni da laifi, saboda Fa'iza har gida ta je ta same ni, ba gidan su na je ba, don haka ba fyad'e na yi mata da amincewarta, sannan d'an'uwanta ya kama ni har cikin gidana, ba bisa k'a'ida ba, kuma sun azabtar da ni, sun yi mini dukan kawo wuk'a, wanda har sai da na kwanta jinya a asibiti.
Lauyan su kuma ya ce fyad'e ne, saboda Fa'iza ta fad'a musu ba ta amince ba, duk da ta ce da k'afarta ta je gidan.
A k'arshe dai alk'ali ya gamsu da hujjojin lauyana, muka you nasara, aka ajiye zancen a matsayin mun aikata zina ne, ban yi wa Fa'iza fyad'e ba, har ma aka ci tarar saurayin nata, bisa kama ni da ya yi, ya azabtar da ni, ba bisa k'a'ida ba.
Shari'a ta watse, na yi wa kaina fad'an na daina neman mata, amma sai gangar jikina ta k'aryata ni, bisa wata babbar k'addarar na ci gaba da neman mata, tun sati biyu da faruwar lamarin, sai dai fa na daina bin yara k'anana, a yanzu idan na san ke buduwaruwa ce ma ko kallo ba ki ishe ni ba, manyan karuwan nake bi, wad'anda na san ba ma za su yarda su samu ciki ba, kuma ko kun samu su kan su ba za su tantance cikin waye ba.
Nabila ta dage da kyautata mini, yarinyar sam ba ta da zuciya, duk da ina kyarar ta, amma kamar ba ta damuwa, ganin ko me zan yi mata ba ta ma damuwar sai na d'an sassauta mata, har ma nake had'a shimfid'a da ita lokaci zuwa lokaci. [12/13, 9:23 AM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕