Page 18
Cika iddar Khairi tamkar cikon burikana na duniya na ji, farin ciki kamar na zuba ruwa a k'asa na sha, nan muka bud'e sabon babin soyayya ta waya, wannan karon sai na ga kamar ba ita ba ce, yadda ta zage take mai da mini martanin soyayya, muka samu shak'uwa da fahimtar nuna sosai, sai na ji kamar ma ban tab'a sanin ta ba, sai yanzu, duk wanda ya kalle ni zai gane ina cikin nishad'i, da nutsuwa, sai dai tana fargabar na fara zuwa gidansu, a lokacin sai na ja baya sosai na rage neman mata, muryar Khairi kawai tana isa ta d'ebe kewa. Nabila kuma tana laulayin cikinta na wata biyu.
Sai da ta yi wata biyu da gama iddar, na tiso ta a gaba da zancen ni fa dole zan fara zuwa, don da wuri nake so a yi duk wacce za a yi, duk yadda ta so zamewa sai na taro ta, har dai ta saka mini rana na je, da kaina na nemi gaisawa da Babanta, don na fi so a san wannan karon na yi d'amara.
Bayan na gaishe shi, na ce"Baba Saifullahi ne".
Ya ce"ai na gane ka! Dama da ba ka nemi gani na ba, dole ni zan neme ka".
Na fara fargaba, amma na dake ban nuna ba.
Ya ce"mun ji komai, na komawa wurin Ni'ima da ka yi, bayan ka fasa auren Ummul-khairi, kuma ka yi sanadin tab'arbarewar karatun ta, bayan mahaifinta ya raba ku tun kafin abun ya yi nisa".
Gabana ya dinga fad'uwa, na hadiyi wani yawu na ce"Baba don Allah ku yi hak'uri, wannan ya wuce in sha Allah! Kuma ko a lokacin Ni'imar ce ta nuna mini ba ta son rabuwar mu, sannan wallahi ba da niyyar yaudara na je wurin ta ba, na je ne a k'ok'arina na ganin na maye gurbin Ummul-khairi da ita, sai kuma aka samu rashin fahimta".
Baba ya ce"to yanzu me ya dawo da kai?"
"Auren Khairi! Wallahi wannan karon ba za samu wata matsala ba, na yi muku alk'awari, ko yau kuke buk'ata zan turo a yi zancen auren".
Baba ya ce"A'a! Mu ba gaggawa muke yi ba, sannan ba mu ce ba za mu ba ka ba, matuk'ar tana son ka, amma daga yau ka dakata da zuwa wurin ta, har sai na neme ka!".
Tsoro sai ya kama ni, zuciyata ta soma karaya, a sanyaye na ce"amma Baba don Allah akwai wani laifin da na yi?"
Ya girgiza kai alamar babu, sannan ya ce "akwai binciken da zan yi ne, idan na kammala ni da kaina zan neme ka, ina laifin mai son naka?"
A sanyaye ce"to Baba na gode!".
Na tashi na tafi, ina nadamar zuwa wurin shi, ganin Khairi da na yi yau, muka zauna ga ni, ga ta, muka yi fira, ba k'aramin shauki, da zumudin auren ta na ji ba, na koma gida cike da fargabar kalar binciken da zai yi.
Sati biyu ba na zuwa, sai dai kullum muna jone a waya, a cikin sati na ukun ta ce Baban yana kira na. Na tafi zuciyata cike da fargaba, bayan mun gaisa, ya kira sunana a tsanake, "Na'am Baba!" Na amsa kaina a k'asa, zuciyata tana bugu, fatana kawai na ji ya ce komai daidai, gobe na turo magabatana.
Ya ce"na tarar da wani b'oyayyen hali mara kyau a tare da kai, da gaske kana neman mata?"
Haba! Ai sai na ji kamar na nutse a wurin, ko na tashi sama, zuciyata kamar za ta fad'o saboda fargaba, na shiga taraddadin na amsa, ko na musa? Kar na amsa ya haramta mini auren Khairi, kar kuma na musa ya ce na karyata shi, sai na yi shiru zufa tana karyo mini, wata nadama ta rufe ni lokaci daya.
Nan take kuma ya sanar mini kalar labarin da ya ci karo da shi na fyad'en da na yi wa Fa'iza a cikin gidana, har ma aka k'ara da cewar da muka je kotu, mun siye alk'ali an wanke ni nan take, kuma dama can ana zargi na da neman mata.
Tuni idanuwana suka kawo ruwa, da rawan murya na ce"Baba kai uba ne a gare ni, saboda haka ba zan iya yi maka k'arya ba, idan na yi hakan kamar na raina ka ne, haka ne, na aikata, amma babu zancen canza magana da aka yi a kotu, hakan yake wallahi ban yi mata fyad'e ba!".
Na tsagaita, don na ji yadda ya d'auki zancen, zuciyata cike da fargabar rasa burina, har tsawon lokaci bai ce komai ba, hakan ya sa na ci gaba "wallahi Baba ni wannan shi ne k'addarata, amma na daina tun lokacin da abun ya faru, kuma wallahi da ba haka nake ba, rashin Ummul-khairi shi ya canza rayuwata, na san na yi kuskure, amma na tuba, don Allah kar wannan ya shafi aurenmu da Khairi, muna son junanmu!".
Ya ce"Assha! Ba ka kyautawa kanka ba, kenan ka nuna wa Allah ba ka karb'i hukuncin shi ba, kai ba za ka d'auki k'addara ba, sai ka zab'i sab'a maka, tun da ba ka samu son zuciyarka ba ko?"
Na girgiza kai, alamar ba haka ba ne, hawaye tuni sun wanke mini fuska.
Ya ce"zan yi magana da ita, idan har ta amince, ta ji , ta gani, za ta aure ka a hakan, Allah ya sanya alkairi!".
Na ji sanyi har raina, na ce"to Baba na gode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya k'ara girma da lafiya".
Daga haka muka yi sallama na tafi.
Tun a daren na fara yi wa Khairi shimfid'a kafin Baba ya tunkare ta, da zancen, bayan mun tab'a fira na ce"Khairi wane kalar namiji kika fi tsana, kike jin ba za ki iya zama da shi ba?"
"Mara tarbiyya, mara addini, wanda ba ya so na, d'an shaye-shaye, da kuma manemin mata!". Ta fad'a kai tsaye.
Da ta ambaci manemin mata, sai da na ji zuciyata ta motsa, na sauke ajiyar zuciya, na ce"yanzu idan kika same ni da d'aya daga cikin wannan halayen da kika jero, ya za ki yi? Fasa auren, ko kuma k'ok'arin ganin na shiryu?"
Sai ta yi 'yar dariya ta ce"ai na san ma ba ka da ko d'aya daga ciki".
"Hmmm!" Na sauke ajiyar zuciya.
Ta ce"ko akwai?"
Na sauke numfashi na ce"Khairi a yanzu na san kina so na, amma duk da hakan ba ni da tabbacin za ki aure ni, idan na kalli yanayin rayuwata, na kalli taki rayuwar, da kuma kyakkyawar zuciyarki, sai na ga kamar ba mu dace ba".
Ta ce"Saifullahi, a iya sani na dai duk halayenka ma su kyau ne, sai dai ko daga baya ka canza".
Na ce"haka ne Khairi, kin san ita k'addara takan iya canza komai, sannan tun bawa yana cike Allah ya gama tsara masa komai na k'addarar shi, ita ce ta canza mini rayuwa, amma idan kin so za ki iya gyara ni, saboda so yana canza komai!".
Ta yi shiru na d'an lokaci, kafin ta ce"akwai wani halinka da ka b'oye mini?"
Na ce"ba b'oye miki na yi ba, don ba zai b'oyu ba, sai yanzu dai ya kamata a ce kin sani".
Ta ce"to ina jin ka!".
Cikin sakanni na yi gwagwarmayar danne k'uncin da ya mamaye zuciyata, na sauke numfashi mai zafi, na ce"Khairi ina rok'on alfama a gare ki, ina so ki fara yi mini alk'awarin kasancewa da ni har k'arshen rayuwarki, don Allah kar abin da zan fad'a miki, ya sa ki bar ni, saboda na san dole zai zabtare rabin k'aunata a zuciyarki".
"Ina jin ka" Ta fad'a muryarta da sanyi.
Na ce"Khairi, a baya na fad'a miki jikina yana ba ni, ke ce kad'ai macen da zuciyata za ta so, tun da na rabu da ke ban sake haduwa da wacce na ji zan iya maye gurbinki da ita ba, hakan ya sa har matar da aka aura mini, ba na kallon ta da daraja..."
"Don Allah ka fad'a mini matsalar kai tsaye!" Ta katse ni.
Na ce"Khairi! Allah ya jarbce ni da neman mata, ta sanadin rashin ki cikin rayuwata..."
"Neman mata!?" Ta katse ni da tambayar.
Na jinjina kaiz kamar tana gani na, na ce"I, amma ki yarda wannan yana cikin k'addarata, kuma yanzu na daina, amma na san ko ban sanar miki ba, za ki iya jin labari, son gaskiya nake yi miki, kuma a yanzu na san ke ma kina tare da ni, shi ya sa nake kyautata zaton za ki yi mini uzuri, ki rungume ni a duk irin halin da na shiga, saboda har zuciyata idan ke ce kika shiga wata rayuwa, matuk'ar ba ke kika goje ni ba, ba zan juya miki baya ba".
"Khairi!" Na kira sunanta, jin ta yi shiru, kamar ba ta tare da ni.
"Zan yi tunanin akan yiwuwar aurenmu". Abin da ta ce kenan ta katse kiran.
Na sake kiranta, sai na ji wayar a kashe, na kwanta cike da fargaba, hawaye suka fara kwaranya ta gefen idona, Allah ya sani a wannan karon idan na rasa Khairi, za a samu babbar matsala. [12/20, 11:32 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕